Umaru Musa Yar'Adua

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Simpleicons Interface user-outline.svg Umaru Musa Yar'Adua
Umaruyaradua07052007.jpg
shugaban ƙasar Najeriya

29 Mayu 2007 - 5 Mayu 2010
Olusegun Obasanjo - Goodluck Jonathan
gwamnan jihar Katsina

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Joseph Akaagerger - Ibrahim Shema
Rayuwa
Haihuwa Katsina, 16 ga Augusta, 1951
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Fillanci
Mutuwa Aso Rock Villa, 5 Mayu 2010
Makwanci Jihar Katsina
Yanayin mutuwa  (Churg-Strauss syndrome (en) Fassara)
Ƴan uwa
Mahaifi Musa Yar'Adua
Abokiyar zama Turai Yar'Adua  (1975 -  5 Mayu 2010)
Ahali Shehu Musa Yar'Adua
Karatu
Makaranta Kwalejin Barewa
Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Fillanci
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan/'yar siyasa, university teacher (en) Fassara da entrepreneur (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
Umaru Musa Yar'Adua a wani babban taro
Umaru Musa Yar'Adua a wani taro

Umar Musa Yar'adua G.C.F.R (an haife shi a ranar 16 ga watan Agustan shekara ta 1951) a cikin birnin Katsina da ke arewacin Najeriya.[1] [2] Mahaifinsa ya kasance tsohon ministan birnin Lagos na farko a jamhuriya ta farko, kuma kafin rasuwar sa shi ne Matawallen Katsina, sarautar da shi marigayin Umaru Musa 'Yar'adua ya gada daga wajen mahaifinsa wato Musa Yar'adua.[3] Akwai dan uwansa (babban yayan sa) watau Shehu Musa Yar'adua, wanda shi ma shahararren ɗan siyasa ne a kasar Najeriya; kuma shi ya kafa jam'iyyar "PDM" (People's Democratic Movement), Shehu Musa Yar'adua ya rasu a gidan yari a shekarar 1997.[1].

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Shugaba Umaru Musa a wani babban taro a Abuja

Marigayi Umaru Musa Yar'aduwa ya fara makarantar Firamarensa ne a Rafukka ne a shekara ta 1958, kafin a mayar da shi makarantar sakandare ta kwana da ke karamar hukumar Dutsin-ma a shekara ta 1962. Ya kuma halarci kwalejin gwamnati da ke Keffi daga shekarata 1965 zuwa shekarata 1969. Sai ya wuce kwalejin Barewa a shekarata 1971, inda ya samu takardar shedar karatunsa ta HSC.[3]

Tsohon shugaba 'Yar'aduwa ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga shekarata 1972 zuwa shekara ta 1978 inda ya samu takardar shedar Digirinsa akan kimiyyar haɗa sinadirai (Chemistry) da Koyarwa, kafin ya koma domin samun babban digiri duk dai akan kimiyyar hada sinadarai (Chemistry). Marigayin yayi bautar ƙasarsa ne a Jihar Lagos inda ya koyar a makarantar Holy Trinity daga shekarar 1975 zuwa shekara ta 1976.[3]

Bayan da ya kammala aikin yiwa ƙasa hidima ya fara aikin koyarwa kadan-kadan a kwalejin share fagen shiga jami'a da ake kira CAST da ke Zariya a tsakanin shekara ta 1976 zuwa shekara ta 1979. A shekara ta 1983 marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'aduwa ya bar aikin koyarwa ya fara aiki da Gonar Sambo Farms a Funtua, da ke a jihar Katsina inda ya zama GM daga shekarata 1983 zuwa shekara ta 1989.

Daga shekara ta alif 1984 bayan da Sojoji suka yi juyin mulki, Malam Umaru Musa 'Yar'aduwa an kira shi domin zama wakili a hukumar gudanarwar kanfanoni da hukumomin gwamnati da dama da suka haɗa da hukumar samar da kayan Noma da kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar katsina, Bankin Habib,Hamada Carpets,Madara Limited,da kuma kanfanin buga Jaridu da Mujallar The Nation wanda ke Kaduna wanda kuma wansa Marigayi Janar Shehu Musa 'Yar'aduwa ya mallaka.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A lokacin da marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'aduwa ya shiga siyasa, ya samu sabani da mahaifinsa, wanda a wancan lokacin yake mataimakin shugaban Jam'iyar NPN, inda shi kuma ya zama wakili a jam'iyar PRP ta Malam Aminu Kano mai adawa da NPN. A lokacin da Janar Babangida ya kaɗa gangar siyasa ya zama sakataren jam'iyar SDP a jihar ta Katsina kuma ɗan takararta na gwamna, amma kuma ɗan takarar jam'iyar NRC na wancan lokaci Malam Saidu Barda ya kada shi a zaben. To sai dai duk da haka bai hakuri ba inda a shekara ta 1999 Malam Umaru Musa 'Yar'aduwa ya tsaya takarar muƙamin gwamnan jihar ta Katsina kuma ya samu nasara a ƙarƙashin jam'iyar PDP,

