Abba Kyari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Abba Kyari
gwamnan jihar Kaduna

28 Mayu 1967 - ga Yuli, 1975 - Usman Jibrin (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 17 Nuwamba, 1938
ƙasa Najeriya
ƙungiyar ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 25 Nuwamba, 2018
Karatu
Makaranta Kwalejin Barewa
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Abba Kyari OON (an haife shi a ranar 23 ga watan Satumba shekara ta 1952 - sannan kuma ya rasu a ranar 17 ga watan Afrilu shekara ta 2020) wani babban lauya ne kuma dan Najeriya wanda ya yi aiki a matsayin Shugaban Ma’aikata na Shugaban Najeriya daga watan Agusta shekara ta 2015 zuwa watan Afrilun shekara ta 2020.

Rayuwar farko[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Kyari a ranar 23 ga watan Satumba shekara ta 1952, daga gidan dangin Kanuri daga Jihar Borno . Ya fara karatu a St. Paul ta College a garin Wusasa da ke Zariya, kuma daga baya ya shiga cikin sojojin Najeriya wadannan shawara daga Mamman Daura da kuma Ibrahim Tahir . A shekara ta 1976, ya hadu da Janar Muhammadu Buhari wanda a lokacin yana Gwamnan jihar Borno .

Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ya kammala karatun digiri na farko a fannin ilimin zamantakewar dan adam daga Jami'ar Warwick a shekara ta 1980, sannan kuma ya samu digirin lauya daga Jami'ar Cambridge . An kira Kyari zuwa Lauyan Najeriya a shekara ta 1983 bayan ya halarci Makarantar Koyon Lauya ta Najeriya . A shekarar 1984, ya sami digiri na biyu a fannin shari'a daga Jami'ar Cambridge. Daga baya ya halarci Cibiyar bunkasa cigaban kasa da kasa ta Lausanne, Switzerland, sannan a cikin shekara ta 1992 da kuma shekara ta 1994 ya shiga cikin Harvard Business School 's.

Ayyuka[gyara sashe | Gyara masomin]

Abba Kyari ya yi aiki da kamfanin lauyoyi wato Fani-Kayode da Sowemimo na wani lokaci bayan dawowarsa Najeriya.

Daga shekara ta 1988 zuwa shekara ta 1990, ya kasance Edita a kamfanin New Africa Holdings Limited Kaduna . Ya kuma yi aiki a matsayin kwamishinan gandun daji da albarkatun dabbobi a jihar ta Borno a cikin shekara ta 1990s.

Daga shekara ta 1990 zuwa shekara ta 1995, Abba Kyari ya kasance sakatare a hukumar bankin African International Bank Limited, reshen bankin Credit and Commerce International .

Kyari ya kasance babban darakta mai kula da ayyukan gudanarwa a bankin na United for Africa, daga baya kuma aka nada shi babban jami'in gudanarwa . A shekara ta 2002, an nada shi darakta a hukumar Unilever Nigeria, sannan daga baya ya yi aiki a hukumar Exxon Mobil Nigeria.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa[gyara sashe | Gyara masomin]

A watan Agusta na shekara 2015, an nada Kyari a matsayin Shugaban Ma’aikata na Shugaba Muhammadu Buhari . A matsayinsa na shugaban ma’aikata, ana daukarsa a matsayin fuskar “kabal” kuma mutum ne mafi karfi iko a gwamnatin Buhari.

A lokacin wa'adin mulkin farko, ya yi aiki galibi a bayan fage don aiwatar da ajandar shugaban kasa. A cikin shekarar 2019 tare da sake zaben Buhari a karo na biyu, ya umarci majalisar ministocinsa da su gabatar da duk wata bukata ta ofishin Kyari - ya kara inganta tasirinsa a tsakanin bangarorin gwamnati, kuma ana yi masa lakabi da ainahin shugaban gwamnati.

A shekara ta 2017, bayan bayanan sirri da aka bankado, Kyari ya shiga cikin bahasin jama'a tare da Shugaban Ma'aikatan Gwamnati, wanda daga baya aka cire shi daga mukaminsa aka kama shi. A shekara ta 2020, a wani bayanin da ya bayyana, Babagana Monguno mai ba da shawara kan tsaro na kasa ya zargi Kyari da tsoma baki cikin harkokin tsaron kasa.

Iyali[gyara sashe | Gyara masomin]

Abba Kyari ya auri kanwar Ibrahim Tahir, kuma sun haifi ‘yaya hudu da it a, sune: Aisha, Nurudeen, Ibrahim, Zainab.

Mutuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

A ranar 24 ga watan Maris shekara ta 2020, an bayyana cewa Kyari yayi gwaji na cutar ta COVID-19, kuma aka gano yana dauke da cutar, bayan wata ziyarar aiki da ya yi zuwa kasar Jamus kwanaki tara da suka gabata. Akwai rahotanni da ke cewa an fitar da shi daga kasar don neman magani, kuma daga baya Reuters ya ruwaito cewa yana da "tarihin matsalolin rashin lafiya, ciki har da ciwon sukari ".

A ranar 29 ga watan Maris shekara ta 2020, Kyari ya sanar da cewa an dauke shi daga keɓewa da aka yi zuwa Abuja zuwa Legas don “maganin rigakafi” Daga baya Abba Kyari ya mutu da yammacin ranar 17 ga watan Afrilu shekara ta 2020 yana da shekara 67. Jaridar The Economist ce ta yaba masa a matsayin "babban mutum ne mai mutunci da daraja wanda ya tafi da zuciya.

Girmamawa da kyaututtuka[gyara sashe | Gyara masomin]

Jami'in Umurnin Nijar (OON) Ribbon bar of the Order of the Niger.gif</img> Darajar kasa a Najeriya

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]