Jump to content

Sabo Bakin Zuwo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Sabo Bakin Zuwo
gwamnan jihar Kano

Oktoba 1983 - Disamba 1983
Abdu Dawakin Tofa - Hamza Abdullahi
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 31 Disamba 1934
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 15 ga Faburairu, 1989
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Aliyu Sabo Bakin Zuwo (December 31, 1934 – February 15, shekarar 1989) ɗan siyasan Najeriya ne na jam’iyyar PRP. Ya kasance Sanata a jamhuriya ta biyu ta Najeriya kuma an zabe shi gwamnan jihar Kano a watan Oktoba na shekarar 1983, inda yayi mulki na takaitaccen lokaci [1]Sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 31 ga watan Disamba 1983 wanda ya kawo Janar Mohammadu Buhari kan karagar mulki.

Asalin. Zuwo dai ana iya samo shi ne daga Barebari daga Daular Kanem-Bornu inda kakanninsa suka yi hijira zuwa Kano, inda aka haife shi kuma ya girma. Sunan mahaifinsa Abubakar, sunan kakansa Yusuf, sunan kakansa kuwa Ibrahim; Mahaifiyarsa Salamatu ‘yar Gunduwawa ce a karamar hukumar Minjibir .[2]

Ba shi da ilimin boko, amma ya ce ya yi "Malam Aminu Kano Political School, Sudawa, Kano." Zuwo ya shigar da kansa makaranta yana dan shekara sha shida. Sannan makarantar karatun manya ta firamare ta Shahuchi a shekarar 1950 zuwa 1954; Daga cikin malamansa akwai Maitama Sule . Zuwo ya kuma halartar makarantar Igbo Community School Sabon Gari Kano da kwas kan gudanar da harkokin kananan hukumomi a Cibiyar Gudanarwa ta Kongo Campus na Jami'ar Ahmadu Bello . Ya rasa damar samun ilimin yamma tun yana karami amma ya samu kadan daga ciki lokacin da ya girma.

A jamhuriya ta biyu, an ce Zuwo, ‘dan siyasa ne mai fafutuka, ta yi amfani da rediyo sosai fiye da kowane dan siyasa a Arewacin Najeriya. An zabe shi a Majalisar Dattawa a shekarata 1979, Zuwo ya daukar kudi fiye da kowane Sanata. [3]

Gwamnan Kano

[gyara sashe | gyara masomin]

A zaben gwamnan jihar Kano a shekarar 1983, ya doke tsohon gwamnan jihar, Abubakar Rimi, wanda ya yi murabus a farkon wannan shekarar ya koma jam'iyyar NPP. Daya daga cikin abin da Zuwo ya fara yi a matsayin gwamna shi ne cire duk wani sarki da Rimi ya nada. A wani abin farin ciki da ya yi, ya rufe gidan sinima na Palace da ke Kano, wanda ya zama wurin da samari ke shan kwaya ya mayar da shi asibiti.[4]

Cin hanci da rashawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Gwamnatin mulkin soja ta Janar Muhammadu Buhari ta kama shi a wani juyin mulki a ranar 31 ga Disamba 1983 . N3.4 miliyan akace an iske a cikin gidan Zuwo a lokacin da sabuwar gwamnatin mulkin soja ta yi bincike a kansa. A shekarar 1985, wata kotun soji ta musamman ta same shi da laifuffuka uku kuma ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 23 a gidan yari kan kowane laifi amma zaiyisu a lokaci guda.[5]

Ya rasu a shekara ta 1989. Kafin rasuwarsa ya hada kai da jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Janar Shehu Musa 'Yar'aduwa tare da wasu 'yan siyasar jihar Kano, kamar mataimakinsa Gwamna Wada Abubakar, Abdullahi Aliyu Sumaila, da Rabi'u Kwankwaso .

Samfuri:Governors of Kano StateSamfuri:State governors in the Nigerian Second Republic

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-18. Retrieved 2022-07-03.
  2. https://punchng.com/dad-never-spent-a-night-at-government-house-as-governor-bakin-zuwos-son/
  3. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named leader21ap
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-07-03. Retrieved 2022-07-03.
  5. https://quotes.ng/mobile/biography.php?title=sabo-bakin-zuwo&id=1667