Jump to content

Kungiyar Agaji Ta Red Cross Ta Duniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kungiyar Agaji Ta Red Cross Ta Duniya

Neutrality, Independence, Impartiality, Humanity, Universality, Unity, Voluntary Service
Bayanai
Gajeren suna ICRC da CICR
Iri international non-governmental organization (en) Fassara
Ƙasa Switzerland
Aiki
Mamba na Memoriav (en) Fassara da DLM Forum (en) Fassara
Bangare na Kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta kasa da kasa
Ma'aikata 25 (2016)
Mulki
Shugaba Mirjana Spoljaric Egger (en) Fassara
Shugaba Pierre Krähenbühl (en) Fassara
Hedkwata Geneva (en) Fassara da Villa Moynier (en) Fassara
Tsari a hukumance association (en) Fassara
Mamallaki Kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta kasa da kasa
Financial data
Budget (en) Fassara 1,900,000,000 Fr (2019)
Tarihi
Ƙirƙira 17 ga Faburairu, 1863
Wanda ya samar
Awards received

icrc.org


Comité international de la croix rouge
Henri Dunant (1828-1919)

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta duniya ƙungiya ce ta agaji da gudanar da ayyukan jin kai mai zaman kanta wato ba ta gwamnati ba ce, helkwatarta kuwa tana a birnin Geneva na ƙasar habasha ne.

Tsohon wurin Hedikwatar Hukumar dake a birnin Geneva

Duk da cewa an kafa ƙungiyar agaji ta Red Cross din ne 1863 to amma tunanin kafa ƙungiyar ya faro ne a shekarar 1859 lokacin da dan kasuwan nan kuma mai gudanar da ayyukan jin kai da zamantakewa dan kasar Switzerland wato Jean Henry Dunant wanda daga baya aka fi sani da Henry Dunant, ya irin ababe masu tada hankali da suka faru a lokacin yaƙin Solferino a kasar Italiya na yanzu, inda dubban mutane suka mutu wasu da dama kuma suka sami raunuka, a bangare guda kuma wadanda suka sami raunukan sun sami samun magani da kulawar da suke bukata. To bayan dawowarsa gida Geneva ne ya yi kira da a kafa ƙungiyar agaji don ba da taimako ga wadanda suka jikkata a fagen yaki. Hakan ne ya sanya aka kafa kwamitin Red Cross a shekarar 1863.

To amma a wancan lokacin kusan ƙasashe daban-daban suna da nasu ƙungiyar ta Red Cross ko kuma ta agaji, to amma an kafa asalin ƙungiyar Red Cross din ta ƙasa da ƙasa ne a shekarar 1919 bayan yakin duniya na farko lokacin da shugaban kwamitin Red Cross na Amurka a lokacin yaki Henry Davison ya ba da shawarar kafa wata harɗaɗɗiyar ƙungiya ta ƙungiyoyin Red Cross na ƙasashe daban daban don jagorantara kan ayyukan ba da agaji a duk fadin duniya. A farkon shekarar 1919, an kira taron ƙasa da ƙasa kan harkokin kiwon lafiya a birnin Cannes na kasar Faransa. A yayin wannan taron an tsai da shawarar cewa dole ne a kafa hadaddiyar kungiya ta ƙungiyoyin Red Cross ta ƙasashe daban daban gaba daya don kara inganta nasarorin da ƙungiyoyin agaji na Red Cross na ƙasashe daban daban suka cimma, an dai ba wa wannan ƙungiya sunan League of Red Cross Societies. Daga baya, saboda shigowar ƙungiyoyin Red Crescent na ƙasashen Larabawa da kuma Ƙaruwarsu, ƙungiyar Red Cross ta kira babban taro na uku a watan Oktoba na shekarar 1983, inda aka yanke shawarar sake sunan kungiyar zuwa International Red Cross and Red Crescent Societies (ƙungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta duniya).

Ko shakka babu kafa wannan kungiyar ta Red Cross da Red Crescent tana da alaka da lamari na addini. Saboda kuwa kamar yadda muka ce sakamakon shigowar ƙasashen musulmi cikin wannan lamari na ba da agaji sosai ya sanya wasu suna ganin bai kamata su ci gaba da amfani da cross ba wanda a bangare guda yana a matsayin alama ce ta mabiya addinin kirista wato alamar da suke amfani da ita don nuna giciye Annabi Isa al-Masihu (a.s) da aka yi don haka wasu suka fara tunanin su ma musulmi su ƙirƙiro wata alamar ta su a wannan bangaren. To da yake ana amfani da alama ta wata a matsayin abin da ke nuni da Musulunci wanda hatta ko a hasumiyar masallatai a kan sa hakan don haka sai suka yi amfani da wannan alama ta wata a matsayin alamarsu. Don haka ne alamar wannan kungiya ta zamanto cross da kuma alamar wata (ko kuma crescent a turance.

An amince da wannan alama ta crescent ne kuwa a hukumance a shekarar 1929 kuma ya zuwa yanzu kimanin kasashe 33 ne suka amince da hakan. Duk da cewa an fara amfani da wannan alama ce tun a shekarar 1877-1878 lokacin rikici da yakin da aka yi tsakanin kasashen Rasha da Turkiyya.

Manufar ita ma wannan kungiya ta Red Cross da Red Crescent ita ce ba da agaji da jin kai ga wadanda suka sami raunuka a lokacin yaƙi har ila yau da kuma batun kiyaye sulhu da zaman lafiya.

Wani lamari kuma da ya ke da kyau a fahimta shi ne cewa kasashe biyar ne ake daukansu a matsayin wadanda suka kafa ita wannan kungiyar ta Red Cross, su ne kuwa: Birtaniya, Faransa, Italiya, Japan da kuma Amurka. To sai dai daga baya sun ta karuwa lokacin da kungiyoyin red cross da na red crescent na kasashe daban-daban suka ta shigowa cikin uwar ƙungiya inda ya zuwa yanzu akwai sama da ƙasashe 180 a cikin ƙungiyar. A takaice dai ana iya cewa kusan dukkanin ƙasashen duniya suna da ko dai k kungiyar agaji ta Red Cross ko kuma ta Red Crescent

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Ayyukan ƙungiyar

[gyara sashe | gyara masomin]

Ma`aikatan kungiyar

[gyara sashe | gyara masomin]