Tawayen Boko Haram, 2009
| |
Iri | rikici |
---|---|
Bangare na | Rikicin Boko Haram |
Kwanan watan | 29 ga Yuli, 2009 |
Wuri | Najeriya |
Rikicin Boko Haram na 2009 rikici ne tsakanin Boko Haram, kungiyar masu kaifin kishin Islama, da jami'an tsaron Najeriya.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Rikicin da ya barke a jihohi da dama a arewa maso gabashin Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 1,000, tare da kashe kusan 700 a birnin Maiduguri kadai, a cewar wani jami'in soji.[1][2][3]
Wani bincike da gwamnati ta gudanar ya gano cewa, yayin da aka dade ana takun saƙa tsakanin yan Boko Haram da jami’an tsaron Najeriya, abin da ya haddasa rikicin ya samo asali ne daga wata arangama da wasu gungun yan kungiyar suka yi da jami’an haraji na hadin gwiwa da ke unguwar gadar Gamboru kwastam a yankin, birnin Maiduguri. Yan Boko Haram din na kan hanyarsu ne domin binne daya daga cikin mambobinsu a makabartar Gwange. Jami’ai, a wani mataki na musamman na dakile tashe-tashen hankula da yawaitar miyagun laifuka a jihar Borno, sun bukaci matasan (yan boko haram), da su bi dokar da ta tanadi fasinjojin babura na su sanya hular kwano. Sun ki yarda, kuma a arangamar da ta biyo baya, yan sanda sun harbe wasu da dama daga cikin mutanen.[1]
A cewar rahotannin farko da aka samu daga kafafen yaɗa labarai, rikicin ya fara ne a ranar 26 ga watan Yuli lokacin da kungiyar Boko Haram ta kai hari a ofishin yan sanda a jihar Bauchi. An yi arangama tsakanin yan bindiga da rundunar ‘yan sandan Najeriya a Kano, Yobe da kuma Borno jim kadan. Sai dai shugaban kasa (na lokacin) Umaru 'Yar'aduwa ya yi sabani kan wannan lamari, inda ya ce jami'an tsaron gwamnati ne suka fara kai hari.
Error: No text given for quotation (or equals sign used in the actual argument to an unnamed parameter)
— "Ina so in jaddada cewa wannan ba rikicin addini ba ne kuma ba kungiyar Taliban ce ta fara kai wa jami'an tsaro hari ba, a'a. Sakamakon bayanan tsaro da aka tattara kan aniyarsu...su kai wani babban hari,” inji shi.[4]
Kisan shugaban kungiyar
[gyara sashe | gyara masomin]Sojojin Najeriya sun kewaye gidan Ustaz Mohammed Yusuf, wanda ya kafa kuma jagoran kungiyar Boko Haram tun 2002, a Maiduguri a ranar 28 ga watan Yuli bayan da mabiyansa suka yi wa kansu shinge. A ranar 30 ga watan Yuli ne sojoji suka kama Yusuf tare da Mika shi hannun yan sanda. A takaice dai sun kashe shi a bainar jama'a a wajen hedikwatar 'yan sanda.[5]
Islam Online ta nuna cewa siyasa ce ta haddasa tashin hankalin ba addini ba.[6] An kashe mutane irin su Fasto Kirista George Orjih.[7][5]
Kafin wannan arangama, da yawa daga cikin shugabannin musulmin yankin da akalla jami’in soja daya sun gargadi hukumomin Najeriya game da kungiyar Boko Haram. An yi “kunnen uwar shegu” da waɗannan gargadi n.[3]
Bauchi, Jihar Bauchi
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 26 ga watan Yuli, sama da mutane 50 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a Bauchi, yayin da wata gobara ta tashi a yayin da wasu yan kungiyar Boko Haram su 70 a Najeriya suka kai wa ofishin yan sanda hari, wadanda ke dauke da gurneti da kananan makamai. An kashe sojan gwamnati daya da mayakan Boko Haram 32 bayan harin farko da aka kai.[8][9] Gwamnati ta ce an kashe 'yan ta'adda 39, kuma ta tabbatar da mutuwar soja guda ɗaya. Kungiyar Boko Haram ce ta fara kai harin bayan ‘yan sanda sun tsare shugabanninsu.[8] Jami’an tsaro sun yi ramuwar gayya ta hanyar kai samame a unguwannin da ‘yan kungiyar suka jibge.[8]
Isa Yuguda, Gwamnan Jihar Bauchi, ya yi tsokaci: “Mun riga mun fatattaki ‘yan bindigar. In ba haka ba da lamarin ya yi muni. Ina kira ga daukacin al’ummar Bauchi da su kwantar da hankalinsu kuma su sani anriga da an shawo kan lamarin.”[10]
Gwamna Yugudan ya ayyana dokar hana fita da daddare, kuma yan sanda sun ci gaba da Sa ido don ganin an kiyaye dokar.[9][11] Kasuwanci a wuraren na cigaba da gudana a yankin.[9]
