Jump to content

Adarawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adarawa
Yankuna masu yawan jama'a
Najeriya

Adarawa (kuma Eda da Kadara ), ƙabilu ne a yankin Tsakiyar Najeriya da ke magana da yaren Adara, harshen Arewacin Filato na Najeriya.[1]Mr. Dio Awemi Maisamari shine shugaban kungiyar mutanen adara watau Adara Development Association (ADA)[2] tare da kuma mataimakin sakatare Luke Waziri.[3]

Yawan jama'a.

[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu kimantawa suna sanya yawan mutanen Adara a kusan 381,000. [4]

Kimanin kashi 55% na Adara Kiristoci ne yayin da wasu kuma suke bin addinin Islama. [4]

Ana iya sumun mutanen Adara a yankunan kusa da sahara na Afurka amma a Najeriya kadai ake iya samun asalin su. Ana iya samunsu kuma a Jihar Benue da wasu sassan jihar Kaduna kamar kananan hukumomin Kajuru da Kachia dake jihar Kaduna.[5]Unguwanninsu kuma sun hada da suMagunguna, Idazo, Ungwan Galadima, Ungwan Guza, Etissi, Ungwan Ma’aji, Ungwan Dantata, Ungwan Araha 1 & 2, Ungwan Goshi, Ungwan Shaban, Ungwan Jibo, Ungwan Maijama’a, Ungwan Sako, Ungwan Maidoki and Ungwan Masaba.[6]

Rikice-rikice.

[gyara sashe | gyara masomin]

Al’umar Adara sun wahala daga rikice-rikicen kabilanci da ke faruwa a Nijeriya, musamman rikice-rikicen makiyaya da manoma a Najeriya, ciki har da na Jihar Kaduna .

  1. Roger Blench (5 July 2009). "The Eda [= Kadara] language of Central Nigeria" (PDF).
  2. "Tauna, Amos (2021-06-27). "Adara people reject changes in traditional institutions in Kaduna". Daily Post Nigeria. Retrieved 2022-01-16.
  3. "We are suffering under you' -- Adara people write el-Rufai". TheCable. 2019-12-04. Retrieved 2022-01-16
  4. 4.0 4.1 Joshua project entry on the Adara
  5. "PeopleGroups.org. "PeopleGroups.org - Adara of Nigeria". peoplegroups.org. Retrieved 2022-01-16.
  6. Adara people in Kaduna count losses from Kajuru crisis". Vanguard News. 2020-05-23. Retrieved 2022-01-16.