Kaduna (jiha)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Globe icon.svgKaduna
Kaduna State (en)
Kaduna State Collage.jpg

Suna saboda Kaduna
Wuri
NigeriaKaduna.png
 10°20′N 7°45′E / 10.33°N 7.75°E / 10.33; 7.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Kaduna
Yawan mutane
Faɗi 8,252,366 (2016)
• Yawan mutane 179.19 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 46,053 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Arewa ta Tsakiya
Ƙirƙira 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Majalisar zartaswa ta jihar Kaduna
Gangar majalisa Kaduna State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 720001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-KD
Wasu abun

Yanar gizo kadunastate.gov.ng

Jihar Kaduna wacce ake mata da kirari wato(Centre of learning) jiha ce dake arewacin Najeriya. Babban birnin jihar na da suna daya a jihar, birnin jihar Kaduna wanda ya kasance shine na 8th mafi girman birni a kasa kamar yadda a shekara ta 2006. An kirkire ta a shekara ta alif 1967, da sunan Jihar Tsakiyar Arewa, wanda kuma yake dauke da jihar Katsina ta yanzu, Kaduna ta samu iyakar ta ne a shekara ta alif1987. Itace jiha ta uku a girman kasa kuma ta hudu a yawan mutane jihohin Najeria, Ana ma jihar Kaduna lakabine da Cibiyan koyon Ilimi (Centre of Learning,) saboda ta kasan ce manyan makarantun gaba da sakan diri a jihar masu muhimmanci, kamar su Jami'ar Ahmadu Bello, Jami'ar Tsaron Najeriya da sauran su.[1]

Asalin suna[gyara sashe | gyara masomin]

Lambar mota ta jahar kaduna
Kada

Jahar Kaduna ta kasance ta samo sunan ta Kaduna ne daga kalmar kada, jam'in kalmar Kadduna, sai aka cire harafin ''D" sai ya koma "Kaduna". A wani fadin kuma an ce kalmar ta Kaduna ta samo asali ne daga yaran Gwari, sun kasance "Odna" suna nufin "Kogi" kasancewar kaduna a zagaye take da rafuka. Tambarin jahar kaduna dai shi ne hoton Kada.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Gadar masallacin sultan bello a Kaduna
Sarauniya amina lokacin da take mulki
Kada
Crocodile

A zance mafi inganci ba a san lokacin da mutane suka fara rayuwa ba a yankin Kaduna, amman akan iya tina garin a wasu ma'auni na tarihi da suka shude, kuma hakan ya faru ne kasancewar yawan kabilun da ke zaune a cikin garin, Hakika birnin ya kafu ne tun kafin zamanin Usman dan Fodiyo wato tun tale-tale a shekarar, birnin Kaduna ya kasance cibiyar jamhuriyyar Arewa tun da ga shekarar 1917, har zuwa shekarar 1967, tarihi ya nuna cewar an mallake kaduna ne ga masu mulkin mallaka na turawan kasar Birtaniya, babban kwamandan yakin mulkin mallaka Frederick Lugard ya kwace Kaduna a shekarar 1897, da shi da sauran yan koransa. Daga baya kuma suka yi hadin gwuiwa tsakanin Kudancin Najeriya da kuma arewacin Najeriya a shekarar 1913. Wasu daga cikin tsofaffin garuruwan Kaduna sun hada da Zariya, Kafanchan da kuma Nok, wanda wadannan garuruwan tarihi ya kasa riskan farkon garuruwan da tarihinsu tin asali. Garin Zaria shi ne tsohon gari a duk fadin yankin Kaduna, wanda ake tunanin an kafa garin a shekarar 1536, wanda a wannan lokacin garin ba ya da suna, wanda daga bisani kuma aka saka ma garin sunan wata shahararriyar sarauniya wato Amina.


