Ekiti

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ekiti


Wuri
Map
 7°40′N 5°15′E / 7.67°N 5.25°E / 7.67; 5.25
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Ado Ekiti
Yawan mutane
Faɗi 3,270,798 (2016)
• Yawan mutane 514.84 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 6,353 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Ondo
Ƙirƙira 1 Oktoba 1996
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Ekiti State (en) Fassara
Gangar majalisa Ekiti State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-EK
Wasu abun

Yanar gizo ekiti.com
Jami'ar adi Ekiti
Ado Ekiti
Mutanen Ekiti
Cikin Ekiti
jami'ar ekiti

Jihar Ekiti Jiha ce da take kudu maso yammacin Najeriya, ta haɗa iyaka daga arewa da Jihar Kwara, da arewa maso gabas ta Jihar Kogi, daga kudu maso gabas kuwa da Jihar Ondo, sannan daga yamma da Jihar Osun. Ta kuma samo sunanta daga mutanen Ekiti ɓangare na Ƙabilar Yarbawa waɗanda suka mamaye mafi yawan yankunan Jihar. An ƙirƙiri Jihar Ekiti daga wani sashe na Jihar Ondo a shekarar alif 1996 sannan babban birnin jihar ita ce Ado-Ekiti.

Tana ɗaya daga cikin ƙananun jihohi a Nijeriya ta fuskar faɗin ƙasa, Ita ce jiha ta 31 a girma a Najeriya, tare da kimanin mutum 3.3 a bisa ƙiyasin shekara ta 2016. Dangane da yanayin ƙasa kuwa, Jihar tana da dazuzzuka masu kwari, a Najeriya a mafi yawancin yankunan Jihar tare da bushashiyar yanayi na Guinea forest Savanna mosaic daga arewacin jihar. A cikin watan Mayu na shekara ta 2022, Jihar Ekiti ta zamo jiha ta farko da ta fara ƙaddamar da bishiya a matsayin tambarinta na gwamnati. A ranar Tunawa da Dajikan Duniya (World Forest Day) ne, Gwamna Kayode Fayemi ya sanar cewa sun zaɓi Icen Obeche a matsayin bishiyar Jihar dangane da muhimmancinta na muhalli, tattalin arziƙi da sauran amfani na gargajiya.

Mazauna Jihar Ekiti ta yau sun kasance tun tsawon lokaci daga Kabilar Ekiti , wani sashe na yaren yarbanci, da tsiraru daga sashin yaren Akoko-Yoruba. Mafi akasarin mutanen jihar (80%) mabiya addinin kiristanci ne tare da tsiraru daga musulmai (10%) da kuma mabiya addinan gargajiya (5%).

A zamanin da kafin zuwan turawan mulkin mallaka, yankin Jihar Ekiti ta yau ta kasance a ƙarƙashin daular Masarautar Oyo, Masarautar Benin sannan daga bisani Jihohin Ekiti wanda suka samar da Masarautar Ekiti a shekarar 1800. A tsakanin shekarun 1877 zuwa 1893, yankin sun kafta Yakin Kirji tare da sauran yarbawa na gabas don yakar Masarautar Ibadan da kuma sauran Kungiyoyin Yarbawa na Yamma; ya ƙin ya ƙare ne bayan da Turawan mulkin mallaka suka shiga tsakani kuma suka haɗe yankin acikin Yankin mulkin Mallaka na Kudancin Najeriya wacce daga bisani ta zamo Najeriya Turawa a alif 1914. Bayan samun 'yancin kai a 1960, yankin Jihar Ekiti ta yau na daga cikin yankin Yammacin Najeriya kafin zuwa 1967 lokacin da ka raba yankin kuma jihar ta fada karkashin Jihar Yammacin Najeriya. A cikin shekarar 1976 ne aka raba yankin kuma gabashin yankin ta zamo Jihar Ondo. Shekaru ashirin bayan hakan, an raba yankin arewa maso yammacin Ondo (inda ake kira da Ekiti Zone) inda ta zamo Jihar Ekiti.

