Abdullahi Aliyu Sumaila

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdullahi Aliyu Sumaila
Rayuwa
Haihuwa 21 ga Maris, 1946
Mutuwa Kano, 11 ga Janairu, 2003
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Nigerian People's Party (en) Fassara

Abdullahi Aliyu Sumaila (An haife shi a ranar 23 ga watan Maris shekara ta alif dari Tara da arba'in da shida 1946 - ya rasu a ranar 11 ga watan Janairun shekara ta 2003).

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Ya kasance mutumin da ya fara samun takardar kammala karatun jami'a a mazabar Sumaila ta Karamar Hukumar Sumaila, ya gudanar da aikin Gwamnati a matakai da dama a Nijeriya, dan siyasa, dan kasuwa kuma malamin makaranta, wanda ya zama Sakataren Kungiyar Dalibai Musulmai na Makarantar Horan Malamai ATC/ABU Kano, Sakatare-Janar na Kasa a Kungiyar Dalibai Yan Asalin Jihar Kano, Mataimakin Shugaban Makarantar Firamare ta garin Tsangaya a Karamar Hukumar Albasu, Mataimakin Sakatare a Ofishin Majalisar Zartarwa (Cabinet Office) ne da ke Karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Mataimakin Sakatare a Ma'aikatar Cikin Gida da Watsa Labarai ta Jihar Kano, Sakataren Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano, Babban Sakatare na Gwamnan Jihar Kano, Babban Sakatare na Dindindin na ma'aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri da Kuma Ma'aikatar Daukar Ma'aikata ta Gwamnatin Jihar Kano, Shugaban Kungiyar Wasan Sanda (Hockey) ta Jihar Kano, Shugaban Hukumar Gudanarwa na Gidan Talabijin na Jihar Kano CTV 67 (Gidan Talabijin din Abubakar Rimi),ne wato Shugaban Gudanarwa na Hukumar Fadamun Kogunan Hadejia da Jama'are, Janar Manaja a Kamfanin Arewa Steel Works, ya kuma rike Darakta a wasu Kamfanoni masu zaman Kansu.[1][2]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

A Unguwar Mandawari da ke Kofar Kudu, Karamar Hukumar Sumaila aka haife shi, ana kiran zuriarsa da Muallimawa masu asali daga Zuriar Fulani Jobawa, Fulani Torankawa da kuma Madinawa Malamai, sunan Muallimawa ya samu ne daga kalmar larabci ta Muallim wacce ta ke nufin malami, matarsa da kuma shi sun taba zama malamai a tarihin rayuwarsu dan haka a ke kiran zuriarsu da Muallimawa.[3]

Sunan mahaifinshi Sheikh Aliyu-Talle Sumaila ibn Abdurrahim ibn Ibrahim ibn Shi'ithu ibn Ghali, mutumin unguwar Mandawari ne a garin Sumaila, wanda yake sana'ar noma da sayar da rake.[4]

Dangin mahaifinsa, ta wajen uba, sun fito daga zuriar Banu Gha ta Imam Ghali (Malam Gha), wanda wasu ke kiransu Madinawa Malamai, mashahuran malamai da suka zauna a unguwar Baƙin Ruwa wace ta ke Ƙaramar Hukumar Dala, a Kano, Kafin Masarautar Kano ta tura su Garin Kadawa, a Ƙaramar Hukumar Warawa, domin Koyar da addinin Musulunchi, wanda a Garin Kadawar ne suka kafa Zawiya, kuma aka sa sunan wajen da suke zaune Unguwar Malamai, a ke kuma Kiran Gidan nasu Gidan Malamai, wadansu jama'a su na tunanin Kakansa na wajen uba mai suna Sheikh Abdurrahim Ibrahim Shi'ithu Ghali (Waliyi Abdurrahim-Maiduniya ko Malam Abdu Mai Duniya) waliyi ne, sunan Madinawa da a ke kiran zuriar gidan ya samu ne daga sunan garin Madinah, wasu daga cikin zuriar Madinawa Malamai su na danganta zuriar da Sharifantaka, kuma ahlil bayt ta wajen Hasan ibn Ali jikan manzon Allah (SAW).[5][6][7]

