Jump to content

Damboa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Damboa

Wuri
Map
 11°09′N 12°45′E / 11.15°N 12.75°E / 11.15; 12.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Borno
Yawan mutane
Faɗi 233,200 (2006)
 Yawan mutane 37.5 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 6,219 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Wani yanke a domboa na jahar barno

Damboa ƙaramar hukuma ce dake Jihar Borno Nijeriya. H Shelkwatar ƙaramar hukumar na nan ne a cikin garin Damboa. Tana da girman ƙasa kimanin 6,219 km² da kuma yawan jama'a da suka kai 233,200 tun daga alƙaluman ƙidayar shekara ta 2006.[1]

Lambar aika saƙo zuwa ƙaramar hukumar ta postal itace 601.[2] Asalin mazauna ƙaramar hukumar Damboa sune Mutanen Marghi, amma saboda haɓakar tattalin arziki Damboa ta hanyar sana'ar kamun kifi a wancan lokaci yasa aka samu mutanen Kanuri da wasu suke yawan kai komo a Damboa har yakai ga sun zama mazauna garin da auren matan garin Damboa. Hakan yasa a, yawancin mutanen Damboa akasarin su rabi Kanuri ne kuma rabi Marghi, dukda haka dai har yanzu akwai gidajen Marghi tsantsa waɗanda basu cuɗanya ba. Sanadiyar cuɗanyar al'ada a garin yasanya yawancin ƴan'asalin garin Damboa sunfi son jingina su da Marghi wasun su kuma Kanuri, amma dai ayau a Damboa akwai mutanen Marghi waɗanda sune ke da rinjaye da kuma mutanen Kanuri waɗanda suke binsu kuma suna zaune a garin kansu ɗaya.[1]

Dattawan Damboa

[gyara sashe | gyara masomin]

ENGR.(Dr) Mohammed Abba Gana[3][circular reference]

Comrade Modu Shettima

Alhaji Abaya Lawan

Alhaji Bulama Korede

Karagama M. Kauji

Malami Wakil Korede

Late Dr. Lawan Kabu

Late Alaji Malam Gaji Damboa

Hon Grema Umar

Mustapha Zarma Koljiri

Modu Yerima Gumsuri

Late Babagana Abbas Dawa

Habu Hong

Babagana Musa Kauji

Alhaji Kaumi Damboa

Mohammed Salisu

Ayemu Lawan Gwasha

Mustapha Tokebe

Karagama Yaga

Karagama Azir

Lawan Makinta

Alhaji lawan kolo Gumsuri

Abdullahi Karagama

Habu Daja Damboa

Lawan Kolomi (LK)

Barr. Mohammed Wakil

Prof. Adamu Garba Alooma[4]

Adamu Tubo Usman

Alamin Mohammed Gumsuri

Alhaji Darman Korede

Alhaji Bukar Petrol

Malam Mustapha Gaji[5]

Tana ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi goma sha shida da suka kafa Masarautar Borno kafin ta kafa Majalisar Masarautar Damboa, wata jiha ta gargajiya da ke Jihar Borno, Najeriya.[6]

Haihuwa da mazaunanta masu shahara

[gyara sashe | gyara masomin]

Haihuwa masu shahara da mazauna Damboa na yanzu da na baya sun haɗa da:

Mohammed Abba Gana, Tsohon Ministan FCT, Kwamishina Jihar Arewa maso Gabas[7]

Jami'ar Fasaha ta Noma ta Tarayya Damboa (An gabatar da ita)

Kwalejin Fasaha ta 'Yan Mata ta Gwamnati Damboa

Makarantar Sakandare ta Ranar Gwamnati Damboa

Makarantar Sakandare ta Ranar Gumsury

Makarantar Firamare ta Tsakiya Damboa

Makarantar Firamare ta Kasugula Damboa-

Firamare ta Sabuwar Makarantar Damboa

J S S DAMBOA

MAKARANTAR FARAMA TA GARJANG


  1. 1 2 Brinkhoff, Thomas (2013-11-20). "Damboa (Local Government Area, Nigeria) – population statistics, map and location". www.citypolulation.de. Retrieved 2014-05-21.
  2. "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2012-11-26. Retrieved 2009-10-20.
  3. "Mohammed Abba Gana - Wikipedia"
  4. "LG Polls: Two professors, 26 others contest chairmanship posts in Borno". Premium Times. 27 November 2020
  5. "Zulum, COAS Inspect Maiduguri - Damboa Road, Pledge Adequate Security"
  6. Nigeria (2000). Nigeria: a people united, a future assured. Vol. 2, State Surveys (Millennium ed.). Abuja, Nigeria: Federal Ministry of Information. p. 106. ISBN 9780104089.
  7. Hamidu, L. J.; Molta, N. B. (1989). "Guinea worm (Dracunculus medinensis) infection in Mafi and Kawaram, Borno State". AfricaBib. 6–7: 106–114. Retrieved 2014-07-01.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.