Yusuf Maitama Sule

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yusuf Maitama Sule
Rayuwa
Haihuwa Kano, 1 Oktoba 1929
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Kairo, 3 ga Yuli, 2017
Yanayin mutuwa  (infectious disease (en) Fassara)
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Jam'iyyar National Party of Nigeria
Musa Daggash tare da Yusuf Maitama Sule lokacin da yake sa hannu akan yarjejeniyar man fetur

Alhaji Yusuf Maitama SuleAbout this soundYusuf Maitama Sule , Dan Masanin Kano An haifi Maitama a Shekarar alif 1929, a unguwar Yola, cikin garin Kano. Maitama shi ne na uku a jerin ‘ya’ya a gidansu, sauran yan'uwa biyu mata ne; wato, Rabi, wacce ake kira Yaya ta Zagi, Maimuna wacce ake kira Yaya ta Bichi.

An sa masa suna Yusuf, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, shi Madaki yana kiran shi Abbana. Sunan Maitama kuwa an sa masa shi ne saboda Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da makamai sosai lokacin basasar Kano. Akan yi wa duk wani mai suna Yusuf lakabin Maitama.

Madakin Kano ya yi wa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mai kula da dukkan al’amuransa na gida da kula da Dawakai. Maitama, yana dan shekaru 4 mahaifiyarsa Hauwa, wacce ake kira ‘Yarkayi ta rasu. Ita ALLAH ya yi ta ne mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bikin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan bikin, halinta da iya maganarta Maitama ya gado.


Madakin Kano ya saka Maitama a makarantar Elimintari ta Shahuci a cikin watan daya (Janairu), shekara ta dubu daya, da dari tara, da talatin, da bakwai (1937), dama kafin a kai su makarantar boko, suna yin karatun kur’ani a gida. A ka’ida shekaru hudu ya kamata ace an yi a elimantari, amma saboda hazakar da Maitama ya nuna shekaru biyu kawai, ya yi aka ba shi damar daukar jarabawar zuwa gaba. A wannan lokacin ne Maitama ya fuskanci kalubalen da bai taba fuskanta ba a rayuwarsa.

Domin a wannan gabar ne Madaki Mahmudu, mai daukar dawainiyarsa a rayuwa ya rasu cikin shekara ta dubu daya, da dari tara, da talatin, da tara (1939). Aka bar kujerar Madaki, tsawon shekaru biyu, ba’a nada kowa ba, har sai a shekara ta dubu daya, da dari tara, da arba'in, da daya (1941).

Gaba daya dawainiyyar Maitama ta koma kan Mahaifinsa Abba Sule, wanda a wancan lokacin kuma ba shi da karfin da zai iya daukar dawainiyar 'ya'yan nasa sai da ta kai Abba Sule, ya saida duk wani abunda ya mallaka har da suturunsa (kayan sawa) dan ya dauki dawainiyar ‘ya’yansa, a lokuta da yawa haka suke kwana da yunwa. Ranar da suka samu dan abin daren gasashshen rogo ne za su ci su kwanta.

A karshe Maitama sule ya shiga makarantar Middle, a wannan datsin an kai matsayin da Maitama ko suturar da zai sa ba shi da ita, kayan makaranta kawai su ne kayan sanyawansa.

A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana dan shekaru 13. Maitama, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma kama aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano.

Maitama sun tsaya zabe da shi da tsohon Malaminsa a makaranta, Malam Aminu Kano, wannan zabe ya gudana ne a Central Office, wannan abu ya faru ne cikin shekara ta 1954.

Lokacin da aka fadi sakamakon zaben Malamin, zaben ya bada sanarwar cewa Maitama ne ya lashe wannan zaben. Ana fadar haka Aminu Kano, ya juyo ya cewa Maitama, ina taya ka murna, saura in kaje kuma ka ba mu kunya. Maitama ya cewa Aminu Kano, “Yallabai wallahi, ba zan ba ka kunya ba”.

Suka riko hannun juna suka fito tare, wanda suka fara gamuwa da shi shi ne Ado Bayero, inda ya rike hannun Maitama, ya nufi inda magoya bayansa suke, ya ce sun ci zabe.

Ya zama ministan tama da karafa, duk a wannan jamhuriya ta farko. Bayan faduwar jamhuriya ta farko, ya dawo gida Kano, inda ya rike mukamin kwamishina mai kula da kananan hukumomi a gwamnatin Audu Bako. Ya rike mukamin shugaban hukumar sauraren koke-koken jama’a ta kasa a gwamnatin Murtala. Ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar NPN, amma Shagari ya kada shi a zaben fidda gwani. Ya yi wakilin Najeriya na dindindin a majalisar dinkin Duniya watau "united nation" <<kasashe=da=suka=hada=kai>>.

Muna fatan Allah ya yi masa Rahama kuma yagafarta masa, ya kuma sa aljanna tazama makomarsa ya albarkaci zuriyarsa da dukkan sauran musulmai da suka rigamu gidan gaskiya, idantamu tazo Allah yasa mucika da imani.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

[1]

  1. "UN launches anti-apartheid year," The Globe and Mail (Canada). January 12, 1982