Masallaci
|
type of building (en) | |
|
| |
| Bayanai | |
| Ƙaramin ɓangare na |
wajen bauta, religious building (en) |
| Fuskar |
Islamic architecture (en) |
| Addini | Musulunci |
| Abubuwan da aka hana a wajen |
please take off your shoes (en) |







Masallaci jam'i, ko Masallatai: wajene da musulmai ke bautan Allah (SWA) shikadai Ubangijin kowa da kowa.[1] Da Larabci[2] ana cewa Masjid. A wajen akasarin Musulmai[3], masallaci ya wuce wajen bautan Allah kadai. Musulmai na bauta tareda koyo da koyar da ilimin addinin Musulunci[4] tare da tattaunawa akan matsalolin musulmai tare da neman hanyar warware su a masallaci. A Birtaniya[5] masallatai ne cibiyar matattarar al'umar musulmai tare da koyar da addinin musulunci[4]. Anayin buku-kuwa da taruka a masallaci, musamman ma shagul-gulan daurin aure. Akwai dokokin yadda mutane zasu kasance a masallaci. Daya daga cikin su shine wani bazai takura ma wanda yake bauta ba. Masallatan farko an bude sune a karni na bakwai (7) a fili, amma daga baya an koma ana gina Masallatai a salon gini na Musulunci. Masallatan Quba da masallaci anabi farko farkon masallatai. Akwai masallatai a kowacce Nahiya in banda ta Antarctica.
Masallacin Al Haram a yanzu ya mamaye kimanin murabba'in mita 400,800, wanda ke daukar mutane miliyan hudu a ciki da wajensa lokacin Hajji.[6]
Al-Qur'ani ya bayyana wannan masallacin a matsayin na farko da aka gina a ban kasa domin dan Adam ya bauta wa Allah.[7]
Wannan masallacin, mai suna Al Haram, wato "Mafificin Masallaci" shi ne ya fi ko wanne daraja a duniya baki daya, yana da dadadden tarihi, ya fi ko wanne masallaci daraja da girma da kayatuwa. A zagaye yake d a gine-ginen manyan otal-otal masu kyau da tsari wadanda idan kana daga cikisu ma kana iya hango harabar masallacin da cikinsa.[8]
2. Masallacin Annabi SAW da ke Madinah a kasar Saudiyya[9]
Kingdom of Saudi Arabia Ministry of Information
Bayanan hoto,Mafi darajar wuri a wannan Masallaci shi ne daga tsakiyarsa, inda kabarin Annabi Muhammad SAW ya ke[10]
Wannan masallacin da aka fi sani da masjid An Nabawi, watau "Masallacin Annabi," shi ne masallaci na biyu mafi daraja da kyau da girma bayan na Makkah. Annabi SAW da kansa ya gina masallacin a lokacin da ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina shekara 1439 da ta gabata. A ciki kabarin fiyayyen halitta yake da na manyan abokansa biyu kuma sahabbansa Abubakar da Umar Allah ya kara musu yarda. Gidan Annabi SAW a yanzu haka duk ya shiga cikin masallacin. Ana yi wa masallacin lakabi da 'Koriyar Hubba ta Dan Abdullahi.'[11]
3. Masallacin Kudus da ke Jerusalem a Isra'ila
Al Aqsa Mosque - Jerusalem, PalestineAsalin hoton,Getty Images[12]
Bayanan hoto,Tarihi ya nuna cewa a baya, Annabi Muhammad SAW na jagorantar sallah ne a yayin da ake fuskantar wannan masallaci, kafin daga wata na 17 na hijira, Allah ya umurce shi da maya da alkiblar zuwa Ka'aba, da ke Makkah[13]
Masallaci na uku mafi girma da daraja a ban kasa. Ana kiransa da Al-Aqsa kamar yadda ya zo a Al-Kur'ani mai tsarki ko kuma Baytul-Muqaddas.[14]
An gina Masallacin Al-Aqsa ne a garin birnin Kudus da ke kasar Isra'ila. Masallacin shi kan sa an gina shi ne a wani yanki na Al-Haram ash-Sharif, wato "Mafificin mafaka mai tsarki", wanda su Yahudawa suke kira Temple Mount, wanda shi ne mafi tsarki su kuma a wurinsu. Ta Baitul Mukaddas ne Annabi SAW ya tafi Mi'iraji.[15]
4. Masallacin Hassan na Moroko
Hasumiyarsa ita ce wadda ta fi tsayi da kimanin mita 210. An kammala ginin masallacin ne a shekarar 1993.[16]
5. Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddin a BruneiSultan Omar Ali Saifuddin Mosque - Brunei[17]
An zagaye Masallacin da bishiyoyi da furanni da dama, domin kamanta ni'imar Aljannah Firdausi[18]
Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddien, wani masallacin 'yan sarauta ne da ke garin Bandar Seri Begawan, babban birnin masarautar Brunei. Ana yi wa masallacin kallon wanda ya fi ban sha'awa a yankin Asiya, kuma wata matattara ce ta masu yawon bude ido a Brunei. An kammala gininsa a shekarar 1958, kuma yana daya daga cikin gine-gine da ke nuna bajintar taswirar gine-gine a duniya.[19]
6. Masallacin Zahir da ke Kedah a Malaysia:Zahir Mosque - Kedah, Malaysia[20]
Bayanan hoto,Duk shekara ake gudanar da musabaka a cikin wannan MasallaciMasallacin Zahir, shi ne masallacin jihar Kedah, wanda ke kasar Malaysia, wanda ke tsakiyar garin Alor Star. An gina masallacin a shekarar 1912, da tallafin Tunku Mahmud, dan Sultan Tajuddin Mukarram Shah.[21]
Wannan masallaci babba ne sosai kuma yana da kayan kawa na zamani.[22]
7. Masallacin Faisal da ke Islamabad a Pakistan:Faisal Mosque Islamabad - Pakistan.Masallacin Faisal da ke birnin Islamabad a Pakistan shi ne mafi girma a kudancin Asiya, kuma shi ne na hudu da ya fi girma a duniya[23]
Wannan masallacin shi ne mafi girma a kudu maso gabashi da kudancin Asiya, kazalika shi ne na hudu cikin mafi girman masallatai a duniya. A shekarun 1986 zuwa 1993 shi ne masallacin da ya fi ko wanne girma a duniya, kafin masallacin Hassan na biyu da ke Casablanca a Morocco, da kuma bunkasa Masjid Al-Haram na Makkah da aka yi daga baya, wadanda duk suka doke shi.[24]
8. Masallacin Taj ul da ke Bhopal a Indiya
Taj ul Mosque - Bhopal, India
Asalin hoton,Getty Images
Bayanan hoto,Masallacin na da babban lambu a tsakiyarsa, inda aka dasa wani babban tankin ruwa[25]
Ma'anar sunan wannan masallaci, "Sarkin duk masallatai", kuma yana garin Bhopal ne a Indiya. Ana gudanar da karatun Qur'ani ma a masallacin, da rana. Masallacin shi ne mafi girma a nahiyar Asiya baki daya.[26]
9. Masallacin Badshahi a Lahore, Pakistan
Badshahi Mosque of Lahore - Pakistan
Asalin hoton,Getty Images
Bayanan hoto,Masallacin na daukar masu ibadah dubu 55 lokaci guda wajen sallah, kuma daga waje yana iya daukar masallata dubu 95[27]
Sarkin daular Mughal, Aurangzeb ne ya kaddamar da Masallacin Badshahi, ko kuma "Masallacin sarauta" da ke Lahore, a shekarar 1673, wanda shi ne masallaci mafi girma na biyu a Pakistan da kudancin Asiya. Haka kuma shi ne masallaci na biyar mafi girma a duniya. Masallacin ya yi fice a kyau, wanda ya fito da irin kasaitar daular ta Mughal.[28]
10. Masallacin Sultan na Singapore Sultan Mosque, Singapore[29]
Asalin hoton,Getty Images
Bayanan hoto,An mayar da wannan Masallacin wani gini na tarihin Singapore a hukumance daga ranar 14 ga watan Maris din 1975[30]
Ana yi wa wannan masallacin da ke layin Muscat da ke gundumar Glam Rochor a Singapore, kallon mafi daraja tsakanin dukkan masallatan kasar. asallacin Sultan ya dade ba tare da an sauya masa komai ba tun da aka gina shi, sai wasu 'yan gyare-gyare da aka yi a harabarsa a shekarar 1960, da wasu kare-kare da aka yi a shekarar 1993.[31]
11. Massalacin Hagia Sophia da ke Turkiyya
A shekarar 2020 ne dai Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, ya mayar da gidan tarihi na Hagia Sophia masallaci.[32]
Tun asali wurin coci ne wanda aka mayar masallaci sai kuma daga baya aka mayar da shi wurin tarihi. A halin yanzu bayan shekaru 85 an mayar da ginin masallaci.[33]
