Umaru Musa Yar'Adua

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Umaru Yar'Adua)
Umaru Musa Yar'Adua a wani babban taro
Umaru Musa Yar'Adua a wani taro

Umar Musa Yar'adua G.C.F.R (an haife shi a ranar 16 ga watan Agustan shekara ta alif ɗari tara da hamsin da ɗaya, 1951) haifaffen cikin birnin Katsina ne dake arewacin Najeriya.[1] [2] Mahaifinsa ya kasance tsohon ministan birnin Lagos na farko a jamhuriya ta farko, kuma kafin rasuwar sa shine Matawallen Katsina, sarautar da shi marigayin Umaru Musa Ƴar'adua ya gada daga wajen mahaifinsa wato Musa Yar'adua.[3] Akwai dan uwansa (babban yayan sa) watau Shehu Musa Ƴar'adua, wanda shima shahararren ɗan siyasa ne a ƙasar Najeriya; kuma shiya kafa jam'iyyar 'PDM' (People's Democratic Movement), Shehu Musa Ƴar'adua ya rasu a gidan yari a shekarar alif ɗari tara da chasa'in da tara, 1997.[1].

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Shugaba Umaru Musa a wani babban taro a Abuja

Marigayi Umaru Musa Ƴar'aduwa ya fara makarantar Firamarensa ne a Rafukka a shekara ta alif ɗari tara da hamsin da takwas, 1958, kafin a mayar da shi makarantar sakandare ta kwana dake ƙaramar hukumar Dutsin-ma a shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyu, 1962. Ya kuma halarci kwalejin gwamnati dake Keffi daga shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyar, 1965 zuwa shekara ta alif ɗari tara da sittin da tara, 1969. Sai ya wuce kwalejin Barewa a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da ɗaya, 1971, inda ya samu takardar shedar karatunsa ta HSC.[3]

Tsohon shugaban ƙasa Umaru Ƴar'aduwa ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga shekara ta alif ɗari tara da saba'in da biyu, 1972 zuwa shekara ta alif ɗari tara da saba'in da takwas, 1978 inda ya samu takardar shedar Digirinsa akan kimiyyar haɗa sinadirai (Chemistry) da Koyarwa, kafin ya koma domin samun babban digiri duk dai akan kimiyyar hada sinadarai Chemistry. Marigayin yayi bautar ƙasarsa ne a Jihar Lagos inda ya koyar a makarantar Holy Trinity daga shekarar alif ɗari tara da saba'in da biyar 1975 zuwa shekara ta alif ɗari tara da saba'in da shida, 1976.[3]

Bayan da ya kammala aikin yiwa kasa hidima ya fara aikin koyarwa kadan-kadan a kwalejin share fagen shiga jami'a da ake kira CAST da ke Zaria a tsakanin shekara ta 1976 zuwa shekara ta 1979. A shekara ta 1983, marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'aduwa ya bar aikin koyarwa ya fara aiki da Gonar Sambo Farms a Funtua, da ke a jihar Katsina inda ya zama GM daga shekarata 1983 zuwa shekara ta 1989.

Daga shekara ta 1984 bayan da Sojoji suka yi juyin mulki, an kira Malam Umaru Musa 'Yar'aduwa domin zama wakili a hukumar gudanarwar kanfanoni da hukumomin gwamnati da dama da suka hada da hukumar samar da kayan no noma, kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar katsina, Bankin Habib, Hamada Carpets, Madara Limited da kuma kanfanin buga Jaridu da Mujallar The Nation, da ke Kaduna wanda kuma wansa Marigayi Janar Shehu Musa 'Yar'aduwa ya mallaka.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A lokacin da marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'aduwa ya shiga siyasa, ya samu sabani da mahaifinsa, wanda a wancan lokacin yake mataimakin shugaban Jam'iyar NPN, inda shi kuma ya zama wakili a jam'iyar PRP ta Malam Aminu Kano mai adawa da NPN. A lokacin da Janar Badamasi Babangida ya kada gangar siyasa ya zama sakataren jam'iyar SDP a jihar ta Katsina kuma dan takararta na gwamna, amma kuma dan takarar jam'iyar NRC na wancan lokacin Malam Saidu Barda ya kada shi a zaben. To sai dai duk da haka bai hakura ba inda a shekara ta 1999, lokacin da aka koma mulkin damokaradiyya, Malam Umaru Musa 'Yar'aduwa ya tsaya takarar mukamin gwamnan jihar ta Katsina kuma ya samu nasarar cin zabe a karkashin jam'iyyar PDP. Haka kuma ya sake samun nasara a zaben da aka yi a shekara ta 2003 duk dai a jam'iyyarsa ta PDP.

