Imaan Sulaiman-Ibrahim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Imaan Sulaiman-Ibrahim
Rayuwa
Haihuwa Jos, 19 ga Afirilu, 1980 (44 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Abuja (en) Fassara Digiri a kimiyya
Webster University (en) Fassara Master of Science (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Imaan Sulaiman-Ibrahim, ƴar siyasa ce kuma ƴar kasuwa a Najeriya. Ta shugabanci Hukumar NAPTIP daga ranar 1 ga watan Disamban 2020 har zuwa 27 ga watan Mayun, 2021, lokacin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da sauya sheka sannan aka mayar da ita muƙamin mai girma kwamishiniyar tarayya na Ƴan Gudun Hijira, Baƙi da waɗanda suka rasa Muhallansu na ƙasa.[1]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Imaan ta taso a Abuja, Najeriya. Ta halarci Makarantar Nursery Aruwa da ke Abuja da Jabi Primary School (LEA Primary School Jabi) bayan gama karatun firamare ta shiga Kwalejin Ƴan mata ta Gwamnatin Tarayya dake Bwari Abuja don yin karatun sakandare. Tana da shekaru 19 ta kammala karatu a jami'ar Abuja inda ta yi digiri a fannin zamantakewa. Tana da shekaru 21, ta sami digiri na biyu daga Webster University, MBA da MA. Ta yi aikin bautar ƙasa a NNPC, ofishin shiyyar Kaduna.[2][3]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Imaan ta fara aiki ne a Abuja Geographic Information Systems, (AGIS), kafin ta koma Ingila inda ta yi aiki a fannin albarkatun dan Adam (Human Resources), kafin ta zama mai ba da shawara ta SAP HCM. Imaan ta koma Mary Kay daga baya ta zama babbar darektan tallace-tallace. Ta kasance mai ba da shawara ta musamman kan dabarun sadarwa ga karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba kuma tsohuwar mamba a majalisar ba da shawara kan tattalin arziki ta Jihar Nasarawa. Tsohuwar Darakta-Janar a Hukumar Hana safarar mutane ta ƙasa na tsawon watanni 6 daga Disamba 2020 zuwa Mayu 2021. Ta kuma riƙe muƙamin mai girma Kwamishinan Tarayya a Hukumar Kula da Ƴan Gudun Hijira da Ofishin Ƴan Gudun Hijira ta Ƙasa har zuwa Yuni 4, 2021.[2][3][4]

Darakta Janar ta NAPTIP[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 1 ga Disamba, 2020, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Imaan Sulaiman-Ibrahim a matsayin darakta-Janar na Hukumar Hana Fataucin Bil Adama ta Kasa, NAPTIP na tsawon shekaru hudu don maye gurbin Julie Okah-Donli . Ta yi aiki a matsayin Darakta-Janar na NAPTIP na tsawon watanni 6 daga Disamba 2020 zuwa Mayu 2021, bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na komawa ofishin Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira da Muhawara ta Kasa a matsayin Mai Girma Kwamishinan Tarayya.[5]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Imaan Sulaiman-Ibrahim a Jos, Jihar Filato, a Najeriya. Ta fito daga Keffi, Jihar Nasarawa, Najeriya. Mahaifinta shi ne SK Danladi, injiniya kuma mazaunin Abuja. Mahaifiyarta ita ce Aishatu Sulaiman Danladi, malama. Ita ce ta biyu a gidan mai yara takwas. Sulaiman-Ibrahim tana da aure da ƴa-ƴa uku.[2][3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Buhari Swaps Heads of Two FG Agencies". Premium Times. 27 May 2021. Retrieved 27 May 2021.
  2. 2.0 2.1 2.2 "I Have Zero Tolerance For Negativity – Iman". Leadership Newspaper. Retrieved 7 December 2020.[permanent dead link]
  3. 3.0 3.1 3.2 Alhassan, Amina (5 August 2018). "Iman Sulaiman-Ibrahim - Inspiring women involvement in politics". Daily Trust Newspaper. Retrieved 7 December 2020.
  4. "President Buhari Appoints Imaan Sulaiman-Ibrahim as Director-General, NAPTIP". Government of Nigeria. 1 December 2020. Retrieved 7 December 2020.
  5. Adetayo, Olalekan (1 December 2020). "UPDATED: Buhari appoints new DG for NAPTIP". The Punch Newspaper. Retrieved 7 December 2020.