Jump to content

Bauchi (jiha)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bauchi


Suna saboda Bauchi
Wuri
Map
 10°30′N 10°00′E / 10.5°N 10°E / 10.5; 10
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Bauchi
Yawan mutane
Faɗi 6,834,314 (2016)
• Yawan mutane 149.1 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 45,837 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Arewa maso Gabas
Ƙirƙira 3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Bauchi State (en) Fassara
Gangar majalisa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 740001
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho +234
Lamba ta ISO 3166-2 NG-BA
Wasu abun

Yanar gizo bauchistate.gov.ng
Twitter: BauchiState Edit the value on Wikidata

Jihar Bauchi jiha ce da ke Arewa maso gabashin kasar Najeriya.Ta hada iyaka daga arewa da Kano da Jigawa,Jihar Taraba da Plateau daga kudu, Gombe da Yobe daga Gabas, sai kuma Kaduna daga Yamma. Jihar ta samo asalin sunanta ne daga tarihin masarautar Bauchi, wacce itace babban birnin jihar a yau. An kafa Jihar Bauchi a shekarar alif dari tara da saba'in da shida (1976), a yayin da aka rarraba tsohuwar Jihar Arewa maso Gabacin Najeriya. A baya Jihar Bauchi ta mamaye yankin Jihar Gombe, wacce daga bisani ta zamo jiha mai zaman kanta a shekara ta alif 1996.[1]

Bauchi itace jiha ta biyar a faɗin ƙasa[2], kuma ta bakwai a yawan jama'a[3]. Ta na da yawan fili kimanin kilomita dubu ar,ba’in da biyar da ɗari takwas da casa'in da uku (45, 893) da yawan mutane kimanin miliyan bakwai da dubu dari biyar da arba'in da ɗari shida da sittin da uku (7,540,663)[4] a bisa kidayar shekara ta dubu biyu da shida 2006. Jihar ta rabu dangane da yanayin kasa zuwa kashi biyu (2), West Sudanian savanna daga kudu da kuma semi-desert sahel Savanna daga arewa, da kuma montane Jos Plateau daga kudu maso yammacin Jihar.[5] Daga cikin kayatattun wurare a garin sun hada da, Yankari National Park, wani katafaren wajen ajiye dabbobi ne dake kudancin jihar Bauchi inda akwai dabbobi kaman bijimai, birrai, barewa, zakuna, giwaye da dai sauransu.[6]

Bauchi ne babban birnin jihar Bauchi. Bala Abdulkadir Mohammed shi ne Gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2019 har zuwa yau. Wasu daga cikin dattijan Jihar sun hada da: Abubakar Tafawa Balewa, Isa Yuguda, Isah Hamma Misau, Nazif Gamawa, Haruna Ningi da Ali Wakili.

Akwai yaruka da dama a yankuna daban daban na Jihar wadanda suka hada da: Yaren Bolewa, Butawa, da Yaren Warji daga yankunan tsakiyar jihar; Yaren Fulfulde, Yaren Kanuri, da Yaren Karai-Karai daga arewacin garin; Fulani da Yaren Gerawa acikin birnin Bauchi da kewayen ta; Yaren Zaar (Sayawa) daga kudu; Yaren Tangale daga kudu maso gabas; da kuma Jarawa daga kudu maso yamma. Mafi akasarin mutanen gari (kaso tamanin da biyar 85%) musulmai ne, da karamin kaso kiristoci da kaso shida 6% da maguzawa da kaso tara 9%.[7]

A farkon shekarun alif dubu da dari takwas 1800s, Fulani Jihadi sun kwace mafi akasarin garin birnin Bauchi na yau, sannan suka kafa Masarautar Bauchi a karkashin Daular Masarautar Musulunci na Sokoto. A karni na dubu daya da shatara 1900 ne Turawan mulkin mallaka suka mamaye Masarautar kuma suka hade ta a cikin Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya wacce daga bisani ta zamo Najeriya karkashin mulkin Turawa, kafin samun 'yanci a shekarar alif dari Tara da sittin 1960. Tun asali, yankin Jihar Bauchi a yau tana cikin Yankin Arewa bayan samun 'yanci har zuwa shekarar alif ta 1967 lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta fada karkashin Jihar Arewa ta Gabas.[8] Bayan rarraba Jihar Arewa ta Gabas, an kafa Jihar Bauchi a ranar uku 3 ga watan Fabrairu shekara ta dubu daya da dari tara da saba'in da shida 1976 tare da sauran jihohi goma. Shekaru ashirin (20) kuma bayan kafata, an hade wasu kananan hukumomi daga yammacin Jihar inda suka samar da Jihar Gombe.