Haka kuma ya sake samun nasara a zaɓen da aka yi a shekara ta 2003.

lokacin da Umaru Musa Yar'adua ya zama shugaban kasa

A shekarar 2007 Umaru Musa 'Yar'aduwa ya zama ɗan takarar muƙamin shugaban ƙasa na Jam'iyar PDP bayan ya samu taimakon tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya zama shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, wannan ya bashi daman sanya rigar siyasa na koli a shekarar. [4]

Umaru Musa Yar'adua a wani taro

To sai dai rashin lafiya da tsohon shugaban ya yi fama da ita, ta sanya bai samu sukunin gudanar da harkokin mulki kamar yadda ya yi fata ba, musanman ƙudirorinsa guda bakwai daya tsara na ciyar da ƙasar ta Najeriya gaba kafin nan da ƙarni na 2020.[5]

Kudurorinsa guda 7 (7 point Agenda)

A lokacinda marigayi ya zama shugaban

kasan Nijeriya ya zayyana kudurorinsa na mulki kyawawa guda bakwai da yake so ya cimma a matsayinsa na shugaba kafin shekara ta 2020[1], wanda aka sanyawa laqabi da 'mahangar shekarata 2020' watau (Vision 2020),[6]wanda suka hada da;

 1. Samar da isasshiyar wutar lantarki a ko ina a fadin kasa.
 2. Samar da isasshiyan lafiyayyen abinci a kowane sako da loko dake fadin kasar.
 3. Samar da arziki a kasa musamman a harkokin noma, kere-kere da kuma haqe-haqen albarkatun kasa da karafa da kuma sarrafa su a cikin kasar ta Najeria.
 4. Inganta fannin harkokin sufuri ta hanyar gyara hanyoyin da suka samu matsala da kuma ababan hawa zuwa na zamani.
 5. inganta fannin filaye da samar da muhalli da filayen noma, da na manyan masana'antu ga yan Nageria.
 6. SamardaTsaro - acewarsa tabbatar da tsaro wajibi ne don cigaban kasa, domin wanzuwar zaman lafiya kadai kan bunqasa harkokin kasuwancin kasa baki daya da kuma tabbatar da adalci tsakanin talakawa da Gwamnatin Tarayya.
 7. Ilimi - zai inganta harkokin ilimi a kasa wacce zata riski tsarin ilimi na duniya. Wanda za'a iya cimma wannan buri ne kadai ta hanyar yin gyara managarci a fannin ilimi a Nijeriya.

Rasuwar sa[gyara sashe | gyara masomin]

Marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'adua ya rasu ne a sanadiyar rashin lafiya da ya daɗe yana jinya, ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekarata 2010 a fadar gwamnati da ke Abuja watanni biyu bayan komowarsa gida daga kasar Saudiya inda yake jinya.

Iyalin sa[gyara sashe | gyara masomin]

Turai 'Yar'adua uwar gidan Umar Musa 'Yar'Adua

Umaru Musa ya rasu ne ya bar mahaifiyarsa da 'yan'uwansa da matan Aure guda biyu Hajiya Turai Yar'Adua tare da 'ya'ya bakwai da ya haifa da ita da suka haɗa da mata biyar, da maza biyu. Haka kuma yana da wasu 'ya'ya biyu maza da matarsa ta biyu Hajiya Hauwa Umar Radda. [7] [8]

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

 • Adeniyi, Olusegun, 1965- (2011). Power, politics and death : a front-row account of Nigeria under the late President Umaru Musa Yar'Aduwa. Lagos, Nigeria: Prestige. ISBN 978-978-50726-0-0.
 • Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. 1.0 1.1 1.2 "Umaru Musa Yar'Adua | Profile | Africa Confidential". www.africa-confidential.com. Retrieved 2021-04-10.
 2. "Umaru Yaradua | Encyclopedia.com". www.encyclopedia.com. Retrieved 2021-04-10.
 3. 3.0 3.1 3.2 https://www.bbc.com/hausa/mobile/news/2010/09/100922_umaru_yaradua.shtml
 4. Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. p. 138 ISBN 978-978-906-469-4.
 5. Lagos, Rasheedat Ola in. "Yar'Adua's Seven Point Agenda: any hope for the Nigerian people?". In Defence of Marxism. Retrieved 2021-04-09.
 6. "Vision 2020, Nigeria - Google Search". www.google.com. Retrieved 2021-04-09
 7. https://www.britannica.com/biography/Umaru-Musa-YarAdua
 8. https://www.bbc.com/hausa/news/2010/09/100922_umaru_yaradua