Jump to content

Samaila Bature Chamah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Samaila Bature Chamah
Gwamnan Jihar Kebbi

ga Augusta, 1998 - Mayu 1999
John Ubah - Adamu Aliero
gwamnan jihar Katsina

22 ga Augusta, 1996 - ga Augusta, 1998
Emmanuel Acholonu - Joseph Akaagerger
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 15 ga Janairu, 2007
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar

Birgediya Janar Samuel Bature Chamah: ya kasance shugaban jihar Katsina a Najeriya daga watan Agusta, 1996 zuwa Agustan shekarar 1998 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha, sannan ya yi mulkin jihar Kebbi daga watan Agusta 1998 zuwa Mayu 1999 a lokacin gwamnatin riƙon ƙwarya ta Janar Abdulsalami Abubakar, ya miƙa mulki zuwa ga zaɓaɓɓen gwamnan farar hula Adamu Aliero a ranar 29 ga watan Mayun, 1999.[1]

Ya zama Manajan Darakta / Shugaban Kamfanin (Falpas Ventures Limited) kuma Wakilin Mujallar "My Africa" a Najeriya.

Dukkan gwamnonin soja da masu mulki a gwamnatocin Babangida, Abacha da Abubakar, gwamnatin tarayya ta yi musu ritaya a watan Yunin 1999, ciki har da Birgediya-Janar Samuel Chamah.[2]

Birgediya Janar (Deacon) Samaila Bature Chamah ya rasu a gidan wasan Golf na IBB da ke Abuja a shekarar 2007.[3]

  1. "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-01-18.
  2. "OBASANJO HIRES & FIRES". NDM DEMOCRACY WATCH 1999/03. July 1, 1999. Retrieved 2010-01-18.
  3. "Transition!" (PDF). My Africa Magazine. 2007. Retrieved 2010-01-18.