bauchi emir
bauchi airport

A matsayinta na jihar da ta dogara da noma, tattalin arzkin Jihar sun ta'allaka ne akan dabbobi da hatsi, kamansu auduga, gyaɗa, dawa, tumatiri da kuma doya tare da cigaba a fannin noman rani na kara habaka samar da abinci tun zamanta jiha. Sannan akwai masana'antu na sarrafa abinci da masana'antun sarrafa kayan abinci na gwan-gwani, da kuma hako ma'adanai kamar tin da columbite, da kuma wuraren bude idanu kamar Dajin shakatawa na Yankari da koramunta na Wikki Springs.[9]

Asalin Suna

[gyara sashe | gyara masomin]

Dangane da tarihi na gargajiya, garin ya samo asali ne daga wani mafarauci mai suna Baushe, wanda ya zauna a yankin kafin zuwan jagoran masarutar na farko wato Yakubu (wacce aka samar a tsakanin alif ta 1800–10).[10] Jihohin Bauchi da Adamawa sun kasance kasashen 'yanci da kasuwanci ga mutanen Daular Fulani na Sokoto.[11]

Bauchi a Shekarar 1970

Wurin da ake kira Bauchi ta kasance kafin shakarar alif ta 1976 gunduma a yankin Jihar Arewa ta Gabas. Danagne da kidayar shekara ta 2006, Jihar tana da mutane kimanin 4,653,066.

Jihar Bauchi ta sama cigaba iri-iri a cikin 'yan shekarun nan. Akwai harshen Ajawa da akayi amfani dashi a jihar Bauchi, amma daga bisani ya bace a tsakanin shekarun 1920 da shekara ta 1940 inda asalin masu amfani da harshe suka sauya zuwa Hausa.[12]

A lokacin mulkin Turawa har zuwa samun 'yanci, tana cikin yankin Plateau da Yankin Arewacin Najeriya, har zuwa 1967 lokacin da aka samar da jihohi, yayin da yankunan Bauchi, Borno, da Adamawa suka hade wajen samar da Jihar Arewa ta Gabas.

Bayan samar da Jihar Bauchi a shekara ta alif 1976, a lokacin Jihohi biyu Bauchi da Gombe na hade, jihar nada kananan hukumomi 16. Daga bisani an kara yawan kananan hukumomin zuwa 20 sannan daga bisani 23. Haka zalika, a shekara ta 1997, an samar da Jihar Gombe, daga Jihar Bauchi inda aka samu karin kananan hukumomi a kasar, inda aka bar Jihar Bauchi da kananan hukumomi 20 kamar yadda aka zayyano a kasa:

Kananan Hukumomi

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Bauchi nada adadin Kananan hukumomi ashirin (20). Sune:

Karamar Hukuma Fadin kasa (km2) Adadin 2006
Mutane
Cibiyar Karamar Hukuma Lambar aika
sako
Bauchi 3,687 493,810 Bauchi 740
Tafawa Balewa 2,515 219,988 Bununu 740
Dass 535 89,943 Dass 740
Toro 6,932 350,404 Toro 740
Bogoro 894 84,215 Bogoro 741
Ningi 4,625 387,192 Ningi 742
Warji 625 114,720 Warji 742
Ganjuwa 5,059 280,468 Kafin Madaki 742
Kirfi 2,371 147,618 Kirfi 743
Alkaleri 5,918 329,424 Alkaleri 743
Southern region totals 33,161 2,497,782
Darazo 3,015 251,597 Darazo 750
Misau 1,226 263,487 Misau 750
Giade 668 156,969 Giade 750
Shira 1,321 234,014 Yana 750
Jama'are 493 117,883 Jama'are 751
Katagum 1,436 295,970 Azare 751
Itas/Gadau 1,398 229,996 Itas 751
Zaki 1,476 191,457 Katagum 752
Gamawa 2,925 286,388 Gamawa 752
Damban 1,077 150,922 Damban 752
Northern region totals 15,035 2,178,683
Bauchi Emirate Council

