Kabiru Ibrahim Gaya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Â

Kabiru Ibrahim Gaya
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
District: Kano South
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

9 ga Yuni, 2015 -
District: Kano South
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Kano South
gwamnan jihar Kano

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Idris Garba - Muhammadu Abdullahi Wase
District: Kano South
Rayuwa
Cikakken suna Kabiru Ibrahim Gaya
Haihuwa 16 ga Yuni, 1952 (71 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Government College, Birnin Kudu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party
All Progressives Congress

Kabiru Ibrahim GayaAbout this soundKabiru Ibrahim Gaya  (an haife shi a ranar 16 ga watan Yunin shekara ta alif ɗari tara da hamsin da biyu(1952 ) miladiyya. ɗan siyasar Najeriya ne kuma masanin gine-gine wanda aka zaɓa a majalisar dattijan Najeriya a shekara ta 2007, wanda ya wakilci mazaɓar Kano ta Kudu a jihar Kano a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC). An zaɓi Kabiru Gaya mataimakin shugaban ƙungiyar 'yan majalisar tarayya (IPU) na Afirka a babban taron ƙungiyar karo na 135 a Geneva, Switzerland a Oktoba 2016.[1]

Ya halarci makarantar firamare ta Gaya daga shekara ta alif 1961 zuwa-1964 da Tsangaya Primary School inda ya gama makarantar firamari a shekarar 1968 babban dan uwansa a lokacin shi ne Shugaban Makarantar sannan kuma Abdullahi Aliyu Sumaila shi ne Mataimakin Shugaban makarantar wanda ya koyar da shi Lissafi a makarantar firamare. Ya halarci Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Birnin Kudu daga shekarar 1969 zuwa 1973 inda ya samu takardar shaidar Makarantar Afirka ta Yamma (WAEC) da Kwalejin Ilimin Kimiyya daga 1974-1975 inda ya sami IJMB. Ya sami digiri a fannin Gine-ginen daga Jami'ar Ahmadu Bello a 1977[2]

An zabi Kabiru Ibrahim Gaya a majalisar dattijan Kano ta Kudu a 2007. An kuma naɗa shi a kwamitocin kan gas, Gidaje da na kasashen waje, Jihohi & Kananan hukumomi, da Albarkatun Man Fetur da Ayyuka.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Nassnig.org. Retrieved 2020-01-07.
  2. https://allafrica.com/stories/200301130693.html
  3. https://allafrica.com/stories/200905250350.html?page=3