Sannan Kaduna ta kasance cibiyar addinin musulunci a yankin arewa, kuma daga ciki ne aka baiwa Katsina jaha, birni ne na Hausawa ko dayake daga baya Kaduna ta kasance tana daya daga cikin manyan biranen da sukafi tara kabilu daban-daban, a kalla akwai kabilu acikin Kaduna da suka kusan 57. jahar Kaduna a da ta hada manyan jahohi a cikinta irin su Katsina, kafin daga bisani aka cire su aka mayar da su jahohi masu zaman kansu, a da jahar Kaduna ita ce babban birnin tarayyar yankin arewacin najeriya a zamanin mulkin mallaka na turawa, kafin a bata babban birnin, da Zungeru a1903 zuwa1923) dake Lokoja a(1897 zuwa 1903) su ne manyan biranan. a shekarar 1923 zuwa 1966 aka bama Kaduna babban birnin tarayyar yankin arewacin najeriya. Jahar Kaduna ita ce ta hudu 4 a jadawalin jahohin da suka fi fadin kasa a Najeriya, kuma sannan ita ce ta 3 a jahohin da suka fi kowanne yawan mutane a Najeriya. Babban Birnin Jahar Kaduna Shi ne Kaduna

Babban Kogin Jahar Kaduna kenan wanda ake tinanin jahar ta samo suna daga gare shiTaswira[gyara sashe | gyara masomin]

Jahar Kaduna tana da matukar fadin gaske, wanda fadin kasarta ya kai kimanin kilomita 46,053 km2 k, Kaduna ita ce jaha ta Hudu da ta fi kowacce jaha girman kasa, kuma tana da kananan hukumomi guda 23, kowacce karamar hukuma ta na da shugaba da kananan garuruwa, kananan hukomomi su ne kamar haka:

jihar kaduna
wannan sashin jihar kaduna kenan daga cikin taswirar Nijeriya.
Adadi Karamar Hukama Fadin Kasa Shuwagabanni
1 Birnin Gwari
2 Chikun
3 hukumar Giwa
4 Igabi
5 Ikara
6 Jaba
7 Jama'a
8 Kachia
9 Kaduna ta arewa
10 Kaduna ta kudu
11 Kagarko
12 Kajuru
13 Kaura
14 Kauru
15 Kubau
16 Kudan
17 Lere
18 Makarfi
19 Sabon-Gari
20 Sanga
21 Soba
22 Zangon-Kataf
23 Zariya

Mulki[gyara sashe | gyara masomin]

Nasir el Rufa'i da gwamna Lalong na jahar plateau

A jahar Kaduna akwai masu mulki daban-daban da suka hada da, sarakuna da zababbun shuwagabanni na mulkin dimukuradiya, a jahar ta Kaduna akwai Gwamna, Yan Majalisa, 'yan majalisar dattijai, da kuma Sarakuna, masu mulkin gargajiya. shuwagabanni a bangaran dimukuradiya ana zaban su ne duk bayan shekaru Hudu, su kuma sarakunan gargajiya suna gada ne a wajen iyaye da kakanni, amman gwamna yana da cikakken ikon da zai iya cire kowanne sarki a jahar.

Dimukradiya[gyara sashe | gyara masomin]

A jahar kaduna akwai gwamna da mataimakin gwamna[2][3] wadannan su ne masu cikakken mulki a cikin jahar ta Kaduna, kuma zabansu ake yi a duk bayan shekaru hudu, wanda yanzu haka Mallam Nasir Ahmad el-Rufa'i shi ne gwamnan jahar Kaduna da kuma Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiyar gwamnan jahar ta Kaduna. A tsarin mulkin dimukradiya akwai yan majalisun jaha masu kula da dokokin jahar da kuma tsarinta, sannan akwai sanatoci uku masu kula da yanki uku na Jahar Kaduna sune; Suleiman Abdu Kwari , Danjuma Laah da kuma Uba Sani.

Mulkin Gargajiya[gyara sashe | gyara masomin]

gadar masallacin sarkin musulmai bello kaduna
Shehu Idris Sarkin Zazzau

Akwai sarakuna da hakimai a kowanne karamar hukuma da kuma gunduma, amman da manyan sarakunan gargajiya su ne kamar haka; Sarkin Zazzau Shehu Idris, sarkin Birnin gwari, sarkin Nok da kuma sarkin Kafanchan, wadannan sarakunan suna da ka'idojin salan mulki ga iya mutanan su kadai, sannan gwamnan jahar yana da cikakken ikon da zai sauke su ya daura wanda yake so.

Tambarin kasar Hausa
Wannan tambarin kasar Hausa kenan. Kaduna tana daya daga cikin jahohin Hausa.

Al'ada[gyara sashe | gyara masomin]

                                     Jahar Kaduna jaha ce mai tarin al’adu da ire iren abinci daban-daban Kamar haka:
 1. Hausawa
 2. Gwarawa
 3. Katafawa
 4. Birom da dai sauran
 • .Ire iren abinci:

Tuwon masara da na dawa,dana gero da dan wake da dambu da fate da doya da dankalin Hausa da rogo da koko da dai sauran su.