Kirfi Ta kasance Garine cikin Birnin Bauchi wanda keda aƙalla faɗin aƙalla 700 mita kewaye da gefenta ne rafin Gongola wanda ke isar da ruwa zuwa cikin garin. Wanda ya hade da babban kogin Benue. Gari ne mai tarin albarkoki, a bangaren Noma da Kiwo.[13] A al’adance ta kasance tana maraba ne kaɗai da mutanen da ake kira Kirfawa kuma ta fada karkashin gundumar Hausawa. Bincike akan garin Kirfi ya nuna cewa amsoshin da suka ƙunshi al’ada, da Addini da harkan Siyasa a kasar Hausa ana iya samun sa a garin Kirfi ta garin Bauchi.[13]

Labarin kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Bauchi ta mamaye fadin kasa kimanin 49,119 km2 (18,965 sq mi) inda ta mamaye kaso 5.3% na daukakin fadin Najeriya kuma tana zaune akan lambobin wuri na latitudes 9° 3' da 12° 3' arewa da kuma longitudes 8° 50' da 11° gabas.

Jihar tana da iyaka da jihohi bakwai, Kano da Jigawa daga arewa, Taraba da Plateau daga Kudu, Gombe da Yobe daga Gabas sai kuma Kaduna daga Yamma.

Jihar Bauchi na daga cikin jihohin arewan Najeriya dake da yanayin tsirrai iri biyu, Sudan savannah da kuma Sahel savannah. Haka zalika akwai tsaunuka a kudancin yankin garin, dangane da alakarta da tsaunukan Jos Plateau.

Adadin jama'a

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai Kabilu daban daban har guda 55 a garin wanda suka hada da: Gerawa, Sayawa, Jarawa, Kirfawa, Hausawa Bolewa, Karekare, Kanuri, Fa'awa, Butawa, Warjawa, Zulawa, Boyawa, Badawa. Amma Fulani ne asalin kabilar garin. Hakan na nufin cewa suna da nasu asalin, al'adu, addinai da makamantansu.

Akwai kamaiceceniya tsakanin harsunan garin, dangane da ayyuka, al'adu, sutura, da kuma cudanya a tsakaninsu musamman ta hanyar auratanya da kasuwanci. Wasu daga cikin harsunan na da ba'a a tsakaninsu. da Sayawa da dai sauransu.

Bikin hawan sallah na daya daga cikin muhimman bukukuwa da ke jawo 'yan kallo a duk shekara.[14]

Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa[15] na nan acikin babban birnin Bauchi.[16] Wasu daga cikin wuraren koyarwa sun hada da; Jami'ar Jihar Bauchi,[17] Abubakar Tatari Ali Polytechnic[18] , Federal Polytechnic, Bauchi.[19], Aminu saleh college of Education Azare[20]Federal university of health science Azare[21]

Ire-iren harsunan West Chadic language da ake amfani dasu a Bauchi sun hada da:[22]

Yarukan Bauchi a jere da kananan hukumominsu.[23]

LGA Languages
Alkaleri Dass; Bole; Duguri; Giiwo; Guruntum-Mbaaru; Labir; Tangale
Bauchi Bankal; Duguri; Dulbu; Galambu; Gera; Geruma; Giiwo; Guruntum-Mbaaru; Ju; Kir-Balar; Labir; Luri; Mangas; Mbat; Pa'a; Polci; Shiki; Tala; Zangwal
Bogoro Saya
Darazo Bole; Deno; Diri; Giiwo; Mburku; Ngamo; Zumbun
Dass Bankal; Dass; Gwak; Polci; Saya; Shall-Zwall; Zari
Dukku Bole
Gamawa Karekare
Ganjuwa Ciwogai; Gera; Geruma; Jimi; Kariya; Kubi; Miya
Kirfi Bure
Misau Fulato/Borno; Shuwa; Kanuri; Hausa; Fulani
Ningi Diri; Gamo-Ningi; Kudu-Camo; Pa'a; Siri; Warji; Geruma
Tafawa Balewa Sur; Vaghat-Ya-Bijim-Legeri; Zari; Bankal; Gwak; Izere; Saya
Toro Bankal; Dass; Geji; Geruma; Gwa; Gyem; Iguta; Izere; Jere; Lame; Lemoro; Mawa; Panawa; Polci; Sanga; Saya; Shau; Tunzuii; Zari; Zeem; Ziriya
Zaki Bade

Sauran harsunan Bauchi sun hada da: Ajawa, Beele, Berom, Kanuri, Kwaami, Manga, Pero, da kuma Piya-Kwonci.

