Tarayyar Amurka (da Turanci United States of America) ko Amurka ko Amurika ko Amerika ko Haɗin kan Jahohin Amurka, jamhoriya ce da ta hada jihohi guda 50 da fadar kasa da manya manyan kasashe masu cin gashin kai guda biyar. Akwai kuma wasu yankunan marasa yanci guda 11, da kuma wasu kananan tsibirai guda 9. Amerika na da fadin kasa da yakai sukwaya mil miliyan 3.8 (wato kilo mita 9.8), da kuma adadin mutane miliyan 325, kasar amurka itace ƙasa ta uku ko ta hudu wajen yawan fadin kasa kuma ta uku wajen yawan mutane. Birnin tarayya shine Washinton Gundumar Kolombiya, birni mafi yawan jama'a da girma kuma shine New York. Jihar Alaska itace a gefen kwanar arewa maso yamma na arewacin Amurka, iyaka da kasar Kanada daga gabas. Rushewar Tarayyar Soviets yayi sanadiyyar zaman Amurka ƙasa mafi ƙarfin iko a duniya kuma Amurka itace ƙasar da ta gabatar da mulkin demokaradiyya a kasashen duniya da dama.
Mutanen Paleo-Indian ne suka yi hijira daga Rasha zuwa Arewacin Amurka akalla shekaru 15,000 da suka wuce. Mulkin mallakar turawan Birtaniya ya fara ne daga karni na 16. juyin juya halin Amurka ya fara ne a shekara ta 1776. An kawo karshen yaƙin ne a shekara ta 1783 bayan kafuwar Tarayyar Amurka. Amurka na amfani da Kundin tsarin mulki na shekara ta 1788, wanda aka sama suna The bill of right. Kasar Amurka itace kasa mafi karfin iko a Duniya tun bayan rushewar Taraiyar Soviets. Kuma itace kasar da ta gabatar da mulkin demokaradiyya a wasu daga ƙasashen duniya.