Atiku Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Atiku Abubakar
mataimakin shugaban ƙasar Najeriya

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Mike Akhigbe - Goodluck Jonathan
Rayuwa
Haihuwa Jada (Nijeriya), 25 Nuwamba, 1946 (77 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Ƴan uwa
Abokiyar zama Amina Titi Atiku Abubakar
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a customs officer (en) Fassara da ɗan siyasa
Employers Najeriya
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress
atiku.org
hoton dan siyasa atiku abubakar
hoton atiku da muhammad buhari

Atiku Abubakar'About this soundAtiku Abubakar  (an haife shi a ranar 25 ga watan Nuwamba shekara ta alif dari tara da arba'in da shida, 1946) Miladiyya. ya kasance dan siyasan Najeriya kuma dan kasuwa ne wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasar Najeriya daga shekara ta alif Dari Tara da cassa,in da tara , 1999 zuwa shekara ta 2007 lokacin shugabancin Olusegun Obasanjo.[1][2][3] Atiku ya nemi zama gwamnan Jihar Adamawa a shekara ta alif, 1990 zuwa 1996 daga baya kuma, a shekara ta alif, 1998, aka zaɓe shi kafin nan ya zama mataimakin Olusegun Obasanjo a Zaben shekarar, 1999 na shugaban kasar Najeriya an kuma sake zaben su a zaben shugaban kasar Najeriya ta 2003.[4]

Majar Atiku a jam'iyar APC

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Atiku haifaffen jihar Adamawa ne.[5] An haifeshi a jahar Adamawa acikin garin Jada da daya tilo awajen garba Abubakar da mahaifiyarshi Aisha kande.https://newswirengr.com/2023/02/28/atiku-abubakar-biography-education-career-marriage-net-worth-achievements-and-controversy/

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Atiku bayan zabe

Atiku Abubakar yayi rashin nasarar samun zama shugaban kasar Najeriya a matakai har sau shida. Da farko a 1993, 2007, 2011, 2015 da kuma 2019. A shekarar 1993, yayi takara a karkashin Social Democratic Party dan neman zama shugaban kasar amma ya sha kaye a wurin Moshood Abiola da Baba Gana Kingibe. Ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Action Congress a Zaɓen Shugaban kasar Najeriya ta 2007 amma yayi rashin nasara da zuwa na uku a wurin Umaru Yar'Adua na jam'iyyar PDP da Muhammadu Buhari na ANPP. Ya nemi zama dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party lokacin Zaɓen Shugaban kasar Najeriya ta 2011 nan ma yayi rashin nasara a hannun shugaba mai ci Goodluck Jonathan.[6] A shekara ta, 2014, Atiku ya koma jam'iyyar APC gabanin Zaɓen Shugaban ƙasar Najeriya ta 2015 kuma ya nemi zama ɗan takarar jam'iyyar amma yayi rashin nasara a hannun Muhammadu Buhari. A shekarar, 2017, ya sake komawa jam'iyyar PDP a inda kuma ya zama dan takarar jam'iyyar a Zaben Shugaban kasar Najeriya ta 2019, sai dai har wayau ya sake rashin nasara a hannun shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.[7][8]. A shekarar, 2022 Atiku Abubakar ya bayyana sha'awarsa ta fitowa takarar shugaban kasa a Jam'iyyar PDP mai adawa inda zai kara da Bola Ahmad Tinubu na APC, da Peter Obi na Jam'iyyar Labour da Rabiu Musa Kwankwaso na Jam'iyyar NNPP da sauran Yan takara na kananan jam'iyyu. Bayan fafatawa mai zafi ta cikin gida da kuma ta sauran abokan karawa, hankula sun kasu gida daban-daban kuma da yawan jama'a sun kyautata zaton Atiku ne zai lashe Zaben. Daga cikin dalilan sa ran nasararsa har da rabuwar kanu a cikin ita jam'iyyar APC. Kari kan wannan, jama'a na cikin tsananin talauci da rashin tsaro a Birane da ƙauyuka. Wani abin damuwa shi ne yanda kwatsam gwamnati ta yi sauyin kudi wanda hakan ya jawo karancinsu a hannun mutane. Hatta da su mukarraban jam'iyyar APC sun zargi cewa an yi haka dan kassara tafiyar Tinubu. Atiku Abubakar ya nuna gamsuwar sa da wannan sauyin kuɗi. Bayan an yi zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu na shekarar, 2023, an kwashe kwanaki huɗu ana tattara sakamakon zaɓen kuma da asubahin wayuwar garin Laraba, shugaban hukumar zaben INEC ya bayyana Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.[9]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Profile of Atiku Abubakar: From an only child of a father who opposed western education to a political guru". Nigeria Today. 2 October 2018. Archived from the original on 3 January 2019. Retrieved 3 January 2019.
  2. Adeosun, Olajumoke (2019-07-17). "Atiku Abubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria". Entrepreneurs In Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-09. Retrieved 2020-05-29.
  3. "Atiku Abubakar - the Nigerian operator who knows how to make money". BBC News (in Turanci). 2019-02-06. Retrieved 2020-09-11.
  4. Podcast, N. L.; Giveaway, N. L. (2019-11-25). "Happy Birthday!! Atiku Abubakar Celebrates His 73rd Birthday (Drop Your Well Wishes) » Naijaloaded". Naijaloaded (in Turanci). Retrieved 2020-05-29.
  5. "The Story of My Life by Atiku Abubakar". PM News Nigeria. 15 April 2019.
  6. Adeosun, Olajumoke (2019-07-17). "Atiku Atiku AbAbubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria". Entrepreneurs In Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-09. Retrieved 2020-05-29.
  7. "Atiku emerges PDP presidential candidate". The Punch (in Turanci). 7 October 2018. Retrieved 2019-04-19.
  8. "2023: Where Nigeria's President comes from, not important ― Atiku". Vanguard News (in Turanci). 2021-10-07. Retrieved 2022-02-22.
  9. https://punchng.com/topics/2023-elections Archived 2023-03-01 at the Wayback Machine