Jump to content

Abubakar Rimi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abubakar Rimi
gwamnan jihar Kano

Oktoba 1979 - Mayu 1983
Ishaya Shekari - Abdu Dawakin Tofa
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

Rayuwa
Haihuwa Sumaila, 1940
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Kano, 4 ga Afirilu, 2010
Karatu
Makaranta University of London (en) Fassara
Government College, Birnin Kudu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi (an haife shi ranar 4 ga watan Afrilu, 1940)[1] ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya yi Gwamnan Jihar Kano a lokacin Jamhuriya ta Biyu ta Najeriya. Ya kuma yi aiki a matsayin Ministan Sadarwa na Tarayya daga shekara ta alif ɗari tara da casa'in da uku (1993) zuwa shekara ta alif ɗari tara da casa'in da takwas (1998) a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.

Farkon Rayuwa, Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Alhaji Abubakar Rimi an haife shi a shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in (1940) a kauyen Rimi na Sumaila tsohuwar jihar Kano, Najeriya. A farkon shekarun 1960, ya halarci kwas na malanta a makarantar Gudanarwa da ke Zariya. Ya sami Takaddar Shaida ta ilimi daga Jami'ar London. A shekarar 1972, ya kammala difloma kan harkokin kasa da kasa a cibiyar kula da harkokin duniya ta London, sannan daga baya ya samu digiri na biyu a fannin hulɗa da kasashen duniya.[2] Ya yi aiki a matsayin malami a Cibiyar Horar da Malamai a Sokoto, sannan daga baya ya zama Sakataren Gudanarwa a Cibiyar Kula da Harkokin Ƙasa da Ƙasa ta Najeriya.[3]

Farkon aiki da siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Rimi ya kasance dan takara mai zaman kansa a zaben majalisar tarayya na mazabar Sumaila a shekara ta 1964 yayin da Musa Sa'id Abubakar ya kasance ɗan takarar majalisar tarayya na NEPU na mazabar Sumaila sun fafata da Alhaji Inuwa Wada na NPC amma duk sun janye wa Alhaji Inuwa Wada lokacin da aka ɗaure su. Ya kasance memba na Majalisar Tsarin Mulki shekara ta (1977–1978). A watan Disamba shekara ta 1978, an zabe shi mataimakin sakatare na kasa na jam’iyyar PRP a babban taron jam’iyyar na farko a Legas .Ya kasance dan takarar PRP a zaben shekara ta 1979. An zaɓi Abubakar Rimi a matsayin gwamnan tsohuwar jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PRP a lokacin Jamhuriya ta biyu ta Najeriya, muƙamin da ya rike daga watan Oktoba shekara ta 1979 ,Ana kiran majalisar ministocinsa da "Dukkanin Ministocin Digiri". An nada Alhaji Sule Hamma a matsayin Sakataren Gwamnati (SSG), Alhaji Abdullahi Aliyu Sumaila shi ne Sakataren Majalisar Zartarwa da Babban Sakatare na Gwamna, (PS ga Gwamna) daga baya ya zama Manajan Kamfen din Rimi a zaɓen shekara ta 1983, Tijjani Indabawa shi ne Sakatare mai lura da harkokin cikin gida na Gwamna (PPS ga Gwamna) da Sully Abu shi ne Sakataren Yada Labarai na Gwamnan.  Ya kasance mai sassaucin ra'ayi da tasiri, da kuma karfafa mata su fita daga Kulle a Gida. Ya kawar da haraji (harajin mutum) da jangali (harajin shanu), kayayyakin tarihi na lokacin mulkin mallaka lokacin da Turawan mulkin mallaka na Birtaniyya ke mulkin ta masarautu a Arewa. A shekara( 1980), ya ayyana ranar ma'aikata ta shekara-shekara. Dakatarwar da ya yiwa Sarkin Kano ya haifar da tarzoma a watan Yulin shekara ta 1981, sannan aka kashe mai ba Rimi shawara kan harkokin siyasa Dr. Bala Mohammed. A lokacin ofisoshin Jaridun Triumph, Rediyon Kano da ma'aikatu da yawa sun zone.

A watan Mayu shekara ta 1983, Rimi ya yi rashin jituwa tare da malaminsa Aminu Kano kuma suka sauya sheka daga Jam’iyyar Redemption Party (PRP) zuwa Jam’iyyar Jama’ar Najeriya (NPP) a shirye-shiryen zaben shekara ta 1983. Ya yi murabus daga mukaminsa sannan mataimakinsa, Abdu Dawakin Tofa ya maye gurbinsa a matsayin gwamna.

Aiki daga baya[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta alif 1993, Rimi ya karbi aikinsa a matsayin Shugaban Bankin Noma da Hadin Kan Najeriya (NACB) a karkashin gwamnatin Janar Ibrahim Babangida . A lokacin sauya sheka zuwa Jamhuriya ta Uku ta Najeriya, Rimi ya kasance memba na tsakiyar-hagu Social Democratic Party (SDP) kuma yana daga cikin magoyan bayan farko na yunkurin (12 )ga Yuni da ke adawa da soke zaben MKO Abiola . Daga baya ya bar tafiyar( 12 )ga Yuni, kuma ya zama Ministan Sadarwa a karkashin gwamnatin Janar Sani Abacha .

Yana daya daga cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP. Ya kasance Shugaban kwamitin kudi na Jam’iyyar a lokacin da aka kafa ta sannan kuma daya daga cikin ‘yan takarar ta na shugaban kasa. An nada shi Shugaban Kamfanin Kula da Tsaro da Lantarki na Najeriya (NSPMC) a farkon lokacin mulkin Obasanjo a matsayin Shugaban farar hula. Daga baya ya koma Action Congress (AC), amma a shekara ta 2007 Rimi ya koma (PDP). A watan Disambar shekara ta 2008,ya yi kira ga Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, (INEC), Farfesa Maurice Iwu, da ya yi murabus daga mukaminsa, saboda kura-kuran da aka samu a zaben shugaban kasar da ya gabata. A watan Janairun shekara ta (2006 ),an kashe matarsa a gidansa. Kisansa na cikin wadanda ake tuhuma da kisan, amma daga baya aka sake shi saboda rashin hujja kuma har yanzu ana tsare da wani dan uwan nasa, Mustapha.

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar hudu 4 ga watan Afrilu, a shekara ta 2010, wasu ’yan fashi da makami suka kai wa Abubakar Rimi hari yayin da yake komawa gida jihar Kano daga jihar Bauchi. Kodayake bai samu rauni ba, da alama ya sha wahala sosai kuma ya mutu jim kadan bayan wannan ibtila'i da ya auku dashi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.bing.com/ck/a?!&&p=598dfa01fdf8c88cJmltdHM9MTcxOTAxNDQwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTIyMA&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Alhaji+Muhammadu+Abubakar+Rimi+biography&u=a1aHR0cHM6Ly9ibGVyZi5vcmcvaW5kZXgucGhwL2Jpb2dyYXBoeS9yaW1pLWFsaGFqaS1tb2hhbW1lZC1hYnViYWthci8&ntb=1
  2. "A Meeting of the Minds". BNW MagazineLondon institute of World Affairs,. 22 Jan 2005. Archived from the original on 2009-08-03. Retrieved 2009-09-16.CS1 maint: extra punctuation (link)
  3. "Mohammed Abubakar Rimi (1940–2010)". Guardian. 21 April 2010. Retrieved 2004-04-26. [dead link]