Maiduguri, Jihar Borno
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Yulin 2009, kafafen yada labarai sun ruwaito cewa an gano gawarwaki 100 a gefen hedikwatar yan sanda a Maiduguri.[11][12] Ɗaruruwan mutane ne ke barin gidajensu domin gujewa tashin hankalin.[11][12] An samu labarin fasa gidan yarin, amma ba a tabbatar da faruwar hakan ba.[11] Gawarwakin farar hula da dama birjik a titunan birnin; Wadanda suka shaida lamarin sun ce an harbe su ne bayan an ciro su daga cikin motocinsu.[11] Sojojin da yan sandan kasa duk sun yi sintiri da harbi kan waɗanda ake zargi. [11]
A ranar 28 ga watan Yuli ne aka ce sojojin sun kai farmaki a harabar shugaban kungiyar Mohammed Yusuf da wani masallaci da mabiyansa ke amfani da shi a Maiduguri babban birnin jihar Borno. Sojoji sun yi ruwan bama-bamai a gidan Mohammed Yusuf da ke cikin birnin bayan da mabiyan sa suka yi wa kansu shinge.[13][14] An yi ta harbe-harbe a faɗin birnin.[13]
A ranar 30 ga watan Yuli ne jami’an tsaron Najeriya suka kashe mayakan Boko Haram 100 a wani fada a Maiduguri. Jami'an tsaro sun abka cikin wani masallaci da yan ta'adda suka mamaye, inda suka yi ta harbin bindiga a ciki. A wani labarin kuma jami’an soji da na yan sanda sun yi artabu da yan bindiga gida-gida. Da farko dai an bayyana cewa an kashe mataimakin shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, amma daga baya aka ce yana raye.[15] An kuma kashe yan sandan Najeriya. Bayan da gwamnati ta ayyana neman a kawo tsaro a Maidguri, sojojin Najeriya sun fara kafa shingaye domin yin luguden wuta a sauran wuraren da yan ta'addan suka rage.[16]
A ranar 30 ga watan Yuli ne sojoji suka kama Yusuf tare da Mika shi ga ‘yan sanda a hedikwatar ‘yan sanda da ke Maiduguri. Jami’an yan sanda sun yi wa Yusuf kisan gilla a cikin harabar gidan, kuma a bainar jama’a.[5][17] Da farko dai jami’an ƴan sanda sun yi iƙirarin cewa ko dai an harbe Yusuf ne a lokacin da yake kokarin tserewa ko kuma ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a yayin artabun sa da sojoji.[5][17] Rundunar ƴan sandan ta kuma kashe wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram da suka hada da surukin Yusuf a wajen hedikwatar yan sandan.[5][17]
A ranar 2 ga watan Agusta, an gano wasu mata da yara da Boko Haram suka sace a kulle a wani gida a Maiduguri.[18] Sojojin sun ce an kashe mutane 700 a Maiduguri yayin arangamar. [18] Daga baya kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta kwashe gawarwaki 780 daga titunan birnin domin binne su a kaburbura.[19]
Potiskum, Jihar Yobe
[gyara sashe | gyara masomin]An shafe sa'o'i da dama ana gwabza fada a garin Potiskum. Mayakan na Boko Haram sun kona ofishin yan sanda ta hanyar amfani da babura dauke da mai. Kuma ofishin yan sandan ya kone kurmus, a sakamakon haka, an kashe jami’in dan sanda da jami’in kashe gobara. Yan sanda sun yi artabu da mayakan tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu. Harwayau yan sanda sun kama mayaka 23 bayan yakin.[11] A cewar majiyoyin Najeriya, an kashe mayakan Boko Haram 43 a wani harbi da aka yi a kusa da birnin a ranar 30 ga watan Yuli.[20][21]
Wudil, Jihar Kano
[gyara sashe | gyara masomin]An kashe mutane uku a wani hari da aka kai a Wudil, kuma jami’an yan sanda sun kama fiye da 33.[11] An jikkata babban jami’in ‘yan sanda na Wudil.[11]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Fasa Gidan Yarin Bauchi a Jihar Bauchi
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Umar, Sani (2011). "The Discourses of Salafi Radicalism and Salafi Counter-radicalism in Nigeria : A Case-study of Boko Haram". Northwestern University: 12. Cite journal requires
|journal=
(help) - ↑ Bavier, Jow (17 February 2012). "Nigeria: Boko Haram 101". Pulizer Center on Crisis Reporting. Archived from the original on 23 August 2015. Retrieved 13 July 2015.
