Abubakar Shekau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Simpleicons Interface user-outline.svg Abubakar Shekau
Leader of Boko Haram (en) Fassara

30 ga Yuli, 2009 - 20 Mayu 2021
Muhammad Yusuf
Rayuwa
Haihuwa Shekau (en) Fassara, 24 ga Maris, 1973
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Dajin Sambisa, 20 Mayu 2021
Yanayin mutuwa Kisan kai (suicide bombing (en) Fassara)
Karatu
Harsuna Hausa
Larabci
Kanuri
Fillanci
Turanci
Sana'a
Sana'a soja
Aikin soja
Ya faɗaci Rikicin Boko Haram
Tawayen Boko Haram, 2009
Ta'addancin Boko Haram a kamerun
Imani
Addini Musulunci
Rahoto akan barazanar shekau Shugaban Kungiyar boko haram

Abubakar Shekau, an kuma sanshi da Darul Akeem wa Zamunda Tauhid, ko Darul Tauh woto (gidan tauhidi) (larabci دار التوحيد ), an haifeshi tsakanin 1967 ko 1975 (babu tabbaci) ɗan ƙabilar Kanuri ne kuma wanda akafi sani da shugaban ƙungiyar Boko Haram, mai ƙoƙarin kafa daular Musulunci a yankin Arewacin ƙasar. Ƙungiya ce ta masu tayar da ƙayar baya a Najeriya kamar yadda ƙasar ta ayyana ta sakamakon fitar da wani faifan bidiyo da Shugaban ta Sheƙau yayi ya nuna ikirarin ƙungiyar nayin mubaya'a ga Ƙungiyar dake ƙoƙarin kafa daular musulinci a yankin gabas ta tsakiya wato (ISIS). Shekau ya riƙe matsayin mataimakin shugaban ƙungiyar a karkashin wanda ya kafa ta Muhammad Yusuf har zuwa lokacin da Yusuf ya rada rayuwar sa a hannun jami'an tsaron ƙasar Najeriya a shekara ta dubu biyu da tara, 2009 inda daga bisani ya zama shugaban ƙungiyar har zuwa yanzu. Abubakar Sheƙau Musulmi ne kuma mabiyin aƙidar Sunni Islam ko Salafiyya.[1][2][3][4]

Bayanin Shekau[gyara sashe | gyara masomin]

Asalin yaren haihuwa na Sheƙau shine Kanuri, amma kuma yana jin harsunan Hausa, Larabci, Filatanci da Turanci sosai. Yayi ikirarin cewa shi Musulmi ne kuma wanda yayi ilimin addinin na Musulunci na ainihi kuma mai bin aƙidar musulunci sauda ƙafa.

A faya fayan bidiyon da Sheƙau yake fitarwa a kafafen Yanar gizo yasha ƙalubalantar sojojin dake yaƙi da ƙungiyar sa cewa yafi ƙarfin su kuma yananan kan aƙidar sa ta kafa daular Musulunci sannan bazasu iya dakatar dashi ba ko su kasheshi har sai in Allah ne ya kawo ƙarshen rayuwar sa.

A wantan Yuni na 2012 hukumar ƙasar Amurka ta ayyana Sheƙau a matsayin ɗan ta'adda. Tun daga shekarar 2013 ne ƙasar ta Amurka tayi ikirarin bayar da ladan $7miliyan na dalar Amurka ga duk wanda ya taimaka wajen kama sheƙau. A wani ƙarin kuma ƙasar Najeriya ma tayi ikirarin bayar da Naira miliyan 50 ga wanda ya taimaka wajen kama sheƙau ɗin.

Sheƙau ya tsallake ma wani harbi da sojojin Najeriya suka yi masa a ƙafa a samamen da suka kai masa a shekarar 2009. Bayan ya tsallake rijiya da baya ne yaci gaba da kai hare-hare. A ɗaya daga cikin sanannun hare-haren sa akwai wanda yayi garkuwa da yanmatan makarantar sakandare sama da 200 a 2014. Shekau yayi sanarwar cewar ya musuluntar da yanmatan dukkan su daga bisani kuma yayi barazanar ƴanmatan zasu rinka kai hare-hare kan Kiristoci.

A watan Augusta na sekarar 2016 ƙungiyar ISIS ta ayyana Abu Musab Al Barnawi a matsayin shugaban ƙungiyar ta boko haram kuma ya maye gurbin Shekau wanda yaƙi amincewa da hakan. Saidai daga baya Hukumomin tsaro na ƙasar ta Najeriya sun kama Albarnawi ranar 26 ga watan Disamba na 2016.

Rayuwar sa ta kashin kai[gyara sashe | gyara masomin]

Sheƙau ɗan Najeriya ne kuma yayi ikirarin shi haifaffen ƙauyen Sheƙau ne na jahar Yobe. Amma babu tabbaci game da adadin shekarun sa. Ya auri ɗaya daga cikin matan Muhammad Yusuf.

Ana masa laƙabi da Darul Tauhid wato Matattarar Kaɗaita Allah.

Raho tannin rasuwar sa daga bangaren gwamnati[gyara sashe | gyara masomin]

Sau tari ɓangaren gwamnatin taraiya tasha ikirarin cewar ta kashe Sheƙau, amma daga bisani sai ya fito a faifan bidiyo ya ƙaryata maganar ta ɓangaren gwamnatin.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named france24-20120113
  2. "Boko Haram militant leader is dead, Nigerian military says". France 24 (in Turanci). 25 September 2014. Retrieved 19 February 2020.
  3. "Nigeria army claims death of Boko Haram leader". www.aa.com.tr. Retrieved 19 February 2020.
  4. Akinyelure, Didi (27 September 2016). "Dead or alive? The six lives of Boko Haram's leader". BBC News (in Turanci). Retrieved 19 February 2020.