lokacin da Umaru Musa Yar'adua ya zama shugaban kasa

A shekarar 2007, Umaru Musa 'Yar'aduwa ya zama dan takarar mukamin shugaban kasa na Jam'iyar PDP bayan ya samu taimakon tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo inda ya zama shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, wannan ya bashi daman sanya rigar siyasa na koli a shekarar. [4]

Umaru Musa Yar'adua a wani taro

To sai dai rashin lafiya da tsohon shugaban ya yi fama da ita, ta sanya bai samu sukunin gudanar da harkokin mulkinsa kamar yadda ya yi fata ba, musamman kudirorinsa guda bakwai (7) daya tsara na ciyar da kasar ta Najeriya gaba kafin nan da karni na 2020.[5]

Kudurorinsa guda 7 (7 point Agenda)

A lokacin da marigayi Umaru Musa ya zama shugaban kasar Najeriya ya zayyana kudurorinsa na mulki kyawawa guda bakwai (7) da yake so ya cimmawa a matsayinsa na shugaba kafin shekara ta 2020[1], wanda aka sanyawa laqabi da 'mahangar shekarata 2020' watau (Vision 2020),[6]wanda suka hada da;

 1. Samar da isasshiyar wutar lantarki a ko ina a fadin kasar.
 2. Samar da isasshiyan lafiyayyen abinci a kowane sako da loko dake fadin kasar.
 3. Samar da arziki a kasa musamman a harkokin noma, kere-kere da kuma haqe-haqen albarkatun kasa da karafa da kuma sarrafa su a cikin kasar ta Najeriya.
 4. Inganta fannin harkokin sufuri ta hanyar gyara hanyoyin da suka samu matsala da kuma ababan hawa zuwa na zamani.
 5. inganta fannin filaye da samar da muhalli da filayen noma, da na manyan masana'antu ga yan Nageria.
 6. Samar da tsaro - acewarsa tabbatar da tsaro wajibi ne don cigaban kasa, domin wanzuwar zaman lafiya kadai kan bunqasa harkokin kasuwancin kasa baki daya da kuma tabbatar da adalci tsakanin talakawa da Gwamnatin Tarayya.
 7. Ilimi - zai inganta harkokin ilimi a kasa wacce zata riski tsarin ilimi na duniya. Wanda za'a iya cimma wannan buri ne kadai ta hanyar yin gyara managarci a fannin ilimi a Najeriya.

Rasuwar sa[gyara sashe | gyara masomin]

Marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'adua ya rasu ne a sanadiyar rashin lafiya da ya dade yana fama da ita, ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekara ta 2010 a fadar gwamnati da ke Abuja watanni biyu bayan komowarsa gida daga kasar Saudiya inda yake jinya.

Iyalin sa[gyara sashe | gyara masomin]

Turai 'Yar'adua ita ce uwar gidan Umar Musa 'Yar'Adua

Umaru Musa ya rasu ne ya bar mahaifiyarsa da 'yan'uwansa da matan aure guda biyu Hajiya Turai Yar'Adua tare da 'ya'ya bakwai da ya haifa da ita da suka hada da mata biyar, Maza biyu. Haka kuma yana da wasu 'ya'ya biyu Maza da matarsa ta biyu Hajiya Hauwa Umar Radda. ta haifa. [7] [8]

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

 • Adeniyi, Olusegun, 1965- (2011). Power, politics and death : a front-row account of Nigeria under the late President Umaru Musa Yar'Aduwa. Lagos, Nigeria: Prestige. ISBN 978-978-50726-0-0.
 • Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. 1.0 1.1 1.2 "Umaru Musa Yar'Adua | Profile | Africa Confidential". www.africa-confidential.com. Retrieved 2021-04-10.
 2. "Umaru Yaradua | Encyclopedia.com". www.encyclopedia.com. Retrieved 2021-04-10.
 3. 3.0 3.1 3.2 https://www.bbc.com/hausa/mobile/news/2010/09/100922_umaru_yaradua.shtml
 4. Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. p. 138 ISBN 978-978-906-469-4.
 5. Lagos, Rasheedat Ola in. "Yar'Adua's Seven Point Agenda: any hope for the Nigerian people?". In Defence of Marxism. Retrieved 2021-04-09.
 6. "Vision 2020, Nigeria - Google Search". www.google.com. Retrieved 2021-04-09
 7. https://www.britannica.com/biography/Umaru-Musa-YarAdua
 8. https://www.bbc.com/hausa/news/2010/09/100922_umaru_yaradua