- ↑ 3.0 3.1 "Nigeria accused of ignoring sect warnings before wave of killings". The Guardian. London. Associated Press. 2 August 2009. Retrieved 6 August 2009.
- ↑ "Nigeria accused of ignoring sect warnings before wave of killings". Boston.com. Associated Press. 8 March 2012. Archived from the original on 25 July 2012. Retrieved 6 August 2009.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 5.3 5.4 Human Rights Watch (11 October 2012). Spiraling Violence: Boko Haram Attacks and Security Force Abuses in Nigeria. Retrieved 27 June 2015.
- ↑ Oriyomi, Rafiu (29 July 2009). "Politics Vs Religion in Nigeria Attacks". IslamOnline. Archived from the original on 31 July 2009. Retrieved 29 July 2009.
- ↑ Ola, Timothy (6 August 2009). "Boko Haram: How 3 pastors were beheaded eyewitness". Sun News Online. Archived from the original on 12 August 2009.
- ↑ 8.0 8.1 8.2 "Nigeria forces kill 32 after attack on police station". Reuters. 26 July 2009. Retrieved 27 July 2009.
- ↑ 9.0 9.1 9.2 "Security forces kill 50 in Nigeria". The Irish Times. 26 July 2009. Retrieved 27 July 2009.
- ↑ "Religious riots in Bauchi". Oyibos OnLine (in Turanci). 2009-07-27. Retrieved 2020-02-03.
- ↑ 11.0 11.1 11.2 11.3 11.4 11.5 11.6 11.7 11.8 "Nigerian Islamist attacks spread". BBC News. 27 July 2009. Retrieved 27 July 2009.
- ↑ 12.0 12.1 "Over 100 dead in Nigerian clashes". RTÉ. 27 July 2009. Archived from the original on 30 July 2009. Retrieved 27 July 2009.
- ↑ 13.0 13.1 "Nigerian troops shell Islamists". BBC News. 28 July 2009. Retrieved 28 July 2009.
- ↑
- "Sect leader's home shelled". news.com.au. Agence France-Presse. 29 July 2009. Archived from the original on 2 August 2009. Retrieved 28 July 2009.
- "Nigerian troops surround militant hideout". The Miami Herald. 28 July 2009. Retrieved 28 July 2009. [dead link]
- ↑ "Islamist leader Shekau 'hiding in the desert'". Worldwide Religious News. 16 July 2010. Retrieved 13 July 2015.
- ↑ Smith, David; Press, Associated (2009-07-30). "Nigerian forces storm militant Islamist mosque". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Retrieved 2020-01-22.
- ↑ 17.0 17.1 17.2 "Video shows Nigeria 'executions'". Al Jazeera. 9 February 2010. Retrieved 27 June 2015.
- ↑ 18.0 18.1 "Nigerian police find sect women". BBC News. 2 August 2009. Retrieved 2 August 2009.
- ↑ "Nigeria tops happiness survey" (in Turanci). 2003-10-02. Retrieved 2022-09-28.
- ↑ "Spiraling Violence | Boko Haram Attacks and Security Force Abuses in Nigeria". Human Rights Watch (in Turanci). 2012-10-11. Retrieved 2020-01-30.
- ↑ Group, Sinclair Broadcast (2009-07-30). "Nigeria: Rights worker says civilians being killed". WPDE. Archived from the original on 2020-02-07. Retrieved 2020-02-07.
Hanyoyin hadi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Al Jazeera (9 Fabrairu 2010), Bidiyo ya nuna 'kisa' a Najeriya
- Baldauf, Scott (29 ga Yuli, 2009), "Sojojin Najeriya sun shiga kan masu tsattsauran ra'ayin Islama", Christian Science Monitor
- Human Rights Watch (2012), Tashin hankali: Hare-haren Boko Haram da cin zarafin Jami'an Tsaro a Najeriya, 11 Oktoba 2012
- Murtada, Ahmad (2013), Boko Haram: Farko, Ka'idoji da Ayyukanta a Najeriya, Sashen Nazarin Addinin Musulunci, Jami'ar Bayero, Kano, Nigeria