12. Masallacin Qaboos da ke Oman
A 1992, Qaboos bin Said al Said wanda shi ne Sarkin Oman na lokacin, ya bayar da umarnin gina katafaren masallaci a ƙasar. An fara ginin masallacin ne a 1994 bayan an fitar da taswira da surar masallacin a 1993. An shafe shekaru shida da watanni bakwai ana ginin masallacin.[34]
Masallacin dai na ɗaukar masallata 20,000
13. Masallacin Jama, Indiya
Masallacin Jehan Numa wanda aka fi sani da masallacin Jama da ke Delhi, na daga cikin manyan masallatan da ke Indiya.[35]
Sarki na Daular Mughal wato Sha Jahan ne ya gina shi tsakanin shekarun 1650 zuwa 1656 kan kuɗi da suka kai rupee miliyan ɗaya. A lokacin buɗe masallaci, Imam Syed Abdul Ghafoor Shah Bukhari daga Bukhara shi ne ya buɗe masallacin.[36]
14. Masallacin Istiqlal, Jakarta
Masallacin Istiqlal da ke Jakarta a Indonesia shi ne masallaci ma fi girma a kudu maso gabashin nahiyar Asia. Masallacin wanda shi ne babba a ƙasar, an gina shi ne domin tunawa da samun 'yancin kai na ƙasar wanda aka yi masa laƙabi da Istiqlal, a Larabce hakan na nufin 'yancin kai.[37]
15. Masallacin Putra, Malasiya
Masallacin Putra shi ne Babban Masallacin birnin Putrajaya, kuma an fara ginin masallacin ne a 1997 inda aka kammala shi bayan shekaru biyu. Haka kuma yana makwaftaka ne da ofishin Firaiministan ƙasar da kuma tafkin Putrajaya. Masallacin na ɗaukar masallata kusan 15,000[38]



Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]Ana gina Masallatai ne a yanayin gine-gine irin na Musulunci a bisa akasari, amma kuma yawancin salon ginin masallatai ya danganta ne ga irin yadda salon ginin kasashe da al'adun mutane.
- Babban masallacin mai matsayi na daya a duniya wato Masallacin Harami
- Masallacin Temple Mount a tsohon birnin Jerusalem
- Masallaci Quba a Madina, Hejaz
- Masallacin al-Qiblatayn a Madina
- Babban masallaci Xi'an, misali na salon ginin masallaci a kasar Sin
- Masallacin Kampung Hulu masallaci mafi dadewa a Malesiya, misali na salon ginin masallaci irin na Malay da Sin da Hindu
- Masallacin Huseina Čauša džamija (wanda akafi sani da Džindijska), masallacin da aka gina a karni na 7 a garin Tuzla, Bosnia da Herzegovina
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑
Books, Cgp (2009). GCSE Religion Studies: Complete Revision and Practice (Revised ed.). Coordination Group
Publications. p. 96. ISBN 978-1-84762-406-2. line feed character in
|publisher=at position 19 (help); line feed character in|title=at position 5 (help) - ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/c882l4z01y3o.amp&ved=2ahUKEwjGkMbd4f6GAxUBRkEAHVYRA44QyM8BKAB6BAgIEAI&usg=AOvVaw329ve_xupZNQlaXZ-pm_-X
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2lp34dye1o.amp&ved=2ahUKEwjt6Ij64f6GAxV9a0EAHbgwBPIQyM8BKAB6BAgPEAI&usg=AOvVaw2OSsODdyWAW2Au0UsHaPJ3
- 1 2 https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2dlln375go.amp&ved=2ahUKEwjZ07CT4v6GAxUwVEEAHT8LBykQyM8BKAB6BAgKEAI&usg=AOvVaw1fQzgzBuc4-Wl43CC_t6ZA
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/c72264x7x87o.amp&ved=2ahUKEwitypOq4v6GAxUHWEEAHXpxCVMQyM8BKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw2C9yv8FEK-scRwUz3iXmK5
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ bnc
- ↑ bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ bbc
- ↑ karatu
- ↑ bbc
- ↑ nbc
- ↑ nazari
- ↑ bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ bbc
- ↑ Http
- ↑ Http
- ↑ bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Karatu
- ↑ bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ karatu
- ↑ Bbc
- ↑ bbc