Ilmi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
manhajar Koyar da yara

Akan yi wa ilimi kirari da cewa:"Ilimi garkuwar Dan Adam."

Ma'anar Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ilimi shi ne: Sanin abu a bisa hakikaninsa, sani na yanke ba na shakka ba, ko rudu.

Shi ilmi wani irin baiwa ne da Allah Ya ke bayar wa ga bayin sa. Hakika, ilmi ya na tabbatuwa a cikin kwakwalwar dan adam. Mutum mai Ilmi ya sha banban da jahili ta kowacce fuska, saboda mai ilmi yana aiki ne ko barin aiki a sakamakon umarnin da ilmin sa zai ba shi, wato ai, ilmin zai kasance tamkar shi ne linzamin da ke jan ragamar hankalin sa da al’amuran sa.

lallai, ilmi fitila ne da ke haskaka Rayuwa. Duk mutumin da ba shi da ilmi, to hakika, za ka ga rayuwar sa cikin kunci ta ke.

Hanyoyin Samun Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Bincike

Bincike hanya ce ta samu ilimi a wannan zamani da ba kamarta.

  • IYAYE

Hanya ta farko: Iyaye; Ana fara samun ilimin farko ne daga iyaye, musamman Mahaifiya. Daga gareta ne mutum yake fara koyar abubuwa iri-iri. Kamar su cin abinci, sanya tufafi, tarbiyyar rayuwa, tsafta da sauransu. Da taimakon mahaifi kuma yaro ya ke samun Juriya, Dogaro da Kai, Nagarta da kuma tabbatuwa a kan turba ta gari.

  • DANDALI

Hanya ta biyu: Ita ce Dandali ko kuma mu ce rariya ko kan layi. Anan ne yaro yake koyon gane wadansu mutane daban da na gidan su. Kuma a nan ne yaro yake koyon wasanni da koyon zama da jama'a daban.

  • MAKARANTA

Hanya ta uku: Makaranta; Daga hannun Iyaye kuma, sai makaranta. Anan mutum ya ke koyon ilimin Addini da Duniya. A Makarantar ne za a koyawa mutum ilimi daban-daban, tun daga Firamare zuwa Sakandire, har zuwa Jami'ah. A nan a ke samun shaidar karatu babba da karama don aiki a manya ko kananan ma'aikatu.

Nau'o'in Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Nau'o'in ilimi ya kasu ne zuwa gida uku kamar yarda masana suka tsara su.

  • ILIMIN ZAMANI (boko)
  • ILIMIN ADDINI
  • ILIMIN GARGAJIYA

Yanzu zamu dauko su daya bayan daya mudan tattauna akan su, amma a takaice.

ILIMIN ZAMANI (boko)[gyara sashe | Gyara masomin]

Shi ilimin zamani ko kuma muce boko kamar yarda akasarin hausawa muke kiran shi. Ya samo asaline daga Turawa wadanda suka yi mulkin mallaka a kasar mu Najeriya .

Turawan kasar Ingila su ne suka kawo mana ilimin boko a kasarmu ta Najeriya . Sun fara kaddamar da tsarin ilimin boko ne a sashen dukancin Najeriya kafin su gabatar da shi a yankin Arewacin Najeriya . Duk da dai lokacin turawa sun sha wahala harma da yake-yake kafin samun nasarar kaddamar da ilimin zamani a yankin Arewacin Najeriya amma kuma yanzu jama'ar yankin sun karbeshi hannu bibbiyu.

  • tsarin ilimin boko

Ilimin boko ilimine wanda yake da tsare tsare kafin, bayan da kuma lokacin da ake koyar da shi. Akwai tsare-tsare kafin a koyar da ilimin boko, kamar hukumomi daban-daban na ilimi su tsara abin da za'a koyar a shekara-shekara, zangunan karatu da kuma sati-sati, wanda ake kira da (SYLLABUS) a harshen Turanci. Sannan malami yana da tsare-tsaren da zai yi kafin shigar shi cikin aji wanda ake kira [LESSON PLAN] da kuma [LESSON NOTE] a turance.

ILIMIN ADDINI[gyara sashe | Gyara masomin]

Ilimin addini, ilimine da ya samo asali bayan zuwan addinin Musulunci a Kasar Hausa .

  • tsarin Ilimin Addini.

Hanyar da ake bi wajen koyar da ilimin addini a gargajiya shine, idan yaro ya kai kamar shekara bakwai da haihuwa. Ana kaishi makarantar Alkur'ani wadda akafi sani da makarantar allo . Bayan yaro yayi saukar Kur'ani kuma, sai ya tafi makarantar da zai koyi karatun litattafai. Akasarin wannan karatun an fi yin sa ne a masallaci ko a gidan malamin da zai koyar.

ILIMIN GARGAJIYA[gyara sashe | Gyara masomin]

Ilimin gargajiya ilimi ne wanda ake koyon shi akasari a wajen da ake aiwatar da shi. Misali idan anaso yaro ya koyi yarda ake wata sana'a kamar kira , noma , kafinta kokuma jima to ana zaunar da shi ne a inda ake aiwatar da ita wannan sana'a din. A haka har ya koya kuma ya iya. To amma dayake yanzu zamani ya can kuma al'amurra da yawa sun sauya, duk sauran abubuwan da ake koyo a gargajiyance a yanzu an zamanantar dasu. Misali ana koyon noma, kafinta, saka a makaranta tun daga matakin firamare har yazuwa Jami'a .

  • domin karin bayani jeka