Alkaleri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Template:Infobox settlement Alkaleri karamar hukuma ce a jihar Bauchi, Najeriya . Babban hedkwatarsa yana cikin garin Alkaleri (ko Alkalere) akan babbar hanyar A345 a arewacin yankin.10°15′58″N 10°20′07″E / 10.26611°N 10.33528°E / 10.26611; 10.33528 . Layin arewa maso gabas daidai latitude da longitude ya ratsa ta karamar hukumar.

Yana da yanki 5,918 km2 da yawan jama'a 329,424 a ƙidayar 2006.

Kabilar da suka fi yawa a yankin su ne fulani, Kanuri, Dugurawa, Guruntawa da Labur "Jaku".

Lambar akwatin gidan waya ita ce 743.

Gundumomin karamar hukumar sune Pali, Duguri, da Gwana. Manyan garuruwa da kauyukan karamar hukumar kamar Fanti, Gar, Gokaru, Guma, Gwaram da dai sauransu ciki har da hedikwatar karamar hukumar, Alkaleri suna cikin gundumar Pali. Gundumar Duguri gida ce ga Yankari -West Africa's premiere game Reserve, kuma ta ƙunshi garuruwa da ƙauyuka kamar Badara, Dagudi, Dan, Gajin Duguri, Mainamaji, Yashi, Yelwan Duguri, da Duguri mai tarihi. Gwana yana yankin kudu maso gabas na karamar hukumar.

Nassoshi[gyara sashe | Gyara masomin]

Template:Bauchi State