Tattalin arzikin Jihar Ekiti sun ta'allaka ne akan noma, inda suka fi shukan shinkafa, doya, cocoa, da rogo. Muhimman masana'antu sun hada da masana'antun katakai da wuraren bude idanu. Jihar Ekiti itace ta 19 a cikin Jerin Jihohi Najeriya dangane da Ma'aunin Cigaban Jama'a kuma ana daukar ta a matsayin cibiyar mutanen Ekiti.[1]

Tana da yawan fili kimani na kilomita araba’i 6,353 da yawan jama’a milyan biyu da dubu dari uku da tisa'in da takwas ta da dari tara da hamsin da bakwai (ƙidayar yawan jama'ca shekara 2006). Babban birnin jahar ita ce Ado Ekiti. Kayode Fayemi shine gwamna a Jihar ayanzu bayan yasamu nasara a zaben da ya nema a takarar gwamna a Jihar karo na biyu,ya karba a hannun Ayo Fayose Wanda yazama gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2014. Mataimakin gwamnan shi ne Kolapo Olubunmi Olusola. Dattijan jihar sun hada da: Fatimat Raji-Rasaki, Duro Faseyi da Biodun Olujimi.

Jihar Ekiti tana da iyaka da misalin jihohi biyar, su ne: Kogi, Kwara, Ondo kuma da Osun.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Ekiti jiha ce mai zaman kanta kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Tana daga cikin muhimman garuruwan Yarbawa a Najeriya. Ekiti a matsayin gari kuma alƙaryar ƙabilar yarbawa ta samo asalinta ne daga Oduduwa, wanda shine ya samar da asalin ƙabilar yarbawa duk da cewa akwai labari mai karfi na wanzuwar yarbawa 'yan asalin Ekiti tun kafin kafuwar masarautar Ile Ifẹ.[2]

Akwai muhimman labarai guda biyu dangane da tarihin Ekiti. Na farko ya ƙunshi asalin Ekiti daga Ife. Labarin ya nuna cewa Olofin, daya daga cikin 'ya'yan Oduduwa na da 'ya'ya 16 wanda suka fito tare da sauran mutanensa don neman sabon muhalli suka ratsa ta Iwo - Eleru (Kogon Toka) da ke Isarun kuma suka tsaya a Igbo-Aka da ke kusa da Ile Oluji/Okeigbo.[3]

Olofin da 'ya'yansa da kuma sauran jama'a sun ci gaba da tafiya har sai da suka isa wani kyakyawan waje mai shimfidadden fili Owa-Obokun (Mausarautar kasar Ijesha) sannan kuma Orangun sannan daga bisani suka yanke shawarar tsayawa a Ijesha da Igbomina na Jihar Osun.[3] A yayin da sauran 'ya'yansa 14 suka cigaba da tafiya har suka iso yankin kasar Ekiti ta yau. Sun lura cewa akwai tsaunuka da dama kuma suka kira ta da yarensu "Ile olokiti" wato kasar tsaunuka. A dalilin haka aka sauya kalmar Okiti zuwa Ekiti. Ta haka Ekiti ta samo asalin sunanta daga tuddai/tsaunuka.

Har wayau, ana iya lura da cewa wannna tarihi ta ƙunshi wasu daga cikin masarautun Ekiti amma ba duka kasar Ekiti ba wacce ta kunshi manya manyan birane guda 131, kowacce da masarautar ta da kuma sauran dumbin garuruwan da ke zaman kansu.

Labari na biyu ya ta'allaƙa ne a kan tarihin gaske. An zayyano cewa Oduduwa kakan yarbawa ya yi tafiya zuwa garin Ife (Ife Ooyelagbo) inda ya iske mutane da ke rayuwa a wurin. Daga cikin mutanen da ya iske a yankin sun hada da; Agbonniregun [Stetillu], Obatala, Orelure, Obameri, Elesije, Obamirin, Obalejugbe. An sanar cewa tsatson Agbonniregun [Baba Ifa] sun zauna a yankin, misali kuwa shine Alara da Ajero wadanda sun kace 'ya'yan Ifa. A ta dalilin hakan aka samu kalmar ‘Ado ni ile Ifa’ wato [Ado ita ce gida ga Ifa]. Tun daga lokacin mutanen suke zaune a yankin.

