Keffi
Keffi | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Nasarawa | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 138 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Lambar aika saƙo | 961101 | |||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Keffi karamar hukuma ne, da ke a jihar Nasarawa, a ƙasar Najeriya . Hedkwatar ta tana cikin garin Keffi. Keffi na da tazarar kilomita 50 daga Abuja. Jami'ar Jihar Nasarawa tana garin Keffi zaune a kan hanyar Keffi zuwa Akwanga.
Yana da yanki 138 km2 da yawan jama'a kusan 2 a ƙidayar ta shekara ta 2006. Lambar gidan waya na yankin ita ce 961.
An kafa garin Keffi a shekara ta 1802 a hannun wani jagoran Fulani Abdu Zanga wanda ya karbi sarautar sarki. [1] Karamin mulkinsa ya kasance karkashin masarautar Zariya wanda sai da ta rika biyan harajin bayi a duk shekara. [2]
A cikin shekarar alif ta 1902 Keffi ne wani lamari ya faru wanda ya kai ga mamaye Arewacin Najeriya, bayan “magaji”, wakilin Sarkin Zariya ya kashe wani Bature. A lokacin da Magaji ya samu mafaka a Kano, wannan shi ne dalilin da Lugard ya sanya ya mamaye halifancin arewa. [3]
Fitattun mutane
[gyara sashe | gyara masomin]- Imaan Sulaiman-Ibrahim – Darakta-Janar na NAPTIP
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Keffi, an Encyclopaedia Britannica entry, lookup ion March 2019
- ↑ The Ancient City of Keffi (Nasarawa State), Muzzammilwrites blog dated 22 November 2017, lookup in March 2019. The blogpost quotes from "Notes on Nassarawa Province, Nigeria", by Sciortino, J. C, p.7, Publication date ca. 1920, original accessible via [https://archive.org/details/notesonnassarawa00scioiala archive.org
- ↑ cf. Sciortino p.7