Dangin mahaifinsa ta wajen uwa daga Ƙabilar Fulanin Chango suka fito da Fulani Jobawa domin Kakarsa ta wajen uba, Maryam Inuwa Chango Bafulatanar Chango ce ta wajen mahaifin ta, kuma Bafulatanar Jobawa ta wajen mahaifiyar ta Binta ibna Sarkin Sumaila Dansumaila Akilu. Shi Sarkin Sumaila Dansumaila Akilu ya fito ne daga cikin zuriar Gidan Makaman Kano Iliyasu da Makaman Kano Isa na Daya wanda suka riƙe sarautar Hakimai a Gundumar Wudil wanda a yanzu sune Ƙananan hukumomin Wudil, Sumaila, Takai da Garko.[8][9][10]A zamanin Sarkin Kano Aliyu Babba ya nada Sarkin Takai Umaru Dan Maisaje a matsayin Makaman Kano wanda Bajobe ne ta wajen Kakarsa ta wajen uba Habiba ya'yar Malam Bakatsine, daga lokachin ne ya'yan maza da ya'yan mata a zuriar Jobawa sukan yi fatan zama Makaman Kano.[11]

Dangin mahaifiyarsa Mai suna Hajiya Amina Idris Ali Kofar Yamma Sumaila sun fito ne daga Ƙabilar Hausawa na unguwar Kofar Yamma a Garin Sumaila, mahaifinta yana noma da sayar da tufafin maza, kakanta na wajen uba kuma ya yi cinikin bayi da noma.[12][13]

Ana kiran Abdullahi Aliyu Sumaila da laqabin sunan Dattijo, domin sunan Kawun Kakarsa ta wajen uba aka mayar, mai suna Abdullahi Mai Kili Wudil (Kakar Abdullahi Sumaila ta wajen uba mai Suna Maryam ta na da mahaifiya mai suna Binta ibna Dansumaila Akilu, ita Binta ibna Sarkin Sumaila Akilu da Abdullahi Mai Kili uwarsu daya, amma uba kowa da nasa).[14]

Ya shiga makarantar Al-Qur'ani ya haddace Al-Qur'ani kuma ya zama Hafiz, ya kuma karanci sauran litattafan fiƙihu, Yawancin Malaman da suka koyar da shi yan darikar Tijaniya ne, amma ya sauki shugabancin Tijaniya lokachin da yake karatun jami'a a rubutunsa, daga bisani ya mayar da hankalinsa zuwa karatukan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Aminudden Abubakar, wadanda su ke da ra'ayin Izala amma bai yarda da wasu ra'ayoyi na wasu yan Izala ba musali yana da ra'ayin babu laifi karatun Dalailul Khayrati, a kan Mawlidi ya na ganin cewa idan aka bi shari'ar musulunci wajen yin sa babu laifi wannan ra'ayi na Mawlidi ya zo dai-dai da na Imam Siyudi.[15]