Babu wanda zai iya bada tsayayyen lokacin da waɗannan abubuwa suka faru saboda rashin rubutaccen hujja, amma mutane sun wanzu a Ekiti na tsawon ƙarnuka da dama. Yana nan a rubuce cewa sarakunan Ekiti sun wanzu tun daga ƙarni na 13. Misalin hakan shine zamanin Ewi Ata na Ado-Ekiti a ƙarni na 1400.

Dangane da mutanen Ekiti, Samuel Johnson ya fada cewa:

A tarihance, mutanen Ekiti na daga cikin al'amuran asali na Najeriya waɗanda masu kai farmaki daga gabas suka mamaye (Yarbawa daga Ile Ife). Kalmar Ekiti na nufin "laka/taɓo, kuma ya samo asali ne daga hanyoyi marasa dadin bi na gefen tsaunuka na cikin yankunan kasar. Daula ce mai matukar tsari wacce ke da albarkar ruwaye, wanda ke dauke da harsuna da yaruka da dama a daidai iyakar Neja daga gabas. Mutanen na da bambanci da mutanen Ijesa, musamman ta fuskar "harkokin siyasa" (Samuel Johnson, The History of the Yoruba, 1921). An amince da cewa kakanni na farko na Mutanen Ekiti sun taso ne daga yankin Ile Ife, asalin alkaryar yarbawa zuwa yankin Ekiti ta yau. Dangane da labaran baka da rubuce-rubuce akan tarihin Yarabawa, Oduduwa sarkin Yarbawa yayi tafiya zuwa garin Ife [Ife Ooyelagbo] inda ya iske mutane wadanda ke zaune a wajen. Daga cikin tsofaffin da ya iske a lokacin sun haɗa da; Agbonniregun [Stetillu], Obatala, Orelure, Obameri, Elesije, Obamirin, Obalejugbe. An sani cewa jikokin Agbonniregun [Baba Ifa] sun zauna a Ekiti, misali kuwa shine Alara da Ajero waɗanda sun kasance 'ya'yan Ifa ne. Shi kanshi Orunmila [Agbonniregun] ya kwashe mafi akasarin rayuwarsa a Ado. A dalilin haka ake cewa ‘Ado ni ile Ifa’ [Ado gida ne ga Ifa]. Tun daga lokacin mutanen Ekiti basu kara zama a wannan wuri ba na yanzu. Kasar Ekiti ta farko ta kasu zuwa gundumomi 16 (kuma suna nan har zuwa yau), kowacce da sarkinta watau Owa (wanda kalma ne na gama gari ga mutanenta). Wadanda guda hudu sune madaukaka: (1) Owore na Otun, (2) Ajero na Ijero, (3) Ewi na Ado da kuma (4) Elekole na Ikole. Ƙananan sarakunan Ekiti kuma sun haɗa da (5) Alara na Aramoko, (6) Alaye na Efon Alaye, (7) Ajanpanda na Akure, (8) Alagotun na Ogotun, (9) Olojudo na Ido, (10) Attah na Aiyede, (11) Oloja Oke na Igbo Odo, (12) Oloye na Oye, (13) Olomuwo na Omuwo, (14) Onire na Ire, (15) Arinjale na Ise and (16) Onitaji na Itaji. A wasu lokutan akan sanya Orangun na Ila a cikinsu.

An cire Jihar Ekiti ta yau daga sashin Jihar Ondo a shekarar 1996. Kafin hakan, ta kasance daga cikin yankin gundumar Ondo na Yankin Yammacin Najeriya.

Yanayin ƙasa[gyara sashe | gyara masomin]

Mafi akasarin ƙasar jihar na kan tudu ne, mai tsawon mita 250 daga matakin teku. Jihar na yankin dake ƙarƙashin "dutsen metamorphic"

Kananan Hukumomi[gyara sashe | gyara masomin]

Danjar bada hannu a ekiti

Jihar Ekiti nada Kananan hukumomi guda goma sha shida (16). Sune:

Babbar cocin ekiti


Manyan duwatsun ekiti
Ekiti
Ekiti

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]

Galerry[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Human Development Indices". Global Data Lab. Retrieved 15 December 2021.
  2. "About Ekiti State". Retrieved 2021-07-12.
  3. 3.0 3.1 "How The Ara People Of Ekiti Committed Mass Suicide To Avoid Enslavement". Spread.ng. 2021-03-23. Retrieved 2021-07-12.


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara