Jump to content

Tabi'un

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tabi'un
group of humans (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na malamin addini da Salaf
Addini Musulunci
Mabiyi Sahabi
Ta biyo baya Tabi‘ al-Tabi‘in

Tābi‘un Tabi'ai (larabci|التابعون, At-Tabi'un, ko kuma Tābi‘een larabci|ar|التابعي, guda tābi'i larabci|ar|التابع), Ma'ana "Mabiya" ko "Masu zuwa", sune al'ummar Musulmai dasuka biyo bayan Sahabbai ("Al'ummar" Manzon Allah Muhammad (S.A.W), sannan kuma suka koyi karatuttukan Manzon Allah daga sahabbai.[1] Tabi'i shine wanda yasani ko yaga wani Sahaba koda dayane.[2] hakane yasa, suka taka muhimmuyar rawa a bangaren cigaban addinin Musulunci da kuma kafa daular musulunci na Halifanci. Karnin Musulmai dasuka biyo bayan Sahabbai sune Tabi'ai da Tabi‘ al-Tabi‘in. Wadannan karnoni uku sune suka hada karnonin salaf a musulunci.

Ma'anar Sunna

[gyara sashe | gyara masomin]

Musulmi daga reshen Sunna na Musulunci sun siffanta tabi’a a matsayin musulmi wanda:

  1. Yaga akalla daya daga cikin sahabban Muhammad
  2. Ya kasance mai shiryuwa kan tafarkin gaskiya (ar-rāšidūn)
  3. Wanda kuma ya rasu a wannan tafarki. Don haka ba a kiran Khawarij da tabi’un duk da cewa sun ga yawancin sahabban Muhammad.

Musulmi Ahlus-Sunnah kuma suna daukar tabi’un a matsayin mafificin zamani bayan sahabbai. A wajen musulmi ‘yan Sunna, Muhammad ya ce: “Mafi alherin mutane su ne wadanda suke rayuwa a zamanina, sannan wadanda suke bayansu, sannan wadanda suke bayansu (zuriya ta biyu)”.[3]

Mafi yawan malaman musulmi sun kasu tabi’un zuwa kashi uku:[4]

  1. Daliban sahabbai wadanda suka musulunta kafin a mallakar Makka
  2. Daliban sahabbai da suka karbi musulunci bayan an mallaki Makkah
  3. Daliban sahabbai wadanda ba su balaga ba a lokacin wafatin Muhammad (SAW)

Jerin Tabi'ai

[gyara sashe | gyara masomin]

Tabi'i na farko da ya rasu shi ne Zaidu bn Ma'amar bn Zaid, shekara 30 bayan hijira, kuma na karshe da ya rasu shi ne Khalaf bn Khalifa, wanda ya rasu a shekara ta 180 bayan hijira. A madadin haka, tun da kasancewar Khalaf ibn Khalifa a matsayin tabi’u yana fuskantar ƙalubale daga manyan malamai, na ƙarshe wanda ya mutu a cikinsu shi ne Jarir bin Haazim a shekara ta 170 bayan hijira. Don haka da yawa daga cikin tabi’un an ba su aikin kiyaye hadisan Musulunci tun daga zamanin sahabbai har zuwa musulmi na baya.

  1. Glasse, Cyril (2001). The New Encyclopedia of Islam. Altamira. p. 443. ISBN 0-7591-0189-2.
  2. Esposito, John L. (2003). The Oxford Dictionary of Islam. Oxford University Press. p. 301.
  3. "CRCC: Center For Muslim-Jewish Engagement: Resources: Religious Texts". www.usc.edu. Archived from the original on 2008-12-05.
  4. Siddiqi, Muhammad (1993). Hadith Literature (PDF). Oxford: The Islamic Texts Society. p. 29. ISBN 0946621381.
  5. Morony, Michael G. (1984). Iraq after the Muslim Conquest. Princeton, New Jersey: Princeton University Press. pp. 435, 467. ISBN 0-691-05395-2.
  6. Meri, Josef W. (October 31, 2005). Medieval Islamic Civilization: An Encyclopedia (in Turanci). Routledge. p. 5. ISBN 9781135456030. Abu Hanifa is counted among the most illustrious of the Tabi'un (literally “the successors,”which refers to the second generation of Muslims), and some sources relate that he met at least four Companions of the Prophet
  7. Öncü Sûfîlerden Fudayl b.‘Iyâd’ın (öl. 187/802) İlmî Şahsiyeti." Şırnak Üniversitesi İlahiyat Fakültesi Dergisi 11.24 (2020): 159-185. "..Tabi'un are the people who followed Sahaba, the companions of the prophet), is one of the important names in the history of Islamic science. Fudayl, who was an Arab, spent his life in three regions: Khorasan, Kufa, and Mecca. Names such as Abu Hanifa, Mansur bin Mu'temir.."
  8. 8.00 8.01 8.02 8.03 8.04 8.05 8.06 8.07 8.08 8.09 USC-MSA Compendium of Muslim Texts Archived 2006-07-15 at the Wayback Machine
  9. Hazrat Ali bin Usman Al-Hujwiri (2001). The Kashf Al-Mahjub:A Persian Treatise on Sufism. Justice Karam Shah. Zia-ul-Quran Publications Lahore Pakistan.