Amina Titi Atiku Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Amina Titi Atiku Abubakar
Rayuwa
Haihuwa Osun, 6 ga Yuni, 1949 (74 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Abokiyar zama Atiku Abubakar
Karatu
Makaranta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a gwagwarmaya da ɗan siyasa

Amina Titi Atiku Abubakar ta kasance ɗaya daga cikin matan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.[1] Tana daga cikin masu assasa 'yancin yara, kuma ita ta samar da ƙungiyar kula da satan yara da mata wato Gidauniyar Masu Fataucin Mata da Kawar da Aikin yi da Yara (WOTCLEF) kuma tana daga cikin waɗanda suka assassa[2] kafa hukumar kula sace-sacen yara na mata na Hukumar hana fataucin Bil-Adama ta Ƙasa (NAPTIP).[3]

Kuruciya da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Titi Abubakar a iyalan yarbawa daga ilesa na jihar Osun.[4][5] Tayi ilimin firamare a makarantan Lafiaji, Lagos sannan kuma ta cigaba da karatun ta na sakandire a makarantar St. Mary's Iwo, har zuwa shekara ta 1969i a jihar Lagos.[6][7]

Ta auri Atiku Abubakar a lokacin yana jami'in Custom kafin daga baya ta halarci Kaduna Polytechnic.[8] Bayan turanci, Titi tana jin yarukan yarbanci da kuma hausa sosai. Ta karbi addinin musulunci daga bisani.[9][10]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ta kasance malama a kwalejin fasaha ta jihar kaduna.[11]

Bayan ta cigaba da karatun ta a shekara ta 1986 zuwa shekarar 1987 a kasar Roma, ta hadu da yan matan Nigeria da yawa sun wanda ke sana'ar karuwanci ga uwargoyoyinsu,[12] kuma galibi ba biyansyu akeyi ba. Kuma ta gano galibi an yaudare su ne da cewa zsuyi aiki a kasar italiya ko wasu kasashen ketare. Sannan kuma ta ci alwashin yaki da wannan rashin adalcin.

WOTCLEF & NAPTIP[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan ne yasa titi tayi alkawari domin magance wannan matsalan da suka faru bayan dawowar ta a shekara ta 1999 lokacin da mijinta Atiku Abubakar ya zama mataimakin shugaban kasar Nigeria.

Tayi amfani da damar ta wajen bayar da shawarwari don kawo karshen karuwanci da tilastawa yan mata dama sauran siffofin fataucin mutane. Da farko ita ce ta kafa Gidauniyar kawar da safarar kananan yara(WOTCLEF) sannan ta dauki nauyin wani kudiri mai zaman kansa don hukunci mai tsanani ga masu fataucin, ta kuma kafa hukumar hana fataucin mutane ta kasa, ta kuma gudanar da kwasa-kwasan ilimi na maraba da yan mata da gyara su da dawo dasu daga kasashe daban zuwa gida Najeriya.[13]

Kyaututtuka[gyara sashe | gyara masomin]

  • Annual Nigerian Women's Award (2002)[14]
  • D'linga Award (2010)[15]

Wallafe-Wallafe[gyara sashe | gyara masomin]

Amina Titi Abubakar ta wallafa littattafai da dama wanda suka hada da:[16]

  • Educating the Nigerian Child[17]
  • Empower Law to Fight Child Slavery[18]
  • Let Us Celebrate Humanity: A collected speeches on women's right and human trafficking[19]

Kara dubawa[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "How I Met Married Atiku Titi Abubakar". premiumtimesng.com. News Agency of Nigeria. 18 November 2018. Retrieved 19 July 2021.
  2. "Women Trafficking and Child Labour Eradication Foundation (WOTCLEF)". The Communication Initiative Network. 21 March 2011. Retrieved 16 June2017.
  3. "More Laurels for Titi Abubakar". Vanguard News. 2018-01-26. Retrieved 2021-05-20.
  4. "My battle to marry Atiku Titi Abubakar - OnlineNigeria.com". nm.onlinenigeria.com. Online Nigeria. Retrieved 16 June 2017.
  5. "The News, Volume 18". Nigeria: Independent Communications Network Limited. 2002. p. 96.
  6. "Hajiya Titi Abubakar: Working to restore human dignity". www.weekend.peoplesdailyng.com. People's Daily. Archived from the original on 23 August 2017. Retrieved 16 June 2017.
  7. "My mum said she could give all her daughters to Atiku as wives —Titi Abubakar". Punch Newspapers. 2018-12-02. Retrieved 2021-05-20.
  8. Onukaba Adinoyi-Ojo (2006). Atiku: the story of Atiku Abubakar. Africana Legacy Press.
  9. "How a pastor I trusted defrauded me of N918 million". 2017.
  10. Josiah Emerole (2002). Amazing crusade: media portrait of the Titi Atiku Abubakar war against human trafficking. Vol. 1. s.n. (Women Trafficking and Child Labour Eradication Foundation).
  11. "Hajiya Titi Abubakar: Working to restore human dignity". www.weekend.peoplesdailyng.com. People's Daily. Archived from the original on 23 August 2017. Retrieved 16 June 2017.
  12. "Hajiya Titi Abubakar: Working to restore human dignity". www.weekend.peoplesdailyng.com. People's Daily. Archived from the original on 23 August 2017. Retrieved 16 June 2017.
  13. Sufuyan, Ojeifo. "My battle to marry Atiku Titi Abubakar - OnlineNigeria.com". nm.onlinenigeria.com. Online Nigeria. Retrieved 16 June2017.
  14. "Nigeria: Titi Atiku, 16 Others Bag Women Awards". This Day (Lagos). All Africa. 29 May 2002. Retrieved 16 June 2017.
  15. Ojoma, Akor (28 June 2010). "Nigeria: Titi Atiku, Osaze, 73 Others Win d'Linga Award". Daily Trust (Abuja). All Africa. Retrieved 16 June 2017.
  16. "African Books Collective: Educating the Nigerian Child". www.africanbookscollective.com. African Book Collective. Retrieved 16 June 2017.
  17. Atiku-Abubakar, Amina Titi (2005). Educating the Nigerian Child (Paperback) by Amina Titi Atiku Abubakar, Chris Chirwa: Spectrum Books Ltd ,Nigeria, Nigeria 9789780294229 Paperback - The Book Depository (in Turanci). Nigeria: Spectrum Books Ltd ,Nigeria. ISBN 9780294228. Retrieved 16 June 2017.
  18. Atiku Abubakar, Amina Titi (2001). Empower law to fight child slavery (in English). Nigeria: WOTCLEF.CS1 maint: unrecognized language (link)
  19. Atiku Abubakar, Amina Titi; Fagbohungbe, Tunde; Fabiyi, Sayo. Let us celebrate humanity: a collected speeches on women's right and human trafficking, volume II (in English). WOTCLEF. Retrieved 16 June 2017.CS1 maint: unrecognized language (link)