Sallar Idi Babba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Infotaula d'esdevenimentSallar Idi Babba
Jiangwan Mosque - Eid Al-Adha.JPG
Iri religious festival (en) Fassara
Rana 10 Dhu al-Hijjah (en) Fassara
Shagulgulan sallah

Sallar Layya, Babban Sallah, Eid al-Adha (larabci-ar|عيد الأضحى|ʿīd al-ʾaḍḥā|lit da turanci Feast of the Sacrifice), kuma ana kiransa da "Sallar Yanka", shine biki nabiyu da musulmai ke gudanarwa a duk duniya a kowace shekara, dayan bikin shine ( Karamin Sallah), ana ganin wannan babbar yafi daraja acikin biyun. Allah yakarrama Annabi Ibrahim (Abraham) Allaihi Salam, ne bayan yamika wuya gareshi akan yarda da yanka dansa Annabi Ismail daomin bin umurni da Allah yabukace shi. Amma, kafin Annabi Ibrahim ya yanka dansa sai Allah ya aiko da babban rago yayanka, sanadiyar hakane ake yanka kuma ake raba namar gida uku, kaso daya, sadaka ga mabukata, nabiyu a rabawa yan'uwa, na uku wanda yayi layyar yaci abinsa.

Bukukuwan Sallah

A kalandar musulunci Islamic lunar calendar. Ana so a musulce ka chanja hanya a dawo daga idi, watau Hanyar ta sauya akan Wanda abi a wurin zuwa.

Ranar Sallah[gyara sashe | Gyara masomin]

Sallar tana zuwa ne a kowace goma (10th) na watan Dhu al-Hijjah. A kuma kalandar duniya ta girigori ranar na canjawa a dukkanin shekara zuwa shekara, ta hanyar rage kwanaki goma shadaya (11).

Yawon sallah
Arfa
masallacin idi
ragon layya
Hoton Yadda ake gudanar da sallar eid a fili
liyafar ranar sallah
hotln rakumi ya kwanta
tohon rago DA akuya

Babbar sallah ranace mai dunbun tarihi a duniyar musulunci DA misulmai wacce take zuwa bayan anyi sallah karama DA wata2 da kwanaki 20. Ranar babbar sallah ranace wacce dunbin miliyoyin musulmin ke fitowa suje fili idi domin su hallacci sallar nafila raka'a biyu domin nuna gadiya ga mahaliccinsu da nuna murnarsu agareshi daya basu damar halattar wannan Rana atarihin rayuwarsu, amwannan ranar Ana yanka abun layya abunda ya sawwaqa ga mutu daga rago, tunkiya, bunsuru, akuya, sa, shanu, shanuwa, rakumi amale, rakuma. Wadannan sune jinsin dabbobin wadanda ake layya dasu kuma rogo ya fi kowane daraja haka rakuma tafi kowannen su karancin daraja wato itace mai daraja ta can kasar. Akanko mutum ya yanka abun layyar sa ya Ciro wasu sassa acikindabba</nowiki>r yafi kamar yadda sunnar manzon Allah (s.a.w) ta nuna. Yin layyar bin sunnar baban annabawane wato Annabi Ibrahim (a.s) kuma bin KO cika umarnin Allah be inda yake cewa " kayi sallah ga ubangijinka kuma kayi sukar rakumi (wato layyar).

Ba'a siyarda manan layya haramunne wanda ya siyar yayi laifi agun Allah, domin Anaso awadatar DA kowa

Ba anyi layya sai a rarraba wa mafi kusanci daman layyar musamman makwafta DA makusanta, domin wanda bayadashi yasamu domin ba'abakin cikin awannanan ranar Anaso kowa yaiyita nishidi DA wallala.

A ranar babbar sallah akanje ziyara ta musamman ga makusanta DA makwafta domin tayasu murnar wannan Rana me matuqar girman daraja kamar yadda ake aiwatar a ranar karamar sallah. Wannan yawon yafi kebantuwa ga YARA DA wasu daga iyayen YARA musamman sabbin aure zuwa gidajen iyayensu domin tayasu murnar wannan Rana, haka amatayinka na wanda aka ziyarta yanada matukar kyau kabada barka da sallah (wato wani Dan ihsani na kidi, nama, cincin, dabino, ds-ds). Bayan ka zuba abinci sunci sunkoshi sai ayimusu wannan ihsani.

Gudanar da bikin sallah babba ya banbanta kowacce kasar DA kuma kowacce al'adar DA yadda take aiwata danata bikin sallah baba DA karama, ya danganta DA yanayin al'adarsu. [1]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. https://www.bbc.com/hausa/multimedia/2012/10/121026_eid_animals_market_gallery