Saidu Barda
Saidu Barda | |||
---|---|---|---|
ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993 ← John Madaki - Emmanuel Acholonu → | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Babban taron jam'iyyar Republican |
Alhaji Sa'idu Barda ɗan siyasar Najeriya ne wanda aka zaɓe shi a dandalin jam'iyyar Republican National Republican Convention (NRC) a matsayin gwamnan jihar Katsina, Nigeria, mai rike da muƙami tsakanin watan Janairu shekarar (1992) zuwa Nuwamban shekara ta (1993) a lokacin jamhuriya ta uku ta Najeriya. Ya ci gaba da taka rawar gani a siyasa a jamhuriya ta hudu ta Najeriya.[1]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Barda ya kammala aikin ginin masakar fulawa a Katsina, wanda aka fara shi a shekarar 1981, amma daga baya aka yi watsi da shi. A cikin watan Yuni a shekara ta1993, Barda ya kafa wani kwamiti a kan Gyaran Ilimi "don duba lalacewar ilimi a makarantu da kuma samar da mafita." Ya kuma aza harsashin ginin Othman Dan Fodio Institute, wanda aka yi niyyar ta zama jami’ar Musulunci ta farko a Najeriya amma daga baya aka yi watsi da ita.[2]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Gwamnan jihar Katsina
[gyara sashe | gyara masomin]A zaɓen gwamnan jihar Katsina a watan Disamba a shekara ta (1991) Barda ya doke Umaru Yar'Adua, ɗan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP). Daga baya 'Yar'Adua ya ci gaba da zama shugaban kasa a watan Afrilun shekara ta (2007).[3] Kanin Umaru Janar Shehu 'Yar'aduwa, wanda a lokacin fitaccen ɗan siyasa ne da ke da muradin zama shugaban ƙasa, ya kasa bayar da cikakken goyon bayansa ga neman Umaru. Barda ya samu tagomashi daga shugaban ƙasa na mulkin soja a lokacin, Janar Ibrahim Babangida.[4]
Barda ya goyi bayan soke zaɓen da Babangida ya yi a ranar 12 ga watan Yunin shekarar (1993) na zaben MKO Abiola a matsayin shugaban ƙasa, yana mai cewa "jini zai rika zubowa a sikelin da ba a taba ganin irinsa ba" idan har za a sauya soke zaɓen[5] Gwagwarmayar siyasar da ta biyo bayan sokewar ta kai ga juyin mulkin da Janar Sani Abacha ya yi a watan Nuwamba a shekara ta (1993) inda aka kori dukkan zaɓaɓɓun gwamnoni.
Rawar gani a siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Barda ya taka rawar gani a siyasa a jamhuriya ta hudu ta Najeriya, inda ya zama shugaban jam'iyyar United Nigeria People's Party (UNPP). A watan Janairun shekara ta (2003) a matsayinsa na shugaban babban taron jam’iyyar UNPP, Barda ya bayyana cewa Sanata Jim Ifeanyichukwu Nwobodo ne zai zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen shugaban kasa na Afrilu a shekara ta (2003).[6] A watan Mayun shekarar (2003) Barda ya kasance memba a kungiyar shawarwari ta Arewa, ƙungiyar shugabannin siyasar Arewa. A watan Oktoban shekara ta (2009) Barda yana wani taro inda tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Muhammadu Buhari ya sanar da kafa sabuwar kawancen siyasa, wato National Democratic Movement.[7][8] A shekara ta (2010) Barda ya kasance mataimakin shugaban kungiyar tuntuba ta Arewa.[9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved April 30, 2010.
- ↑ Renée Ilene Pittin (2002). Women and work in northern Nigeria: transcending boundaries. Palgrave Macmillan. p. 37,356, 365. ISBN 0-333-98456-0.
- ↑ TIMOTHY OLA (March 9, 2010). "Missing President: Is Turai really to blame?". Daily Sun. Retrieved April 30, 2010.[permanent dead link]
- ↑ SHEHU USMAN. "Obasanjo tears Yar'Adua's family apart". National Daily News. Retrieved April 30, 2010.
- ↑ .Olatunji Dare (August 25, 2009). "Abiola: A legacy traduced". The Nation. Archived from the original on June 21, 2010. Retrieved April 30, 2010.
- ↑ Chukwudi Nwabuko and Chuks Okocha (January 12, 2003). "Nwobodo, Nwachukwu Pick Presidential Tickets". ThisDay. Archived from the original on January 17, 2005. Retrieved April 30, 2010.
- ↑ Ali M. Ali; Agaju Madugba; Jare Ilelaboye; Lillian Okenwa; Tokunbo Adedoja (May 1, 2003). "Buhari Gives Conditions for Going to Court: Arewa divided over fresh polls". ThisDay. Archived from the original on April 1, 2012. Retrieved April 30, 2010.
- ↑ Yusuf Alli (October 29, 2009). "We won't give up on Nigeria, says Buhari". The Nation. Archived from the original on October 31, 2009. Retrieved April 30, 2010.
- ↑ Idris Salisu (April 4, 2010). "Zamfara Workers Threaten Govt". Daily Independent. Retrieved April 30, 2010.