Muhammadu Dikko
Muhammadu Dikko | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1865 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 1944 |
Makwanci | Jihar Katsina |
Sana'a | |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Sarki Alhaji Muhammadu Dikko kuma anfi sanin sa da Muhammad Dikko ɗan Gidado CBE (an haife shi a shekara ta alif 1865 – May 1944)[1], ya kasance Sarkin Katsina ne na 47th, wanda ya yi mulki daga 9 ga watan Nuwamba shekara ta, alif 1906 har zuwa rasuwarsa a shekara ta, 1944. Shine sarkin Katsina na tara (9) a bangaren Fulani[1].
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shi a shekara ta 1865[2], a lokacin Sarki Muhammadu Bello, an naɗa shi sarauta lokacin yana da shekara ashirin da biyu (22) da haihuwa[1].
An naɗashi Durbi daidai lokacin yaƙin Basasar Kano. A lokacin da Lord Lugard ya shiga garin katsina, Dikko yana matsayin Durbin Katsina kuma an bashi alhakin kula da Turawa, cinsu da shan su, ƙibarsu da ramar su na hannunsa kamar yadda kuma sarkin lokacin watau Sarki Abubakar ya umurceshi[3].
Tarihi ya nuna cewa lokacin da aka naɗa sarki muhammad Dikko yana Gobir don siyayyar Raƙuma na Sarki Abubakar na lokacin daga nan aka tura masa takarda ya dawo, akan hanya ya haɗu da ɗan aike (mallam Giɗaɗo) daga liman wazirin katsina Haruna, cewa an kama Sarki Yero, an kuma naɗa shi sarki[4].
Da isowar bariki joji yace “Gwamna ya aiko, kaine Sarki” daga nan ya kama sarautar katsina[4].
Tafiye Tafiye
[gyara sashe | gyara masomin]Sarki Muhammadu Dikko yana ɗaya daga cikin sarakunan da suka fi kowa tafiye-tafiye zuwa ƙasashen qetare[4]. Daga lokacin da sarki zai je garin Makkah, Gwamna lugard ya haɗashi da soja mai suna “Mr. Wafaster” (webster) ya rakashi har Makka ya tashi katsina ranar talatin ga watan biyar a shekara ta, 1920, sannan ya isa birnin landan a biyar ga watan Bakwai a shekara ta, 1920. Sarkin ingila Nelo ya bashi lambar girma (Kings Medal for African Chiefs) a ranar 29 ga watan 7 a shekara ta, 1920, ya isa jidda wanda sharifin Makka Usaini ya amshe su, ya kare aikin hajji a ranar 12 ga watan 9 a shekara ta, 1920. Sannan ya fara biyawa ta ingila sannan ya dawo katsina a ranar 22 ga watan nuwamba a shekara ta, 1920[5].
A shekara ta, 1924, Sarki Dikko ya ƙara komawa Ingila don halartar taron nuna kayan ciniki na ƙasashen Ingila (Empire Exhibition).[5]Sarki ya ƙara komawa aikin hajji a shekarar, 1933 inda ya sake biyawa ta turai a shekarar, 1937 ya sake komawa Turai don ayi masa maganin idonsa dake ciwo[6].
Harkokin Wasanni
[gyara sashe | gyara masomin]Duk wanda yasan Sarki Muhammadu Dikko yasanshi da son wasanni na motsa jini musamman wasan dawaki na polo. An kuma fara wasan dawaki watau Polo a katsina a shekarar, 1921, sannan mafi yawanci wanda suka buga wasan ƴa’ƴan sarki ne, da ƴa’ƴan hakimai, da ƴa’ƴan Wazirai. Kuma sarki ya kafa ƙungiyar kwallo da ake kira “katsina polo club”[7].
Gwanayen polo a katsina sun haɗa da;
- Usman Nagoggo (6)
- Alhaji Ibrahim Galadiman Magani (4)
- Alhaji Yusuf (3)
- Ɗan Dada (3)
Wanda ake kiran wannan lambobi “ Nigerian Polo Association Handicape[8]”
Noma
[gyara sashe | gyara masomin]Sarki Muhammadu Dikko ya kula da sha’anin Noma sosai wanda har alƙalin zazzau, Mallam Ahmadu Lugge, ya kanyi masa kirari da “Sahibul Harakaati Wal garaasati”[9].
Rasuwar Sarki
[gyara sashe | gyara masomin]Sarki Muhammadu Dikko ya rasu a watan Fabrairu shekarar, 1944, bayan yayi jinya na kusan wata uku[10].
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Photos of Muhammad Dikko dan Gidado, ca. 1910
-
Photos of Muhammad Dikko dan Gidado, ca. 1910
-
285x285px
-
thumb
-
Muhammad Dikko a BBC
-
Dikko tare da Turawa a 1911
-
Muhammad Dikko Ya ziyarci gidan Tarihi na Ingila.
-
Sarkin Katsina tare da jami'ai a 1911 a birnin Katsina
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers.ISBN 978-135-051-2. OCLC 43147940.
Sani Abubakar Lugga, 1950- (2006). Dikko dynasty : 100 years of the Sullubawa ruling house of Katsina, 1906-2006. Katsina, Nigeria: Lugga Press. ISBN 978-978-2105-20-2. OCLC 137997519.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.14. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ Sani Abubakar Lugga, 1950- (2006). Dikko dynasty : 100 years of the Sullubawa ruling house of Katsina, 1906-2006. Katsina, Nigeria: Lugga Press. p.2. ISBN 978-978-2105-20-2.
- ↑ Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.15. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 Burji,Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.16. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ 5.0 5.1 Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.16-17. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.17. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.19. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.20. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.22. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji :tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.28. ISBN 978-135-051-2.