Ya halarci karamar firamare ta Sumaila daga shekara ta, 1956 zuwa 1959 sannan Sumaila Senior Primary daga shekara ta, 1960-1962 sun yi aji daya tare da Alhaji Bashir Dalhatu (Wazirin Dutse) da kuma Alhaji Idi Salihi Dal. Ya ci jarabawar shiga makarantar Sojan Najeriya da ke Zariya da Kwalejin Malamai ta Wudil, mahaifiyarsa ta ki ba shi izinin shiga Makarantar Soja kuma ta fi son Kwalejin Malamai, ya halarci kwalejin malamai ta Wudil daga shekara ta, 1963 zuwa 1967, kuma ya sami shedar kammala karatun a shekara ta 1967. Ya kasance a aji daya tare da Farouk Iya Sambo tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano, da Alhaji Ado Shehu Ringim, tsohon Babban Sakatare a Gwamnatin Kano. Ya halarci kwalejin ci gaban malamai ta Kano ABU Zariya (ATC / ABU Kano) yanzu ana Kiran makarantar da sunan Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano (FCE,Kano) daga shekara ta , 1968 zuwa 1970 don samun takardar shedar kammala karatun Najeria a fannin ilimi wato NCE, amma ya bari a shekararsa ta biyu ya fara karatun Jami'a a Jami'ar Ahmadu Bello daga shekara ta, 1970 zuwa 1974. Ya kammala karatunsa a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya samu digiri na farko a Kimiyyar aikin Gwamnati (Kimiyyar Siyasa) a shekara ta, 1974, ya yi wannan karatun tare da tsohon gwamnan jihar Filato Fidelis Tapgun, da Abubakar Mustapha mni, MFR, tsohon Sakataren Shirye-shirye na Jam'iyar PDP, ya yi karatun Digiri na biyu a Kimiyyar Siyasa daga shekara ta, 1976 zuwa 1977. Yana da takardar shedar kwararru ta fannin tsaro daga kwas din da ya halarta a fanin.[16][17][18][19]

Ya auri (Mrs.) Hajiya Saude Abdullahi - Aliyu a shekara ta, 1973, a na kiran zuriar da suka samu da Muallimawa, saboda shi da matar sun taba kasan cewa Malaman Makarantar Boko da na Addinin Musulunchi, yanzu haka tsohuwar Daraktar Ma’aikatar Ilimi ta Gwamnatin Taraya ce, mahaifinta Abdullahi Maikano Sarkinfulani ya rike matsayin Sarkin Fulani, Dagacin Tsibiri a Wudil, kakanta Shaykh al Islam Mahmoud Allamah ne kuma mahaifin kakanta Dawaki Bello ya rike sarautar Dagacin garin Wudil, wani bafulatani ne daga Fulani Torankawa (Torodbe), dangin da ke jagorantar Khalifanci na Sakkwato da ke rike da sarautar Sarkin Musulmi da Amir al-Mu'minin, na Daular Fulani. (wanda ya kunshi Jihadin Fulbe Jihad wanda Sakkwato ta kasance hedikwata), yayin da mahaifiyarta Hajiya Rabi ibna Shehu-Usman ibn Abdussalam (Inna) ta kasance jikar Alkalin Gano Isiyaka ta wajen mahaifiyar ta da ake da Kira Hama wace ta fito daga Garin Gano a Karamar Hukumar Dawakin Kudu.[20]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi aikin koyan koyarwa (Teaching Practice) ga daliban firamare a shekara ta, 1965 zuwa 1966. A shekara ta, 1967, ya zama Mataimakin Shugaban Makaranta kuma malamin lissafi a Tsangaya Primary school a Karamar Hukumar Albasu, dalibansa sun hada da Kabiru Ibrahim Gaya, Ya yi bautar kasa wato aikin masu yi wa kasa hidima a matsayin malamin darusan Government, Tarihi, Turanci da Adabin Turanci a Makarantar Etuno Grammar, Igarra Jihar Midwest daga 1/8/1974 - 31/7/1975 inda ya samu yabo don kyakkyawan aiki daga makarantar da al'umma. Ya kasance Mataimakin Sakatare a Cabinet Office a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Mataimakin Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Watsa Labarai ta Jihar, Sakataren Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano, Babban Sakataren Gwamnan Jihar Kano, Babban Sakatare a Gwamnatin Jihar Kano a ma'aikatar ayyuka, gidaje da harkokin sufuri, Babban Sakatare a Hukumar daukar ma'aikata ta Jihar Kano, Janar-Manaja Kamfanin Arewa Steel Works,Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are, Shugaban Gidan Talabijin na Jihar Kano, Sakataren Kwamatin Gwamnatin Kano na mayar da Kasuwanchi wajen 'yan Kasar Najeriya wanda Nigerian Enterprises Promotion Decree ya tanadar, Uban Kungiyar Majalisar Matasa ta Kasa reshen Jihar Kano, Memba a Kwamitin Turaki wanda Alhaji Shehu Shagari GCFR Turakin Sokoto tsohon Shugaban kasa na zartarwa, Tarayyar Najeriya a Jamhuriyyar Najeriya ta Biyu ya jagoranta, da sauran mukamai daban-daban da ya rike.[21]

