Siyasa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Siyaya hanya ce da mutane ke bi wajen rayuwa a hade ko tare ko kungiyance cikin manufa daya. Siyasa na nufin hada yarjejeniya tsakanin mutane domin su zauna tare dukda mabambantan kabilu da addinai, barane da ma kasashe. A manyan kashashe mutane da dama kan dauki dogon lokaci wajen tsayar da yarjejeniyar siyasa. Wadannan mutane su ske kira da Yansiyasa. Yansiyasa da kuma wadansu mutane kan hadu domin samar da Gwamnati da tafiyar da ita. Karatun tafiyar da gwamnati a jami'a ana kiranshi da Ilimin siyasa (turanci Political Science, ko Public Administration ko Political Studies).

A ma'anar koyaushr Siyasa na nufin hanyar da kasashe ke bi domin aiwatar da mulki ko gwamnati, da kuma hanyar da gwamnatoci ke bi wajen aiwatar da dokoki. Ana kuma yin siyasa a wasu guraren kamar Kamfanoni, kungiyoyi, makarantu, masallatai da majami'u.