Maiduguri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Garin Maiduguri dai ita ce babban birnin jihar Borno a arewa maso gabas din Najeria. Maiduguri ita ce birnin da tafi kowane birni wajen girma da yawan jama'a a arewa maso gabas din Najeriya. A'kalla birnin tana da jama'a fiye da miliyan daya. Birnin Maiduguri da sabon birni ne kuma an kafa shi a shekaran alif da dari tara da bakwai (wato 1907). Maiduguri ya 'kunshi unguwar Yerwa (Yerwa yana nufin alheri a harshen kanuri) ta yamma da kuma tsohuwar Maiduwuri ta bangaren gabas.

Mulki[gyara sashe | Gyara masomin]

Birnin Maiduguri shine fadar mai daraja shehun Borno kuma ita ce fadar gwamnatin jihar Borno.

Kasuwanci da tattalin arziki[gyara sashe | Gyara masomin]

Babban kasuwan Maiduguri ita ce kasuwar litinin wannan take a tsakiyar birnin Maiduguri. Abubawan cinikayya sun hada da tufafi, kayan masarufi, kayan abinchi, tukwane, bangaren motoci da babura, kasets na CD da DVD, telebijin, rediyo, takalma da sauransu. Kananan kasuwanni a Maiduguri sun hada da kasuwan Custom wanda yake tsakanin unguwar gamboru da gwange, kasuwar budum, kasuwar tashan Baga wanda yayi suna wurin cinikayyan kifi da ake kowawa a garin Baga wanda yake dab da tafkin Cadi.

Yawancin mutanen garin Maiduguri dai manoma ne amma akwai 'yan kasuwa da dama da kuma ma aikatan gwamnati. Manyan masana'antun Maiduguri sun hada da Maiduguri Flour Mills, kamfin sarrafa Dalaram (wanda a halin yanzu ta dur'kushe), kamfanin Coca Cola, Borno Aluminium company, Kamfin Alewa ta Haske da kuma kamfanin sarrafa takalma ta Natel. Akwai bankuna da yawa a Maiduguri a kan titin Shehu Laminu Way. Yawancin bakuna suna da daukan ku'di da kanka wato ATM.

Zirga-zirga[gyara sashe | Gyara masomin]

Maiduguri tana da filin jirgin sama wadda ake kira Filin jirgin sama a Maiduguri. Jiragen sama kan tashi kowane rana daga Maiduguri zuwa Abuja da Lagos. Akwai kuma jiragen da suke zirga zirgan daukan Musulmi zuwa Saudi Arabia lokacin aikin Hajji. Da fannin jiragen 'kasa kuwa Maiguri tana da Makeken tashan jirgin kasa wanda aka fi sani da Railway Terminus Maiduguri. Tashan jirgin kasan tana dab da inda rikicen Boko Hram ya Barke a 2009 a unguwar goni damgari bayan kwatas. Daukan shanu daga Maiduguri zuwa kudancin Najeriya yana daya daga cikin manyan dilalan kafa layin jirgin 'kasa a Maiduguri.

Maiduguri tana da manyan titunan mota kamar su Sir Kashim Ibrahim Road, Shehu Laminu Way, Bama Road, Jos Road da Baga Road. Hanyoyin motan sun hada Maidguri da sauran Birane kamar Yola, Kano da Bauchi. Akwai kuma hanyoyi zuwa kasashen waje kamar Chadi, Nijar da Kamaru.

Ilmi da makarantu[gyara sashe | Gyara masomin]

Akwai jami'a a birnin Maiduguri wanda ake kira da Jami'ar Maiduguri. Jami'an yana kan Bama Road. Kosakosen da ake karantarwa a jami'ar sun hada da ilmi aikin likita, ilmin injiniyarin, ilmin watsa labarai, ilmin harshen turanci da kuma ilmin addini da al'adu. Jami'ar Maiduguri tana da Asibitin koyarwa na Univesity of Maiduguri Teaching Hospital. Sa'annan akwai makarantar politeknik a Maiduguri mai Suna Ramat Polytechnic. Sauran Makarantu zirfin ilmi sun hada da College of Agriculture, Sir Kashim College of Education da Mohammed Goni College of Islamic and Legal Studies. Sa'annan akwai makarantun sakandare da dama a Maiduguri.

Masaukin ba'ki[gyara sashe | Gyara masomin]

Wuraren suakan ba'ki a Maiduri sun hada da Lake Chad Hotel, Dujima Hotel, Deribe Hotel, Ali Chaman Guest Inn da kuma Maiduguri International Hotel.

Nishadi da wuraren bude ido[gyara sashe | Gyara masomin]

Ba'ki a Maiduguri sukan iya ziyartan makeken kasuwan litinin, fadan mai girma shehun Borno da kuma gidan zoo na Kyarimi Park wanda yake tsakiyan birni Maiduguri.

Addini[gyara sashe | Gyara masomin]

Yawancin mazauna birnin Maiduguri dai Musulmai ne. Amma akwai mabiya addini krista da dama a garin. Akwai manyan majami'o'i a garin kamar babban majami'an dake kan titin Kiri Kasamma. Maiduguri yayi suna kwarai wajen karatun alkur'ani a inda dalibai daka dukkan fadin Najeriya suke zuwa garin don neman ilmi. Manyan masallatai a garin sun hada da masallachin Mai Deribe, masallacin Madinatu, Masallacin Kofar Shehu, Masallacin Indimi da Masallacin Ibrahim Saleh. Akwai shahararrun malaman addinin Musulunci da dama a Maiduguri. A shekaran 2009, wani malamin addinin Muslunci wanda aka fi sani da Mohammed Yusuf ya tada fitina a garin a inda yake ikirarin ya'ki da gwamnati da kuma ilmin boko wanda a ganinsa yana lalata al'umma. Sanda aka yi wajen mako guda ana fafatawa tsakanin sojoji da 'yan sanda da kuma magoya bayan Mohammed Yusuf. Wannan tarzoma tayo sanadiyyar rasa rayuka da dama. Daga karshe jami'an gwamnati sun ci galba kan Mohammed Yusuf wanda sojoji suka cefke kuma suka dan'ka a hannun 'yan sanda. A hannun 'yan sandan Mohammed Yusuf ya rasu. 'Yan sanda sun yi ikirarin cewa ya rasu ne a yayin da ake bindige shi lokacin da yake kokarin kubucewa. Masu bin hakkin bil Adama sun yi harsashen cewa kisan gilla a kayi masa.