Ibrahim Shekarau
Ibrahim Shekarau | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023 ← Rabiu Kwankwaso District: Kano Central
Mayu 2003 - Mayu 2011 ← Rabiu Kwankwaso - Rabiu Kwankwaso → District: Kano Central
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Kano, 5 Nuwamba, 1955 (68 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Harshen uwa | Kanuri | ||||||
Ƴan uwa | |||||||
Abokiyar zama | Amina ibrahim shekarau | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello Jami'ar Bayero | ||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Kanuri | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa, anti-vaccine activist (en) da administrator (en) | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Musulunci | ||||||
Jam'iyar siyasa | New Nigeria Peoples Party (en) |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Malam Ibrahim Shekarau[1] tsohon Malami ne kuma ɗan siyasan Najeriya.[2] An haife shi a shekara ta alif ɗari tara da hamsin da biyar (1955) Miladiyya, a garin Kano, Arewacin Najeriya (a jahar Kano). Ya riƙe Ministan ilimin Najeriya daga shekara ta 2014 zuwa shekarar 2015.[3] Ya fara takarar Gwamnan jahar Kano a shekara ta 2003, wanda daga bisani ya zamto ya lashe zaɓen da aka yi a watan Janairun shekarar 2003. Ya yi mulkin jahar har sau biyu sanadiyyar sake samun nasarar da yayi a zaɓen shekarar 2011, wanda haka ne ya kuma sa ya jagoranci mulkin jahar na tsawon shekaru 8. kafin nan Rabi'u Kwankwaso wanda yayi gwamna kafinsa ya sake dawowa shi ma a karo na biyu inda ya yi takarar matsayin gwamnan jahar a karo na biyu. Kwankwason yayi nasarar lashe zaɓen shi ma inda ya yi mulkin jahar a karo na biyu daga watan Mayun shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.
Zargin cin kudin makamai
[gyara sashe | gyara masomin]A halin yanzu Ibrahim Shekarau ya na fuskantar shari'a a gaban kotu bisa zargin haɗa baki da karkatar da kuɗi kimanin miliyan ɗari tara da hamsin (950,000,000) wanda wani ɓangare ne daga kudaden da gwamnati ta ware a shekarar 2014 don yaki da masu tada ƙayar baya amma aka karkatar da su a wancan lokacin don yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ofishin mai bada shawara akan harkokin tsaro na manzan lokacin, wato Sambo Dasuki ya fitar. Amma sai dai har yanzu ba'a kama shi da laifin ba.