Aminu Kano, Abubakar Rimi da Shehu Musa Yar'adua sun zama jagororin siyasar sa a lokuta daban-daban. Ya kasance mai fada a ji ga 'yan siyasa da yawa ciki har da Rabiu Kwankwaso da Kawu Sumaila wanda ya dauki nauyin takarar sa ta kujerar Shugaban karamar Hukumar Sumaila a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a ranar 15 ga watan Maris, shekara ta, 1997 a karkashin jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) amma Kawu Sumaila ya fadi zaben, dan takarar Magaji Abdullahi, Hon. Musa Inuwa Gala na National Center Party of Nigeria (NCPN), ya lashe zaben. A zaben majalisar dokokin jihar Kano na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a shekara ta, 1998

1999, Abdullahi Aliyu Sumaila ya sa ke daukar nauyin Kawu kuma ya mara masa baya amma tikitin jam'iyyar ya kasance an baiwa Hon. Shehu Musa Usman, Abdullahi Sumaila ya kasance memba na jamiyar Northern Elements Progressive Union (NEPU), People's Redemption Party (PRP), Nigerian People’s Party (NPP), People's Front of Nigeria (PF), Social Democratic Party (SDP), People's Democratic Movement (PDM), People's Consensus Party (PCP), United Nigeria Congress (UNC), United Nigeria Congress Party (UNCP) da People's Democratic Party (PDP).[22][23]

Shi ne Shugaban Kungiyar NEPU Zahar Haqu na Gundumar Sumaila, Sakatare Janar na Jihar Kano na Jam’iyyar PRP bangaren Michael Imodu (yan santsi) a Jamhuriyyar Najeriya ta Biyu da Mataimakin Shugaban Jihar Kano na SDP a Jamhuriyyar Najeriya ta Uku.[24]

