Azumi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Azumi shine kamewa[1] daga cin abinci ko sha ko jima i (saduwan aure) ko shan taba ko allura na abinci daga ketowar alfijir nabiyu har zuwa faduwan rana hakika Allah ya wajabta azumi acikin alkur ani maigirma inda yace dukwanda yaga jinjirin wata to ya dauki azumi madamar shi Musulmi ne (surah albakarah 2:185) sannan yakaracewa hakika anwajabta muku azumi kamar yanda akawajabta ma wanda suke gabaninku koku zakuyi takawa(albakarah 2:183) abubuwanda suke karya azumi 1=cin abinci 2=shan abinsha 3=jimai 4=shantaba 5=abu maisa maye 6=alluran abinci. Azumi akwai wanda yake wajibi akwai kuma na Nafila wato sunnah, Azumin wajibi wato na Farilla shine Azumin watan Ramadan indai ya riski Musulmi yanada lafiya, da hankali, kuma balagagge (Balaga) wanda ya samu ikon yi ma'ana ba matafiyi ba, kuma ba lokacin jinin al'ada ba ga mata ko kuma Jego ko kuma tsohon da tsufa yasa baya iya yin Azumi, ko kuma wani dalili mai ƙarfi wanda ma'abota Ilimin addinin Musulunci sukayi fatawa a kanshi. Sai Azumi Nafila kamar azumin Litinin da Alhamis sai kuma sauran azumin Nafila waɗanda suma sanannun ne. Sai dai azumin bakance shima akwai inda yake wajibi, amma don sanin haka sai a tambaya Malaman Musulunci Masu riƙon sunnah waɗanda keyi don Allah. Ina ƙara nanata wa azumin watan Ramadan wajibi ne[2] don saboda haka Ayoyin Alqur'ani mai girma da sukayi nuni da hakan. Anason a lokacin Azumin watan Ramadan mutum ya yawaita Ibadah kamar yawan karatun Alqur'ani, sadaƙa Istigfari, yawan nafila musamman Sallah tarawihi Tahajjud da kuma kiyaye jam'i Sallolin Farilla da dai sauran Ibadah da shara'a ta yarda da yinta. Don ƙarin bayani akan Azumi a duba littafin (Iziyya da Risala).

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]