Jump to content

Kagarko

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kagarko

Wuri
Map
 9°27′N 7°41′E / 9.45°N 7.68°E / 9.45; 7.68
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Kaduna
Yawan mutane
Faɗi 239,058 (2006)
• Yawan mutane 128.25 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 1,864 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
62394-Leherketa_Nigerian_2007an
Kagarko post ofis
Open fields in kagarko
Shrubs acikin kagarko
A_bridge_on_a_flowing_river

Kagarko karamar [1]hukuma ce a jihar Kaduna, a Najeriya. Hedkwatarta tana cikin garin Kagarko. Ta mamaye yanki mai girman 2,356 km2 da yawan jama'a 239,058 dangane da ƙidayar 2006. [2] Nasara Rabo ke jagorantar Ƙaramar hukumar. Lambobin tura saƙo zuwa yankin sune 802.[3][4]

Karamar hukumar Kagarko (Wogon) tana da iyaka da karamar hukumar Kachia a arewa, karamar hukumar Jaba daga gabas, jihar Neja zuwa yamma da kuma babban birnin tarayya Abuja a kudu.[5][6]

Yaruka/Kabilu.

[gyara sashe | gyara masomin]

Mutanen dai manoma ne. Mutanen Batinor (Koro) sune ke da rinjaye a yankin. Sauran sun hada da Fulani, Gbagyi, Ham, Hausa da Adara . Suna aiki tukuru kuma galibi manoma, kusan kashi 70% na ginger da ake nomawa a jihar Kaduna daga Kagarko suke.[7][8]

Sanannun mutane a Kagarko.

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. Nenadi Usman. Tsohuwar sanatan a kudancin Kaduna kuma tsohuwar ministar kuɗi
  2. Caleb Zagi. Tsohon sanatan a kudancin Kaduna. #Muhammad Bello Umar Kagarko. Tsohon kwamishina na kana nan hukomomi kuma kwamishina na ilimi.[9][10]

Kujerun gargajiya.

[gyara sashe | gyara masomin]

Kagarko ya ƙunshi sarakuna uku:

  1. Masarautar Kagarko : Mai martaba Sarkin Kagarko Alh. Sa’ad Abubakar, mai hedikwata a Garin Kagarko;

2. Jere Royaldom : Sarkin Jere, Marigayi Dr. Sa'ad Usman (OFR)

3. Koro masarautar : Ere-Koro, Ere Yohanna Akaito (JP), mai hedikwata a Kurmin Jibril (Maraban Kubacha) ;

  1. "The Tinɔr [=Koro Waci] language of Central Nigeria and its affinities" (PDF). 20 May 2009. p. 1. Retrieved May 9, 2025.
  2. "Kaduna State of Nigeria". City Population. Retrieved September 26, 2020.
  3. "Kaduna LG Polls: APC humbles PDP, wins 15 chairmanship seats". 2021-09-07. Retrieved 2022-03-14.
  4. "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2009-10-07. Retrieved 2009-10-20.
  5. "Latest violence in Southern Kaduna Longest on record - Report". Premium Times Nigeria. February 12, 2017. Retrieved August 1, 2020.
  6. "Kaduna-State-Political-Map". VON. Retrieved August 7, 2020.
  7. Kagarko, Kaduna State, Nigeria". Retrieved September 25, 2020.
  8. Tauna, Amos (November 22, 2023). "Kaduna Assembly takes over LG legislative duties, suspends eight councillors". Retrieved July 27, 2024
  9. "Kagarko Climate, Weather By Month, Average Temperature (Nigeria) - Weather Spark". weatherspark.com. Retrieved 2023-09-10.
  10. "Kagarko, Kaduna, NG Climate Zone, Monthly Averages, Historical Weather Data". tcktcktck.org. Retrieved 2023-09-10.