Jump to content

Boko Haram

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Boko Haram

Bayanai
Iri irregular military (en) Fassara da ƙungiyar ta'addanci
Ƙasa Najeriya, Kameru, Cadi, Mali da Nijar
Ideology (en) Fassara Islamic terrorism (en) Fassara
Mulki
Shugaba Abubakar Shekau da Muhammad Yusuf
Mamallaki Daular Musulunci ta Iraƙi
Tarihi
Ƙirƙira 2002
Wanda ya samar

Boko Haram. Hakikanin sunan wannan kungiya shi ne Jama'atu Ahlus sunnah Lidda'awath wal-jihad Mabiya Sunnah ta Annabi Muhammad dan Da'awa da Jihadi ( Arabic : جماعة اهل السنة للدعوة والجهاد Jamā'atu Ahlus Sunnah Lidda'awatih wal-Jihad ), amman anfi saninsu da sunansu na Hausa watan "Yan Boko Haram". Kungiya ce ta 'yan jihadi dake da cibiyarta a Arewa maso gabashin Najeriya. Suna adawa ne da dokokin da ba na Allah ba da kuma kimiyyar Zamani. A shekara ta 2002 wani mutum da ake kira da Muhammad Yusuf ya kirkiri kungiyar kuma suke son tabbatar da Shari'ar Musulunci a Najeriya. Hakazalika, kungiyar Boko Haram ta yi daurin suna kan kaiwa kiristoci da ma’aikatar gwamnati hare-hare da dasa bama-bamai a coci-coci da Masallatai.

gawar wani mayakin boko haram

.

Sojojin Najeriya a dajin Sambisa maboyar mayakan Boko Haram yayin fafatawa

Tun daga shekarar 2009 hukumomi a Najeriya suke yaki da kungiyar ta Boko Haram wadda tayi sanadin mutuwar dubbannin mutane tare da lalata dukiya ta miliyoyin nairori.

Rundunar sojin Najeriya dai ta sha cewa tana yin iya bakin kokarinta don shawo kan matsalolin tsaro a jihohin arewa maso gabas da ke cikin arewacin kasar wanda rikicin Boko Haram ya daidaita, amma har yanzu Boko Haram,na da tasiri.

Rikicin wanda aka faro a jihar Borno dake arewa maso gabas ya fantsama zuwa makwabtan ƙasashe kamar su Nijar da Chadi da kuma Kamaru. Gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da rundunar sojin ƙasar sun sha yin iƙirarin karya lagon Boko Haram,sai dai har yanzu mayakan ƙungiyar na ci gaba da zamewa ƙasashen yankin Tafkin Chadi barazana.

Matan Chibok

[gyara sashe | gyara masomin]
Michelle Obama Ta daga takardar nuna tausayi ga yan matan chibok
motocin yaqin yan kungiyar boko haram wanda sojojin camaru suka lalata

.

zanga zanga lumana kenan da dandazon mutane keyi domin ganin an ƙwato ko dawo da chibok girls wanda boko haram suka sace

.

A watan afrilun shekarar dubu biyu da goma sha huɗu, 2014, Boko Haram ta sace 'yan mata 276 'yan makaranta daga Chibok. wanda Sheƙau ya sanar cewa zai saida su a matsayin bayi, Matan tsohuwar shugaban ƙasar Amurka ta tausaya musu a kan alamarin[1][2][3][4][5][6][7][8] tayi rubutu kamar haka ajikin takardar "#BringBackGoodluck2015" ma'ana adawo mana da yaran mu [9] [10] [11].

  1. "Rewards for Justice–First Reward Offers for Terrorists in West Africa". U.S. Department of State. 3 June 2013.
  2. "Nigeria says 219 girls in Boko Haram kidnapping still missing". Fox News. 23 June 2014. Retrieved 1 August 2014.
  3. Maria Tadeo (10 May 2014). "Nigeria kidnapped schoolgirls: Michelle Obama condemns abduction in Mother's Day presidential address". The Independent. Retrieved 1 August 2014.
  4. Tim Cocks (8 July 2014). "Jonathan's PR offensive backfires in Nigeria and abroad". Yahoo! News/Reuters. Retrieved 1 August 2014.
  5. Megan R.Wilson (26 June 2014). "Nigeria hires PR for Boko Haram fallout". The Hill. Retrieved 1 August 2014.
  6. "Nigeria: Government knew of planned Boko Haram kidnapping but failed to act". Amnesty International UK. 9 May 2014. Retrieved 1 August 2014.
  7. Taiwo Ogunmola Omilani (24 July 2014). "Chibok Abduction: NANS Describes Jonathan As Incompetent". Leadership,Nigeria. Archived from the original on 19 August 2014. Retrieved 1 August 2014.
  8. "One month after Chibok girls' abduction". The Nation, Nigeria. 15 May 2014. Retrieved 1 August 2014.
  9. Daniel Magnowski (10 September 2014). "Nigeria's President Jonathan Bans 'Bring Back Goodluck' Campaign". Bloomberg. Retrieved 20 November 2014.
  10. Felix Onuah (11 November 2014). "Nigeria's Jonathan seeks second term, vows to beat Boko Haram". Reuters. Archived from the original on 11 November 2014. Retrieved 11 November 2014.
  11. Liz Ford (16 February 2016). "Women freed from Boko Haram rejected for bringing 'bad blood' back home". The Guardian. Retrieved 15 July 2016.