Sallolin Farilla
Sallolin Farilla | |
---|---|
religious behaviour (en) | |
Bayanai | |
Facet of (en) | Musulunci |
Sallolin Farilla Guda biyar ne gasu kamar haka:[1]
Salloli
[gyara sashe | gyara masomin]1. Sallah Asubah Anayinta bayan fitowan alfijir saadiqi. Daga Rana ta fito lokacin lalurinta ya shiga. Tanada Raka'a biyu ne.[2]
2. Sallah Azahar Anayinta bayan zawalin Rana (idan rana ta gushe daga tsakiya) lokacin lalurinta idan rana ta fadi. Tanada Raka'a hudu (4).
3. Sallah La'asar Anayinta bayan faifayewar hasken rana. Tana zama laluri daga zaran rana ta fadi. Tanada raka'a hudu (4).[3]
4. Sallah Magrib Anayinta bayan faduwar rana. Lokacin lalurinta idan aka shiga daya bisa ukun dare na karshe ⅓ (sulusul lail al-akirah). Tanada raka'a uku (3).
5. Sallah Isha'i Anayinta bayan bayan bacewar Jan rana wato na bayan sallah magrib, wani ja-ja da yake fitowa a yamma bayan rana ta fadi wato dai lokacin da duhu ya bayya sosai. Lokacin lalurinta daya da na magrib. Tanada raka'a hudu (4).[4]
Allah shine masani.
Ire-iren salloli
[gyara sashe | gyara masomin]Bayaga sallolin farilla, akwai wasu sallaloin da suka haɗa da;
- Sallar roƙon ruwa
- Sallar Nafila
- Sallar Matafiyi (Qasaru)
- Sallar Idi ƙarama
- Sallar Idi Babba
- Sallar Sunnah
- Sallar Asham
- Sallah Tarawihi.
- Sallahar gawa da saurasu.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.muhtwa.com/369356/%d8%a2%d9%8a%d8%a7%d8%aa-%d8%b9%d9%86-%d8%a7%d9%84%d8%b5%d9%84%d8%a7%d8%a9/
- ↑ https://www.wattpad.com/747056703-amsoshin-tambayoyinku-bayani-akan-salloli-biyar
- ↑ https://www.islamweb.net/ar/article/178255/%D9%85%D9%8E%D8%AB%D9%8E%D9%84-%D8%A7%D9%84%D8%B5%D9%84%D9%88%D8%A7%D8%AA-%D8%A7%D9%84%D8%AE%D9%85%D8%B3
- ↑ https://www.alukah.net/sharia/0/141741/