Bauchi (birni)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgBauchi
Babban Gwani.jpg

Wuri
 10°18′57″N 9°50′39″E / 10.3158°N 9.8442°E / 10.3158; 9.8442
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jerin jihohi a NijeriyaJihar Bauchi
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 693,700 (2016)
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 616 m
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa supervisory councillors of Bauchi local government (en) Fassara
Gangar majalisa Bauchi legislative council (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Bauchi Birni ne, da ke a Jihar Bauchi, a ƙasar Najeriya. Shi ne babban birnin jihar Bauchi. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2006, akwai jimilar mutane dubu dari huɗu da casa'in da uku, amma bisa ga kimanta a shekarar 2017, jimilar mutane dubu dari bakwai (700,000). Birnin Bauchi kilomita dari daya da talatin ne daga Jos, da kilomita dari huɗu ne daga Abuja, babban birnin Najeriya. Akwai Filin Jirgin Sama a Bauchi.[1]

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ance wai "Yaqub ibn Dadi" ya samar da birnin Bauchi, daya daga cikin sarakunan Daular Sokoto wanda ba fulani bane. Sunan garin ya samo asaline da da wani mafarauci "Baushe" wanda ya shawarci Yakoub da ya kirkiri nashi sabon birnin daga yammacin tsibirin Warinje. Don saka masa ne Yakoub yayi alkawarin sanya wa garin sunansa.

A wannan birnin aka burne tsohon Firaim minista Abubakar Tafawa Balewa, sannan wajen ajiyar namun daji Yankari National Park na kimanin kilomita 110km daga bairnin. Bauchi na bisa hanyar titin jirgin kasa daga Port Harcourt zuwa Maiduguri. An samar da Labrare na Bauchi State Library a 1976.[2]

Acikin watan Julin shekarar ta 2009, a sakamakon hare-haren boko haram ya jawo kashashe-kashen akalla mutum 50 da kuma kame wadanda ake zargi akalla mutum 100.[3]

Bayan faruwar al'amarin kwashe dalibai mata na Chibok da ya faru a cikin shekara ta 2014 ya janyo an maida dalibai mata da dama zuwa makarantan kwana na "Federal Government Girls College" dake Bauchi. Mafi akasarinsu daga makarantar Federal Government Girls’ College, Potiskum, jihar Yobe.[4]

Sufuri[gyara sashe | Gyara masomin]

Akwai titin jirgin kasa a Bauchi wanda ke da fadin 762mm (2 ft 6 in) amma daga bisani an ingantashi zuwa isasshen fadi na 1,067 mm (3 ft 6 in).

Bauchi na da filin jirgin sama watau "Bauchi Airport" tun fil-azal har izuwa shekara ta 2014. Daga bisani an maida harkokin sufurin jirgin saman zuwa Sir Abubakar Tafawa Balewa International Airport wanda ke da nisan kilomitoci 23 km(14 mi) daga arewacin birnin, kusa da kauyen Durum.

Yanayi[gyara sashe | Gyara masomin]

Dangane da rabe-raben yanayi na Köppen Climate Classification, Bauchi na da yanayi na tropical savanna climate a gajarce "Aw" akan taswirorin yanayi.[5]

Climate data for Bauchi
Watan Janairu Fabrairu Maris Afrilu Mayu Yuni Yuli Ogusta Satumba Oktoba Nuwamba Disamba Shekara
Record high °C (°F) 38.3
(100.9)
39.4
(102.9)
39.4
(102.9)
40.6
(105.1)
39.4
(102.9)
37.8
(100.0)
33.3
(91.9)
32.2
(90.0)
33.9
(93.0)
35.6
(96.1)
36.1
(97.0)
36.7
(98.1)
40.6
(105.1)
Average high °C (°F) 31.6
(88.9)
33.9
(93.0)
36.4
(97.5)
36.6
(97.9)
34.6
(94.3)
31.6
(88.9)
29.2
(84.6)
28.6
(83.5)
29.7
(85.5)
32.2
(90.0)
33.0
(91.4)
31.4
(88.5)
32.4
(90.3)
Daily mean °C (°F) 22.4
(72.3)
24.6
(76.3)
28.1
(82.6)
30.0
(86.0)
28.4
(83.1)
26.3
(79.3)
24.6
(76.3)
24.3
(75.7)
24.7
(76.5)
25.5
(77.9)
24.1
(75.4)
22.1
(71.8)
25.4
(77.7)
Average low °C (°F) 13.1
(55.6)
15.3
(59.5)
19.8
(67.6)
22.3
(72.1)
22.2
(72.0)
20.9
(69.6)
20.1
(68.2)
19.9
(67.8)
19.7
(67.5)
18.8
(65.8)
15.2
(59.4)
12.8
(55.0)
18.3
(64.9)
Record low °C (°F) 7.2
(45.0)
8.9
(48.0)
11.7
(53.1)
16.1
(61.0)
16.7
(62.1)
16.7
(62.1)
17.2
(63.0)
17.2
(63.0)
16.1
(61.0)
12.2
(54.0)
9.4
(48.9)
6.1
(43.0)
6.1
(43.0)
Average precipitation mm (inches) 0.5
(0.02)
0.5
(0.02)
5.0
(0.20)
36.0
(1.42)
94.0
(3.70)
147.0
(5.79)
254.0
(10.00)
340.0
(13.39)
183.0
(7.20)
36.0
(1.42)
1.0
(0.04)
0.0
(0.0)
1,095
(43.11)
Average precipitation days (≥ 0.3 mm) 0 0 1 3 9 12 17 21 15 4 0 0 82
Average relative humidity (%) (at 7:00 LST) 42 35 40 63 79 86 92 94 93 88 65 51 69
Mean monthly sunshine hours 275.9 268.4 272.8 225.0 251.1 228.0 186.0 155.0 216.0 282.1 300.0 306.9 2,967.2
Mean daily sunshine hours 8.9 9.5 8.8 7.5 8.1 7.6 6.0 5.0 7.2 9.1 10.0 9.9 8.1
Source: Deutscher Wetterdienst[6]

Yaruka[gyara sashe | Gyara masomin]

Sarkin Bauchi bisa farin doki da alkyabba mai fari da ja.
Baikin sallah a Bauchi
Hawan Bikin sallah na 1970–1973

Sanannun mutane[gyara sashe | Gyara masomin]

John Egbunu (haihuwar 1994), sanannen dan wasan kwallon kwando na America haihuwar Najeriya dan asalin birnin Bauchi ne.

Kara Dubawa[gyara sashe | Gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. "Bauchi history".
  2. World Guide to Libraries (25th ed.), De Gruyter Saur, 2011, ISBN 9783110230710
  3. "Reporter: More than 200 dead in Nigeria violence". Kyiv Post / AP. 2010-03-07. Retrieved 2014-05-11.
  4. "Yobe Killings: Bauchi Receives 200 Students, Articles". This Day Live. 2014-03-20. Archived from the original on 2014-05-12. Retrieved 2014-05-11.
  5. "Bauchi, Nigeria Köppen Climate Classification". Weatherbase. Retrieved 2013-12-10.
  6. "Klimatafel von Bauchi / Nigeria" (PDF). Baseline climate means (1961-1990) from stations all over the world (in Jamusanci). Deutscher Wetterdienst. Retrieved 25 February 2016.