Addini[gyara sashe | gyara masomin]

Addinai biyu sune manyan addinan jahar Kaduna, wato addinin Musulunci da kuma addinin kiristanci, kasancewar addinai ne manya akwai alaka mai tsami a tsakaninsu musamman a shekara ta 2000 zuwa ta 2001 an samu rikicin addini a jahar kaduna a bisa dalilin sharia'ar Musulunci da musulmai sukai kokarin assasawa amma sai aka samu rashin jituwa da kiristoci wai suna tsammanin in har shari'ar musulunci ta kafu, to suma zai shafesu shi yasa suka ki amincewa a dalilin haka rikici ya balle inda aka samu asarar rayuka da dimbin dukiya mai tarin yawa, bayan haka akasa Mutane 1000 suka rasa rayukansu. Bayan haka an kara samun rikicin addini a shekarar 2002 amma a halin yanzu akwai zamantakewa mai karfi tsakanin addinan guda biyu.

Kiristanci[gyara sashe | gyara masomin]


Musulunci[gyara sashe | gyara masomin]

File: sultan bello mosque by Anasskoko 03.jpg\masallacin da yamma

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Ilimin Zamani[gyara sashe | gyara masomin]

A fagen Ilmi kaduna ce cibiyar ilimi a arewacin Najeriya kaduna ce cibiyar makarantar horar da jami'an tsaro ta kasa wato Nigeria Defence Academy an kafaTa ne tun a shekarar 1964. Sai kuma babbar makarantar kimiyya da fasaha dake kaduna, wato Kaduna Polytechnic an kafa ta ne a shekarar 1968, sai kuma jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya ita kuma ta kafu a shekarar 1962.Bayan haka akwai Jami'ar jahar Kaduna (kasu) da Nuhu bamalli polytechnic Zaria da college of education gidan waya da dai sauran manyan cibiyoyin ilimi. Lallai kaduna duniya ce ta ilmi wannan dalilin ne yasa kaduna tayi fice a jahohin Nigeria ta ko'ina ana barkowa daga sassa daban-daban na Najeriya ana wajajeu n neman ilimi a jahar ta kaduna domin ita jahar kaduna ta bambanta da sauran jahohin Arewacin Najeriya.

Jadawalin manyan makarantu[gyara sashe | gyara masomin]

 • Jami'ar Jihar Kaduna
 • Kwalejin Horar da Manyan Jami'an Soja Nigerian Defence Academy' (NDA), Kaduna
 • Jami'ar Greenfield University Kaduna
 • Kwalejin share fagen shiga jami'a wato National Open University of Nigeria. Kaduna.
 • Air Force Institute of Technology, Kaduna
 • Kwalejin horar da malamai National Teachers Institute (NTI), Kaduna
 • Kwalejin unguwar-zoma School of Midwifery Kaduna
 • Kaduna Polytechnic (1968), Kaduna
 • Hukumar kula da ilimin addinin Musulunci da harshen Larabci
 • Kaduna Business School.

Ilimin Addini[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin jahar kaduna ana karantar da ilimin addini matuka, cibiyar addini na bangaren Izala, shi'a, Ɗariƙar Tijjaniya da salafiyya duka suna cikin garin jahar kaduna.

Gina gine[gyara sashe | gyara masomin]

Gina-ginan al'ada[gyara sashe | gyara masomin]

Wani masallacin juma'a na ginin al'ada a zaria kaduna
ginin zamani na hedikwatar Jama'atul nasril Islam kaduna

.

Gina-ginan zamani[gyara sashe | gyara masomin]

wani ginin hotal na zamani a kaduna

Kiwon Lafiya[gyara sashe | gyara masomin]

Jahar Kaduna ta na da manya asibitoci da kananan gurin kula da lafiya sama da dubu 10 a fadin jihar


Wasanni[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai dandalin Murtala Mohammed Square inda ake wasanni da kuma motsa jiki, a ciki akwai Kaduna Polo Club da kuma Kaduna Golf Club kuma akwai sitadiyam mai suna Ahmadu Bello Stadiyam da Ranchers Bees Stadiyam


Sadarwa[gyara sashe | gyara masomin]


Kafofin yada labarai (Talabijin)[gyara sashe | gyara masomin]

 • Nigerian Television Authority Kaduna (NTA)
 • Kaduna State Media Corporation TV (KSTV)
 • Desmims Independent Television (DITV)
 • Liberty TV