Ya kasance manajan yakin neman zabe na Muhammadu Abubakar Rimi dan takarar Gwamna a Jam’iyyar NPP a zaben shekara ta, 1983, Sakataren Siyasa na Dan takarar Gwamnan Jihar Kano Alhaji Ahmadu Rufa’i a karkashin Jam’iyyar SDP a Jamhuriyyar Najeriya ta Uku, Delegate da ke wakiltar Sumaila a Babban Taron Jamiyar People's Front PFN a watan Yunin shekara ta, 1989, Jagoran Jam’iyyar Peoples Front of Nigeria PF na Karamar Hukumar Sumaila, Shugaban Kwamitin hadewar Engr.Magaji Abdullahi da Ahmadu Rufa’i a zaban Gwamnan SDP na Jihar Kano, Daraktan Kamfen Arewa maso Yamma wace take da hedikwata a Jihar Kaduna na Manjo Janar Shehu Musa Yar’adua dan takarar Shugabancin Nijeriya a Jamiyar SDP - a shekara ta, 1992, Ten Delegate daga mazabar Tarauni a Karamar Hukumar Birni (Kano Municipal) a jamiyar SDP a karkashin zaben kai da halinka (Option A4) na ranar 6 ga watan Fabrairu shekara ta, 1993, Jagoran United Najeriya Congress (UNC) na Karamar Hukumar Sumaila, Memba Kwamitin Tattaunawa na Kasa na jamiyar United Nigeria Congress Party (UNCP), Memba na Kwamatin Dattawa a jamiyar UNCP reshen jihar Kano jagoran Jami'yar UNCP na Karamar Hukumar Sumaila, Memba a Kwamitin riko na jihar Kano na jamiyar UNCP a shekara ta, 1997, Jagoran jamiyar People's Democratic Movement PDM na Karamar Hukumar Sumaila, Jagoran Peoples Consensus Party na Karamar Hukumar Sumaila, Memba a Kamitin Dattawan Jihar Kano na Jami'iyar PDP, Memba Kwamatin Gudanar da zaben fida Dantakarar Gwamna da yan majalisun Jiha a Jami'yar PDP na jihar Kano a zaben shekara ta, 1999. Darakta Janar na Kamfen din Hon. Nura Mohammed Dankadai na takarar sanatan Kano ta Kudu Karkashin Jam'iyar PDP - a shekara ta, 2002. Delegate na fidda gwani na takarar Gwamnan jihar Kano a Jami'yar PDP a watan Disamba, shekara ta, 2002, Jagoran Jami'yar PDP na Karamar Hukumar Sumaila a shekara ta, 1998 zuwa 2003, Shugaban kwamitin dattawa na Jami'yar PDP na Karamar Hukumar Sumaila a shekara ta, 1998 zuwa 2003.[25][26]

Ya zama Shugaban darktochi na kampanin KADFRU, Shugaban Darktochi na Kampanin Sauda Voyager Nigeria Limited, Shugaban Darktochi na Kampanin Ramy Palace Nigeria Limited, Shugaban Darktochi na Kampanin Pathfinder Consultancy Services, Shugaban Daraktochi na Kampanin Aurum Nigeria Limited, Shugaban Darktochi na kampanin Precise Oil Resources, Shugaban Darktochi na Kampanin Saymar Bread,Janar Manaja kuma Darakta a kampanin Arewa Steel Works. Ya rike mukamin Darakta a kampanonin Hayder Trading and Manufacturing Company Nigeria Limited, Katday Modern Furnitures Company Nigeria Limited, Dayekh Tiles Nigeria Limited, Rima Farms, Dayekh Ali Nigeria Limited and United Confectionery Nigeria Limited.[27]

Ya kasance memba na Kungiyar Scouts Association of Nigeria, Sakataren Kungiyar dalibai musulmi na Kwalejin Horan Malamai ATC/ABU Kano, Sakatare-Janar na Kungiyar Kasashe masu tasowa reshen Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, Ma'ajin Kwamatin tunawa da Marigayi Dakta Bala Mohammed, Shugaban Kungiyar wasan Hockey ta Jihar Kano, Shugaban Kwamitin yaki da nuna wariyar launin fata na Gwamnatin Jihar Kano, Sakataren Kwamatin Gwamnatin Kano na tunawa da Marigayi Janar Murtala Mohammed tsohon shugaban Kasa, Mamban kwamitin farfado da wasanni na gwamnatin jihar Kano, Mamba kwamitin na Gidauniyar Jihar Kano (Kano Foundation) reshen Karamar Hukumar Wudil, Shugaban Kwamitin Kudi na Gidauniyar Jihar Kano( Kano Foundation) reshen Karamar Hukumar Wudil, Memba Kungiyar bada tallafin Jini ga marassa lafiya, Memba a Kungiyar zartarwa ta iyaye da Malamai na Makarantar Kano Capital School, Memba a Kungiyar zartarwa na Iyaye da Malamai na makarantar St. Thomas Secondary School, Memba Kwamitin Jihar Kano na duba Tsarin Mulkin Najeriya, Memba Babban Kwamitin bada mulki daga soja zuwa farar hula na Gwamnatin Jihar Kano shekara ta, 1999. [28][29]

Ya kasance Memba kungiyar Iyaye da Malamai na Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Kano (FGC, Kano), Memba na Kungiyar Iyaye da Malamai na FGC Kano Staff Primary School, Memba Kungiyar Iyaye da Malamai na Makarantar Samadi International School.[30]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 

 1. Sumaila, Ahmed (2003). The making of a Public Servant:Abdullahi Aliyu Sumaila. Kano: Kadawa Gaskiya Press.
 2. Abdullahi, Ahmed (1994). Kano State Permanent Secretaries in the Second Republic. Kano: Aurora Press.
 3. Sumaila, Ahmed (2003). The Life and Times of Abdullahi Aliyu Sumaila. Kano: Sauda Voyager Press.
 4. Hassan, Muhammad (1998). The History and Genalogy of Sheikh Aliyu T. Sumaila. Sauda Voyager Printers.
 5. Tarikh Arab Hadha al-balad el-Musamma Kano. Journal of Royal History. 1908.
 6. Abubakar, Badamasi. Trans Saharan Trade: Networks and Learning in Ninetenth Century Kano. Danjuma Press.
 7. Sani, Muhammadu (1990). Arab Settlers in Kano. Sauda Voyager.
 8. Aminu, Muhammadu (2005). The Jobawa Fulani of Sumaila. Kano: Kadawa Gaskiya Press.
 9. Aliyu, Sumaila. Jobe a clan compendium. Kano.
 10. Idris Rimi, Abdulhamid (1991). The History of Sumaila. Zaria: Institute of Administration, Ahmadu Bello University.
 11. Smith, M.G. (1997). Government in Kano 1350-1950. Westview Press, A Division of HarperCollins Publishers,Inc.
 12. Danlami, Nasidi (2013). The people of Kofar Yamma Sumaila. Kano: Trends Printers.
 13. Idris, Fatima (1998). The History of Hajiya Amina Idris:A Life of Service. Idrisiya Printers.
 14. Bashir, Ali (2000). Kano Malams in the Ninteenth Century. River Front Press.
 15. Kaptein, N.J.G. (1993). Muḥammad's Birthday Festival: Early History in the Central Muslim Lands and Development in the Muslim West Until the 10th/16th Century. Leiden, The Netherlands: E.J. Brill. p. 21. ISBN 9004094520.
 16. "Bashir Dalhatu".
 17. "KG".
 18. "ABU Zaria Alumni". Archived from the original on 2021-06-28. Retrieved 2021-06-28.
 19. "Nigeria Federal States". WorldStatesmen.org. Retrieved 2010-02-19.
 20. Sumaila, Abdullahi (1974). Rise and fall of the KPP in Kano Province. Ahmadu Bello University Press.
 21. Marxism and African Reality: Solidarity Message. Office of Adviser on Political Matters, Publicity and Propaganda Department, Governors Office. 1983.
 22. Rabiu, Usman. Kwankwasiyya Ideology: Emergence, Influence, and Legitimacy.
 23. Tukur, Sadik (15 July 2016). Gudumawar Zuriár Matawallen Katsina ga kasa. Aminiyya Newspaper.
 24. Bashir, Garba (2002). NEPU in the Sumaila District. Kano: Kadawa Gaskiya Press.
 25. Rimi, Muhammadu Abubakar (1983). Why we are in the NPP. Gaskiya Corporation.
 26. Fayemiwo, Moshood (2017). Asiwaju. Strategic Books. ISBN 978-1-946539-50-2.
 27. Aminu, Muhammadu (2004). Abdullahi Aliyu Sumaila:The Kano Revolutionary. Kano: Kadawa Gaskiya Press.
 28. Maikaba, Balarabe (2001). Political Organiser. Leomax graphics.
 29. Ibrahim, Rufai (1981). The Example of Bala Muhammad.
 30. Aliyu, Aminu. The History of Parents Teachers Associations in Kano State. Kano: Faith Printing Press.