Sallah Tarawihi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sallah Tarawihi
Sallah
Musulmi maza da mata suna sallah tarawihi/asham/Alkayeji
musulmai na sallah tarawihi a masallaci

Sallah Tarawihi sallah ce da akeyi a watan Ramadan wato da Azumi. A Hausa kuma Asham ko kuma Alkayeji duka ana kiranta da wannan sunan, Mafi yawan ta raka'a sha biyu ce (12) anayin takwas goma sha ɗaya,[1] ita kuma sallah tarawihi sunnah ce mai ƙarfi sosai. Sannan kuma duk Bayan anyi raka'a biyu sai a sallame haka har a gama, ana yinta bayan sallah isha'i ne. Idan mutum bai sameta a masallaci ba zai iya yi da iyalinsa a cikin gida sai dai yinta a masallaci yafi lada[2], sallah tarawihi da Tahajjud kusan abu ɗaya ne sai dai ita Tahajjud anayin ta ne a goman ƙarshe a watan Ramadan, sannan kuma ba'a son a buɗe sauti a sallah Tahajjud don kada a shiga hakkin wasu[3] dukkan su dai salloli ne masu matuƙar muhimmanci a watan Ramadan, sai dai don sanin babanci tsakanin tarawihi da Tahajjud shiga nan[4] don ƙarin bayani a tuntuɓa Malamai ma'abota sani. Allah yafi kowa sani.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]