Falsafa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Falsafa
academic discipline (en) Fassara, academic major (en) Fassara, branch of science (en) Fassara da field of work (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na knowledge system (en) Fassara
Bangare na ilimin sanin ɗan adamtaka
Suna a harshen gida φιλοσοφία
Yana haddasa tarihin falsafa
Hashtag (en) Fassara philosophy
Gudanarwan mai falsafa da professor of philosophy (en) Fassara
Is the study of (en) Fassara condition (en) Fassara, phenomenon (en) Fassara, reality (en) Fassara da sani
Uses (en) Fassara philosophical method (en) Fassara
Tarihin maudu'i history of philosophy (en) Fassara
WordLift URL (en) Fassara http://data.thenextweb.com/tnw/entity/philosophy
Stack Exchange site URL (en) Fassara https://philosophy.stackexchange.com/

Falsafa ko (turanci Philosophy) hanya ce ta tunanin duniya ko tunani game da duniya da halittar da take cikin duniya da ma kabilu da muhallai. Ta dogara ne bisa ga tambayoyi da zurfafa tunani game da yanayin mutane, yanayin duniya da kuma abinda ya haɗa su. Ma'ana dai falsafa na nufin yin tunani game da asali na halitta kama daga mutum, dabbobi, tsirrai dama duniyar baki ɗaya, tare da yin tambayoyi akan shin menene asalin su.

Wasu lokutan mutane kanyi batutuwa game da dalilan su da irin falsafar su (yadda suke kallon duniya a mahangar su) dama tunanin su har zuwa binciken su. Sai dai wannan makala din bata kawo bayani game da falsafar wani a karan kansa ba, tayi bayani ne agame da tunani na gamaiyar masana falsafa ne da ittafakin su bai ɗaya ma'ana mutanen da sukayi tunani, tambayoyi tare da rubututtuka game da falsafar duniya tun dauri.

Misalan tambayoyi na falsafa:

  • Menene kyakkyawa?
  • Menene Gaskiya?
  • Menene Dan'adam?
  • Shin akwai Ubangiji (Allah)?
  • Menene asalin Duniya?
  • Menene Shedan?
  • Menene dangantaka tsakanin Jiki da Tunani?
  • Menene Kimiyya?
  • A ina Soyayya take?

Asalin Falsafa[gyara sashe | gyara masomin]

Asalin kalmar falsafa tazo ne daga kalmomin harshen Girkanci guda biyu wato Philo ma'ana So sai kuma Sophia wako hikima, kenan idan an hada kalmar wato Philosopia na nufin Son Hikima, da harshen Hausa kuma sai ake faɗin Falsafa.

Da akwai mabambantan rabe-rabe daga mabambantan gurare da lokuta na falsafa. Wasu masanan Falsafar yan asalin Gargajiyar Girka ne, kamar su Plato da Aristotle. Wasu kuma daga Asiya suke kamar su Budda. Wasu masana falsafar kuma daga yankin Turai suke, kamar su William na Ockham ko kuma Saint Thomas Aquinas.

Masana falsafa na shekaraun 1600s, 1700s, da 1800s sun hada da Thomas Hobbes, René Descartes, John Locke, David Hume, da Immanuel Kant. Masana falsafa na shekarun 1900s sun hada da Ludwig Wittgenstein da kuma Jean-Paul Sartre.


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]