Ramadan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Ramadan
calendar month
subclass ofHijri month Gyara
MabiyiSha'ban Gyara
followed byShawwal Gyara

Ramadan (Larabci رمضان) Watan Musulunci ne na tara, kuma a cikin sa ne aka saukar da Alqur'ani ga Annabi Muhammad (s.a.w).

Musulmi suna gabatar da sallar tarawi da azumi

Azumin Musulunci a watan Ramadan na daya daga cikin shika shikan Musulunci guda biyar. Musulmi kan azumci watan iyakar tsayin sa kullum tun daga fitowar alfijir har ya zuwa faduwar rana. Musulmi sunyi imani da fadin an saukar da Alkur'ani ne a watan na ramadan wanda ake yin wahayin sa a hankali a hankali daga Allah zuwa ga Annabi Muhammad (s.a.w) ta hannun dan aiken Allah Mala'ika Jibrilu. Annabi ya fada ma musulmai "Ana bude dukkannin kofofin Aljannah kuma ana kulle kofofin Jahannama tare da daure shaidanu a watan na Ramadan". Daga karshen watan ana gabatar da bikin karamar sallah.

Lokuta[gyara sashe | Gyara masomin]

Ramadan wata ne Mai falala

Lokuta a watan Ramadan.

Bayan Hijira Ranar farko Ranar karshe
1437 06 Yuni 2016 05 Yuli 2016
1438 27 Mayu 2017 24 Yuni 2017
1439 17 Mayu 2018 14 Yuni 2018
1440 06 Mayu 2019 03 Yuni 2019
1441 24 Afrilu 2020 23 Mayu 2020
1442 13 Afrilu 2021 12 May u2021
Kwanan watan Ramadan tsakanin 2016 da 2021

A kowa wani goma karshen watan Ramadan Ana saran samun rana daya wanda ake kira da lailai kadari a larabce. Wannan rana alqur'an mai girma yayi bayanin cewa wannan ranar ko kuma dAren yafi rana ko dare dubu. Domin kuwa duk wanda yayi sa'ar wannan dAren lailai duk Addu'ar da yayi ta amsu