Kafofin yada labarai (Gidan Rediyo)[gyara sashe | gyara masomin]

A.M masu nisan zango sun hada da:

 • 639 MW – Kada 1 (KSMC)
 • 747 MW – Nagarta Radio
 • 594 MW – FRCN (Hausa), Kaduna
 • 1107 MW – FRCN (English), Kaduna

F.M masu matsakaicin zango sun hada da:

 • Brila FM
 • Kada 2 FM, Kaduna (KSMC)
 • Capital Sounds FM, Kaduna (KSMC)
 • Liberty Radio (English) Kaduna
 • Karama FM, Kaduna (FRCN)
 • Freedom Radio FM, Kaduna
 • Supreme FM, Kaduna (FRCN)
 • Alheri Radio FM, Kaduna
 • Invicta FM, Kaduna
 • Liberty Radio (Hausa) Kaduna
 • Ray Power FM Kaduna
 • Vision FM

Tattalin arziki[gyara sashe | gyara masomin]

Kaduna cibiya ce ta masana'antun arewa,kamar masana'antar karafa, masaka,matatar man fetur ta ƙasa, ginin tukwane,Kaduna garine wanda ake kasuwanci kasancewar yawan mutane da kuma cunkosa,akwai kasuwanni dayawa a cikin garin kaduna,galibi ma kusan kowanne anguwa a cikin babban birnin kaduna tana da kasuwan ta.

Masana'antu[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin kaduna akwai babban kampanin matatan mai, me suna kaduna Refining and Petrochemical Company (KRPC),wanda daya ne daga cikin manyan kampanonin matatan mai da'ake dasu a Najeriya [4][5]

Kasuwanni[gyara sashe | gyara masomin]

Jahar tana da manyan kasuwanni kaman su kusuwan kasuwar sheikh Abubakar gumi,fanteka,kasuwar chechenia, kasuwan magani,kasuwar kawo, kasuwar bacci,kasuwan tudun wadan zaria.

Sufuri[gyara sashe | gyara masomin]

Babbar hanyar data ratsa ta cikin gari ana kiranta Ahmadu Bello way. Kaduna tanada babbar kasuwa wadda aka gina tun a shekarun 1990s bayan ta fuskanci mahaukaciyar gobara. Acikin garin kaduna akwai hanyoyin jiragen kasa wadda ake sufuri daga kaduna zuwa wasu sassan Nigeria.

Jiragen kasa[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai hanyoyin layin dogo na jiragen kasa wadanda aka gina tun a watan satumba shekarar alif 2009 mai nisan tazarar kilomita 1,435 mm (4ft 81/2) zuwa babban birnin tarayya Abuja.[6]

Jiragen sama[gyara sashe | gyara masomin]

Chanchangi Airlines na jihar kaduna

bayan haka akwai filayen jiragen sama guda biyu wato Filin Jirgin Saman Jihar kaduna da kuma filin jirgin sama na chanchangi wato Chanchangi Airlines wadda ake sufuri daga jahar zuwa jaha ko daga Nigeria zuwa kasashen ketare.

Sufurin motoci[gyara sashe | gyara masomin]

Jahar kaduna tana da hukumar dake kula da tafiye-tafiye a fannoni sifirin motoci, wacce ak kira da KSTA.

.

Wuraren bude ido[gyara sashe | gyara masomin]

[7]

 • Lugard Hall
 • Government Monument Bridge
 • General Hassan park
 • Man-made kaduna
 • Nok Terra Cotta
 • Nok Village
 • Cultural kaduna
 • National museum
 • Jakaranda pottery
 • kaduna souvenir

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]

Sanannun mutane mazauna kaduna[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. https://www.britannica.com/place/Kaduna-Nigeria
 2. http://www.highcourt.kd.gov.ng/lawal_bello.html
 3. https://en.wikipedia.org/wiki/List_of_Governors_of_Kaduna_State
 4. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :1
 5. "Kaduna Refining and Petrochemical Company (KRPC)". www.nnpcgroup.com. Archived from the original on 2019-06-27. Retrieved 2019-08-01.
 6. Muhammad, Hamisu (23 July 2016). "A memorable trip on the Abuja-Kaduna train". Daily Trust.
 7. learn about kaduna. Learn about kaduna state.
 8. Nossiter, Adam (2010-01-17). "Lonely Trek to Radicalism for Terror Suspect". The New York Times.


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara