Sokoto (birni)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Gidan Sarkin Musulmin, a Sokoto.

Sokoto ko Sakkwato birni ne, da ke a jihar Sokoto, a ƙasar Nijeriya. Shi ne babban birnin jihar Sokoto. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2006, jimilar mutane 427,760 (dubu dari huɗu da ashirin da bakwai da dari bakwai da sittin). An gina birnin Sokoto a farkon karni na sha tara.