Rabi'u Musa Kwankwaso

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Rabi'u Musa Kwankwaso
Dr Rabiu Musa Kwankwaso.jpg
gwamnan jihar Kano

Mayu 2011 - Mayu 2015
Ibrahim Shekarau - Abdullahi Umar Ganduje
Minister of Defence of Nigeria (en) Fassara

ga Yuli, 2003 - 2007
Theophilus Danjuma (en) Fassara - Thomas Aguiyi-Ironsi (en) Fassara
gwamnan jihar Kano

Mayu 1999 - Mayu 2003
Aminu Isa Kontagora - Ibrahim Shekarau
member of the House of Representatives of Nigeria (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Madobi, 21 Oktoba 1956 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Middlesex University (en) Fassara
Loughborough University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
kwankwaso.com


Muhammad Rabi'u Musa Kwankwaso wanda akafi sani da Rabi'u Kwankwaso dan siyasar Najeriya ne. Ya rike matsayin gwamna a jahar Kano har sau biyu wato shekarun 1999-2003 da kuma 2011-2015. Shine gwamnan farko na jahar Kano a jamhuriya ta hudu kuma ya ci zabe ne duka a karkashin jam'iyyar PDP kafin daga bisani ya canza jam'iyya ya koma jam'iyyar sa ta APC. A zaben 2003 kwankwaso yayi rashin nasara ne a hannun Ibrahim Shekarau. A watan Yuli ne na shekarar dai ta 2003 Olusegun Obasanjo ya nada shi matsayin ministan tsaron Najeriya, bayan samun rashin nasara da yayi a zaben.

A 2015 Kwankwaso yayi rashin nasara a hannun Shugaba Muhammadu Buhari a zaben fidda gwani na dantakarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, inda daga bisani sai ya canza sheka zuwa takarar kujerar Sanata da yake kai yanzu. A shekarar 2018 ya fice daga jam'iyyar APC inda ya sake komawa jam'iyyarsa ta PDP da niyyar yin takarar shugaban ƙasa sai dai yasha ƙasa a hannun abokin karawarsa Atiku Abubakar wanda ya lashe zaɓen fidda gwani wanda aka gudanar Fatakwal.u

Tarihin sa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a ranar 21 Oktoba 1956 a kauyen Kwankwaso dake karamar hukumar Madobi ta jihar Kano[1]. Ya halarci makarantar firamaren gwamnati ta garin Kwankwaso, sai Makarantar sakandardn kwana ta Gwarzo sai yaje makarantar kere-kere ta garin [[Wudil] da Makarantar fasaha a Kano kafin daga bisani ya halarci makarantar Kaduna Polytechnic a inda ya samu shaidun difiloma guda biyu wato National Diploma da Higher National Diploma yayi kuma digirinsa na farko a birtaniya Middlesex Polytechnich (1982-1983)da kuma Loughbrough University of technology (1983-1985)inda yayi babban digirinsa wato Masters Digree[2]. Dukan yawancin makarantun da Kwankwaso yayi karatu shi ne yake rike mukamin shugaban daliban makarantun kuma anma taba zabarsa shugaban kungiyar dalibai na jahar Kano

[3]

[4]

Fara tashensa[gyara sashe | Gyara masomin]

Rabiu musa kwankwaso da kuma rochas okoracha

Kwankwaso ya fara aiki a 1975 inda ya fara aiki da hukumar ruwa ta jahar kano wato Kano Satae Water Resources and Engineering Construction Agency wato WRECA yayi aiki na tsawon shekaru 17 a bangarori daban da ban inda har ya zama shugaban ma'aikatar. A shekarar 1992 aka zabi Kwankwaso danmajalisar wakilai ta taraiyar Najeriya mai wakiltar karamar hukumar Madobi. Kuma shine ya zama mataimakin kakakin majalisar a karkashin jamiyyar SDP A wani taro da akayi na gyaran kundin mulkin kasa an zabi kwankwaso amatsayin wakilin jahar Kano. Ya shiga jam'iyyar PDP a 1998

Zamansa Gwamna[gyara sashe | Gyara masomin]

An zabi Rabiu Kwankwaso gwamna a jahar Kano a 1999 karkashin jam'iyyar PDP har zuwa 2003 inda yayi rashin nasara a hannun Ibrahim Shekarau. Kasantuwar sa gwamna a jahar Kano ya zama wani babban al'amari da ya faru a jahar kano, kamar yadda Kwankwaso ya ke nuna cikakken goyon baya ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Tare da yadda ya kirkiro wasu tsarurruka na musamman a gwamnatin sa da kuma yadda rashin nasarar sa ta kasance a hanun tsohon gwamna Ibrahim Shekarau. Sai dai kuma Kwankwaso ya sake nuna sha'awar tsayawa takara a zaben 2007 amma hakan bata yiyuba sakamakon samunshi da wasu laifuffuka da gwamnatin Ibrahim Shekarau ta jam'iyyar ANPP tayi. Sai kwankwaso ya kawo wanda zai yi takarar a jam'iyyar PDP wato Ahmad Garba Bichi.

Taron Kwankwasiyya kenan, a jihar kano
yan kwankwasiyya a jihar kano
Yadda kwankwaso ya maida kofar nasarawa kenan ta zamani

Kwankwaso baiyi kasa a gwiwa ba wajen sake tsayawa takar gwamna a zaben 2011 kuma yayi nasarar kayar da jam'iyyar ANPP ta Salihu Sagir Takai. Anyi zaben ranar 26 ga Afrilu 2011 kuma ya kama rantsuwar aiki a ranar 29 Mayu 2011. Kwankwaso na daga cikin Gwanoni guda biyar wato G-7 wadanda suka fita daga jam'iyyar su ta PDP tare da sauya sheka zuwa APC.

Akidar siyasar Rabiu Musa Kwankwaso Duba Kwankwasiyya

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. https://www.africa-confidential.com/profile/id/3939/Rabiu_Kwankwaso
  2. https://blerf.org/index.php/biography/kwankwaso-rabiu-musa/
  3. https://blerf.org/index.php/biography/kwankwaso-rabiu-musa/
  4. https://buzznigeria.com/facts-rabiu-kwankwaso/