Kaduna

Daga Wikipedia
A tsallaka zuwa: Shawagi, nema
 jihar kaduna
wannan sashin jihar kaduna kenan daga cikin taswirar Nijeriya.
 Tambarin kasar Hausa
Wannan tambarin kasar Hausa kenan. Kaduna tana daya daga cikin kasashen Hausa.

Kaduna tana daya daga cikin jihohin Arewacin Nijeriya a dai dai yankin kogin Kaduna, jiha ce ta kasuwanci, jihar ta kasance mai cunkoson jama'a akwai adadin jama'a kusan 760,084 a bisa ma'aunin kidayar shekarar (2006).

 • Kasa

Nijeriya

Flag of Nigeria.svg
 • Jiha

Kaduna

 • Gwamna

Ahmad Nasir El-Rufa'i

 • Fadin kasa

1,190 sq mi (3,080 km2)

 • Yawan al'ummah (2006)

6,006,562 [1]

 • Cunkoso

130/km2 (340/sq mi)

 • Manyan Kabilu

Hausa, Gbagyi, Gwandara da Fulani

 • Fasalin lokaci

CET (UTC+1)

 • Yanayin kaka

(DST) CEST (UTC+1)

 • Shafin Yanar gizo

www.kadunastate.gov.ng

Kalmar Kaduna ta samo asali ne daga sunan rafin kaduna, Tambarin jihar kaduna dai shine hoton Kada. Jihar Kaduna tana da kananan hukumomi guda 23 sune kamar haka:

Tarihi[gyarawa | edit source]

Hakika birnin kaduna ya kafu ne tun gabanin zamanin Shehu dan fodio wato tun talin-talin a shekarar (1913) birnin kaduna ya kasance cibiyar jamhuriyyar Arewa tun daga shekarar (1917) har zuwa (1967) sannan kaduna ta kasance cibiyar addinin musulunci a yankin arewa, birni ne na Hausawa ko dayake daga baya kaduna ta kasance tana daya daga cikin manyan biranen da sukafi tara kabilu daban-daban, a kalla akwai kabilu acikin kaduna kusan 57.

Alakar Addinai[gyarawa | edit source]

Addinai biyu sune manyan addinan jihar kaduna wato addinin Musulunci da addinin kiristanciî kasancewar addinai ne manya akwai alaka mai tsami a tsakaninsu musamman a shekarar 2000 da 2001 an samu rikicin addini a jihar kaduna a bisa dalilin sharia'ar Musulunci da musulmai sukai kokarin assasawa amma sai aka samu rashin jituwa da kiristoci wai suna tsammanin in har shari'ar musulunci to suma zai shafesu shi yasa suka ki amincewa a dalilin haka rikici ya balle inda aka samu asarar rayuka da dimbin dukiya mai tarin yawa, bayan haka akalla Mutane 1000 suka rasa rayukansu. Bayan haka an kara samun rikicin addini a shekarar 2002 amma a halin yanzu akwai zamantakewa mai kyau tsakanin addinan biyu.

Batun Ilmi[gyarawa | edit source]

A fagen ilimi kaduna ce cibiyar ilimi a arewacin Nijeriya kaduna ce cibiyar makarantar horas da jami'an tsaron ta kasa wato (NDA) an kafaTa tun a shekarar (1964). Sai kuma babbar makarantar POLY dake kaduna, wato kaduna polytechnic an kafata a (1968), sai kuma jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya ita kuma ta kafu a shekarar (1962).

 ABU Zaria
Wannan wani sashi ne daga cikin Jami'ar Ahmadu Bello Zaria.

Lallai kaduna duniya ce ta ilmi wannan dalilin ne yasa kaduna tayi fice a Nigeria ta ko'ina ana barkowa daga sassa daban-daban na Nijeriya ana zuwa neman ilimi a jihar kaduna.

Tattalin arziki da sufuri[gyarawa | edit source]

Kaduna cibiya ce ta masana'antun arewa, kamar masana'antun karafa, masaka, matatar man fetur, ginin tukwane da dai sauran abubuwa birjik. Babbar hanyar data ratsa ta cikin gari ana kiranta Ahmadu Bello way. Kaduna tanada babbar kasuwa wadda aka gina tun a shekarun 1990s bayan ta fuskanci mahaukaciyar gobara. Acikin garin kaduna akwai hanyoyin jiragen kasa wadda ake sufuri daga kaduna zuwa wasu sassan Nigeria, bayan haka akwai filayen jiragen sama guda biyu wato kaduna airport da kuma filin jirgin sama na chanchangi wato Chanchangi Airlines wadda ake sufuri daga jiha zuwa jiha ko daga Nigeria zuwa kasashen ketare.

Hanyoyin jiragen kasa[gyarawa | edit source]

Akwai hanyoyin layin dogo na jiragen kasa wadanda aka gina tun a watan satumba shekarar 2009 mai nisan tazarar kilomita 1,435 mm (4ft 81/2) zuwa babban birnin tarayya Abuja.

 layin dogo
Hanyar jirgin kasa daga Abuja zuwa kaduna

Wuraren bude ido[gyarawa | edit source]

[2]

 • Luggard Hall
 • Government Monument Bridge
 • General Hassan park
 • Man-made kaduna
 • Nok Terra Cotta
 • Nok Village
 • Cultural kaduna
 • National museum
 • Jakaranda pottery
 • kaduna souvenir

References[gyarawa | edit source]

 1. Summing the 2 LGAs kad North/South FRN (15 MAY 2007) L. Notice.
 2. learn about kaduna. Learn about kaduna state.