Jump to content

Makarantar allo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Makarantar allo
type of educational institution (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na makaranta, residence (en) Fassara da school building (en) Fassara
Nada jerin list of boarding schools (en) Fassara

Makarantar allo ita ce tsohuwar hanyar koyo da koyar da karatun Al-Ƙur’ani mai girma a ƙasar Hausa. A garuruwa kamar Kano da Katsina. A Kano ana sa ran shigowar wannan karatu tun kusan shekaru ɗari (100) shida da sittin a baya, zamanin sarki Yaji Ɗan Tsamiya a shekara ta alif (1349 – 1385) lokacin da Fulani Wangarawa suka zo garin na Kano. A Katsina kuma, ana ganin tun shekaru ɗari shida da sittin da uku baya da suka gabata a zamanin Sarki Muhammadu Korau a shekara ta alif (1384 – 1398) lokacin da Sheikh Abdurrahman Zaite da jama'arsa suka je Katsina.

Wannan makaranta a cikinta ake koyon karatun, Allo da rubutu da kuma haddace Al-Ƙur’anin Mai girma baki ɗaya. Malaman makarantar allo su suke rubuta Al-Ƙur’ani ko dai da ka, ko kuma ta hanyar mai-da-kama.

Wannan wata babbar makarantar Allo ce, ga ɗalibai nan sunata karatu da Allunansu

Tabbas Akwai tarbiyya sosai a makarantar masu yarin yawa a Allo saɓanin yadda wasu suke tunaninsu akai.

Tsarin Makarantar Allo

[gyara sashe | gyara masomin]

Makarantar allo makaranta ce mai tsari sosai. Asali iyaye kan kai yara wannan makaranta kuma yaran da kuma ake kaiwa sai sun kai shekaru shida ko bakwai wanda a wannan lokacin idan namiji ne an yi masa kaciya kenan. Idan aka kai yaro to shi kenan yaro ya zama ɗan makaranta wanda ake kira almajiri. Waɗannan ɗalibai kala biyu ne, akwai wanɗanda a ke kwana a makaranta, akwai kuma waɗanda suke zuwa daga gidajensu, su yi karatu, su koma (kamar dai yanzu yadda ake da tsarin makarantar kwana da kuma jeka-ka-dawo a makarantar boko).

Lokutan Karatu

[gyara sashe | gyara masomin]

A makarantar allo ana karatu kusan sau biyar a kowace rana.

Ana fara zama a ƙarshen dare dab da sallar Asuba (misalin karfe huɗu na asuba kenan a yanzu) har zuwa wayewar gari. Ana cikin wannan karatu ake tashi a je a yi sallar Asubahi sannan a dawo a cigaba da karatu har zuwa wayewar gari. Idan gari ya waye, sai kuma a ɗumama guntun tuwon da ya kwana a ci. Wannan tuwo shi ake ƙira gajala.

Lokaci na biyu kuma, shi ne idan hantsi ya yi, sai kuma a tafi wajen gari a shiga Kisƙali (ɗaki ne da ake yinsa a wajen gari da ciyawa da kara), ko kuma a zauna a gindin visitations. Wannan lokaci yakan zarce har zuwa tsakiyar rana. Daga nan kuma sai a tafi hutu idan rana ta zo tsakiya. A cikin wannan hutun ne ake neman abinci a ci, idan kuma akwai abincin a ajiye sai a ɗauka a ci.

Lokaci na uku kuma shi ne bayan sallar Azahar. Idan aka yi sallar azahar sai kuma a sake zama. Wannan lokaci yakan kai har zuwa kusan da faɗuwar rana. Shi ma wannan lokaci ana cikin karatu ake tashi a yi sallar La’asar.karfe hudu ( 4 )

Sai kuma bayan sallar Magariba. Ana idar da sallar Magariba ake zama na ɗan gajeren lokaci kafin sallar Isha (Idan aka kwatanta da zamani, tsawon wannan karatu baya wuce rabin awa). Wannan shi ake kira karatun Magariba.

Sai kuma bayan sallar Isha. A kan zauna wannan karatu bayan sallar Isha har zuwa ɗaya bisa ukun dare na farko. Wannan karatu shi suke kira ja-dare. Sai dai, akan samu wasu su masu zarce da karatun basa barci. Sannan kuma duk wanda barci ya rinjaya koda ba a kai lokacin tashi ba yakan tashi ya je ya yi.

Waɗannan matakai guda biyar su ne abin da aka sani game da lokutan karatu a makarantar allo ta asali. Haka nan ƙolo da tittiɓiri ba su cika yin ja-dare ba.

Tsarin Shugabanci

[gyara sashe | gyara masomin]

Sanannen abu shi akan samu unguwa guda da ake kira Tsangaya wadda nan ce cibiyar karatun Al-Ƙur’ani a gari. Baƙin malamai, gardawa, da ‘yan gari nan suke zuwa dan koyo da kuma koyar da karatun Al-Ƙur’ani. Saboda haka akwai kyakkyawan tsarin shugabanci a ciki. Yana da matakai kamar haka:

Uban Tsangaya: Uban tsangaya shi ne asalin wanda ya kafa wannan tsangaya, saboda haka shi yake zamowa mai faɗa-a-ji na ƙarshe. Wato shi ne sama da kowa a wannan tsangayar. A wasu lokutan ma akan kira tsangayar da sunansa. Misali, a ce ‘Tsangayar Malam Saleh’.

Mai darasu: Mutum na biyu a tsarin shugabancin tsangaya shi ne Mai darasu; malamin dake bayar da karatu ga gardawa waɗanda a cikinsu wasu ma alarammomi ne. Sai dai, ana raba wannan matsayi ne da na Uban Tsangaya idan ya zama shi Uban tsangayar ba shi da isasshen karatun da zai bayar da darasi. Amma idan Uban tsangaya ya zama yana da karatun da zai bayar da darasu, masu mahinmanchi to shi ne kuma yake zamowa Mai darasu a wannan tsangayar tasa.

Shugaban Gardawa: Muƙami na ƙarshe shi ne jagorancin dukkan almajiran tsangayar wanda suka haɗa da ƙolo, tittiɓiri, gardi, da kuma sauran alarammomi. Dukkan su suna ƙarƙashin shugaban gardawa. Akan zaɓi gardi maras tsoro kuma ƙaƙƙarfa a ɗora masa wannan nauyi. Shugaban gardawa shi yake da alhakin kula da zirga-zigar sauran almajirai ‘yan’uwansa. Ba kasafai ake zuwa gaban Uban tsangaya da matsala ba sai ta kai girman gaske. [1]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-01-28. Retrieved 2021-03-02. More than one of |archiveurl= and |archive-url= specified (help); More than one of |archivedate= and |archive-date= specified (help)