Gwamnan garin shine babban mai zartarwa, tare da fannin shari'a na garin na nan a birnin Bauchi.[24]

Gwamna Bauchi shine Mr. Bala AbdulKadir Mohammed, wanda ya lashe zabe a ranar 9 ga watan March,shekara ta 2019 a karkashin jam'iyyar PDP. An rantsar dashi a ranar May 29, ga watan shekara ta 2019, wanda hakan tasa ya zamo gwamna na shida a Bauchi a karkashin mulkin dimukradiyya sannan kuma gwamna na 16 gaba daya. Baba Tela ne mataimakin gwamnan Bauchi.[25][26]

Kiwon Lafiya

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Bauchi na da tarin asibitoci daman hukumomin kiwon lafiya, wannnan sun hada da:

  • Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital[27][28]
  • Bauchi State Hospital[29]
  • Al-amin Hospital
  • Niima Consultants Hospital
  • Albishir Clinic and Maternity
  • Proactive Clinic and Hospital Ltd.
  • Reemee Medicare Nigeria Limited.

Sanannun Mutane

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Haour, Anne., Rossi, Benedetta (2010) Being and becoming Hausa : interdisciplinary perspectives.Leiden: Brill. ISBN 978-90-04-1854-25
  1. https://www.nigeriagalleria.com/Nigeria/States_Nigeria/Bauchi/
  2. Top 10 Largest States in Nigeria by Landmass • Okay.ng
  3. Bauchi State - Wikipedia
  4. List of Nigerian states by population - Wikipedia
  5. "Bauchi | state, Nigeria | Britannica". www.britannica.com. Retrieved 27 February 2022.
  6. "Yankari Game Reserve". WCS Nigeria. Retrieved 14 Disemba 2021.
  7. "Azare Town | Bauchi State". www.fmcazare.gov.ng. Retrieved 27 February 2022.
  8. "Bauchi State". Nigerian Investment Promotion Commission. 7 January 2019. Retrieved 27 February 2022.
  9. "Bauchi - state, Nigeria". britannica.com. Archived from the original on 18 October 2014. Retrieved 14 December 2021.
  10. "Bauchi - state, Nigeria". britannica.com. Archived from the original on 18 October 2014. Retrieved 30 April 2018.
  11. Johnston, Hugh A.S. (1967). The Fulani Empire of Sokoto. Oxford University Press. p. 161. ISBN 0-19-215428-1.
  12. Ajawa language at Ethnologue
  13. 13.0 13.1 Haour, Anne., Rossi, Benedetta.p.165
  14. "A 100-Year-Old Muslim Festival of Horse Riding". Folio Nigeria. Retrieved 17 August 2020.
  15. keetu (8 March 2018). "List Of Accredited Courses Offered In ATBU Bauchi". Retrieved 6 August2021.
  16. keetu (8 March 2018). "List Of Accredited Courses Offered In ATBU Bauchi". Retrieved 6 August2021.
  17. "List Of BASUG Courses and Programmes Offered - MySchoolGist". www.myschoolgist.com. 9 October 2020. Retrieved 6 August 2021.
  18. "Bauchi poly secures accreditation for 53 courses". The Nation. 16 January 2018. Retrieved 27 March 2019.
  19. keetu (23 November 2017). "List Of Accredited Courses Offered In Federal Poly Bauchi". Retrieved 6 August 2021.
  20. https://freedomonline.com.ng/coe-azare-introduces-4-pgd-courses-3-degree-programs-official/?amp=1
  21. https://independent.ng/federal-university-of-health-sciences-azare-matriculate-760-pioneer-students/
  22. Blench, Roger (2019). An Atlas of Nigerian Languages (4th ed.). Cambridge: Kay Williamson Educational Foundation.
  23. "Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 10 January 2020.
  24. "Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 10 January 2020.
  25. "Huge Crowd Gather for Bala Mohammed's Inauguration in Bauchi". THISDAYLIVE. 29 May 2019. Retrieved 1 April 2022.
  26. "Nigerian States". www.worldstatesmen.org. Retrieved 2 April 2022.
  27. https://dailytrust.com/atbu-teaching-hospital-doctors-others-unite-for-patients-wellbeing/
  28. https://dailypost.ng/2022/11/28/over-300-in-bauchi-to-benefit-from-free-medical-programme/
  29. https://tribuneonlineng.com/bauchi-hospital-management-board-restates-commitment-to-effective-healthcare-services/


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara