Soyayya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Kwado me shati so

Soyayya abu ce wadda take da matuƙar mahimmanci a cikin kowacce irin al'umma, dan haka mu Hausawa muna masu tsananin jin daɗin soyayya musamman wacce aka ginata akan doron gaskiya, soyayya ita ce take gyarawa mutum tarbiyyarsa, mu'amalarsa, da addininsa, kuma, ita asalinta tana fara faɗawa zuciyane ta hanyar gani. Soyayya halitta ce da Ubangiji subhanahu wa ta'alah ya halicceta sannan ya dasata a zuciyar duk wata hallitta mai rai.

Rabe-raben soyayya[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Soyayyar Allah da Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam, Ahlinsa da sahabbansa.
  2. Iyaye.
  3. ƴan Uwa.
  4. Malamai.
  5. Abokai ko ƙawaye.
  6. Soyayyar ma'aurata.

Duka waɗannan idan da baka sami soyayyarsu ba to ina tabbatarmaka da cewar, baka samu jin dadin rayuwar da Allah (S W T) ya halicceka acikinta ba. Da babu soyayya a zukatanmu, da baka sami tallafi da tarbiyya ba daga iyaye ba, da baka gane cewar kana da muhimmanci ba daga 'yan uwanka, da baka sami kyakkyawar mu'amala daga abokai ba, da baka sami tallafi, tausayi, da taimako daga mijinki ko matarka ba. Dan haka ga duk mutumin da ya tsinci kansa awannan fili na doron duniya kuma yake jin cewar yana yin rayuwa mai kyau to ko shakka babu yaci karo da soyayyar waɗannan abubuwan dana lissafa. Ana Gudanar Da Soyayya Ne Ta Hanyar Amfani wasu kalmomi waɗanda suke Shiga Cikin zuciya su idar da sakwanni na musamman.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]