Jump to content

Hadisi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hadisi
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na literary work (en) Fassara da academic discipline (en) Fassara
IPA transcription (en) Fassara ħa.diːθ
Significant person (en) Fassara Muhammad
Karatun ta science of hadith (en) Fassara
Tarihin maudu'i History of hadith (en) Fassara
Kiyaye ta WikiProject Hadith (en) Fassara
Littattafan hadisi.

Hadisi ko Hadith: (da Larabci حديث), a Musulunci ana nufin dukkannin abubuwan da Annabi Muhammad (S.A.W) yayi ko yasa ayi ko aka yi a gabansa bai ce komai ba, ko bai hana ba. Kuma aka tattarashi a rubuce wannan shi ne Hadisi.

Ma'anar Hadisi

[gyara sashe | gyara masomin]

Hadisi na da ma’anoni guda biyu, ma’anarsa a luggance da kuma ma’anarsa a isdilahance. To abinda ya shafemu anan shi ne ma’anarsa a isdilahance, wato ma’anarsa a mahanga ta malaman Hadisi. A wajen su ma’anar Hadisi shi ne Hakaito Fadar Manzon Allah [S.A.W] Aikinsa da kuma Tabbatarwarsa.[1] Wato ya ga abu ko ya ji abu bai ce komai ba. Wannan a Ta’arihi na malaman hadisi na Ahlul Sunnah kenan wato Sunnah Islam. Amma a Ta’arihi na malaman hadisi na Shi'a, hadisi yana nufin Hikaito Fadar Ma’anarsu,Aikinsa da kuma tabbatarwarsa.Wato abinda aka hikaito daga Manzon Allah [S] da kuma A'imma na Ahlul bait [AS] Anan saboda Iiti} adin da mabiya Ahlul-bait suke da shi na cewa Aimma na Ahlul bait Ma’asumaine, saboda haka dukkan zantukansu da ayyukansu da kuma tabbatarwarsu sunna ne. Shi yasa a wannan darasi na Hadisi da za’a dunga gabatarwa lokaci bayan lokaci zamu ga Hadisai masu yawan gaske da aka ruwaito daga wajensu.To tambaya anan menene banbanci tsakanin sunna da hadisi? Sunna ita ce ainihin fadar Manzon Allah,aikinsa ko tabbatarwarsa, ko kuma na daya daga cikin Iimaman Ahlul- bait. Shi ko hadisi shi ne hikaitowa ko ruwaito fadin ko aikin ko kuma tabbatarwar.

Tarihin Rubuta Hadisi

[gyara sashe | gyara masomin]

Tarihin rubuta Hadisi a mahangar shi’a da sunnah.Tarihin rubuta hadisi wani abu ne da Malaman sunnah suka yi bayanai da kuma rubuce-rubuce a kai,kuma ko wannensu da nashi mahangar. Domin a Ahlus-sunnah an soma rubutawa da kuma tattara hadisai a lokacin khalifancin Umar dan Abdul-Aziz, ya yi khalifanci a bayan hijira ta 99 zuwa 101. wannan kuma ya faru ne a kan asasin umarninsa da yin hakan, Amma khalifofin da suka gabace shi sun hana,ba wai kawai sun hana rubutawa ba, a’a har hana yada hadisai aka yi.Ta yiyu wasu su sha mamaki akan haka,amsa anan shi ne su karanci Tarihi zasu ga haka dama fiye da haka.domin zasu ga wadanda suka rubuta hadisai a lokacin Manzon Allah[S] da kuma bayansa aka sa su gogesu,wasu ma konawa suka yi,kai ta kai ma akwai sahabban da aka tsare a madina,aka hana su fita madinar saboda gudun kada su je su yada hadisai. Su wadanda suka dauki wannan mataki hujjarsu ita ce wai kada mutane su shagaltu da wani abu in ba Alkur’ani ba. kuma shi wannan yunkuri na hana rubuta hadisai na Manzon Allah [S.A.W], tun Manzon Allah yana duniya aka fara shi,alal misali akwai wani sahabi mai suna Abdullahi dan Amru da yake rubutawa amma wasu suka hana shi,har ya kai maganar ga Manzon Allah [S.A. W]. Kuma idan mutum duk bai san ire-ire wadannan ba,ai akwai abin da ya auku gab da rasuwar Manzon Allah[S.A.W] da ya bukaci a kawo masa takarda da tawada ya rubuta abinda in an bi shi ba za’a bace ba a bayansa,sai wani daga cikin sahabban da ke wajen ya ce kada a kawo, littafin Allah ya ishemu,to mu duba fa Manzon Allah ne zai rubuta da kansa amma aka hana to ina ga wani. Saboda haka a zahirance ana nunawa cewa wai ka da mutane su shagaltu da wani abu in ba Alqur’ani ba,amma a badinance wadanda suka dauki wannan mataki na hana rubutawa ko yada Hadisai na Manzon Allah suna tsoron hadisai da suke bayanin khalifanci ko kuma fifikon Ahlul-bait,domin idan zata bayyana ma mutane ai ga wadanda Manzon Allah [S.AW] ya bayyana a matsayin khalifofi a bayansa a cikin hadisai to masu khalifanci a lokacin zai kasance ba hujja ga yin khalifcinsu.Shi ya sa a lokacin Mu’awiya ya fito da abun baro-baro yaba da umarnin cewa duk wani hadisi da aka samo daga Imam Ali ko yake bayani dangane da Ahlul bait ko falalarsu kada a yada shi,kuma duk wanda aka samu ya sabama wannan umarni zai dauki mataki a kansa,mutum ya tambayi tarihi zai bashi amsar irin abubuwan da ya yi. Shi ya sa a lokacin idan isnadin hadisi ya tuke ga Imam Ali[AS] sai ka ji an ce,an wane,an wane……daga baban Zainab ko baban Hassan ya ji daga Manzon Allah,wato ba a bayyana sunan Imam Ali,saboda gudun abind a zai biyo baya,kai wasu ma malaman hadisan ko baban Zainab ko Hasan basa fadi,sai dai su ce daga wani mutum ya ji daga Manzon Allah,kuma wani abun mamaki har yanzu a littafan hadisai na Ahlus-sunnah idan mutum na karantawa jefi-jefi zai ci karo da irin wadannan hadisai wanda a karshen isnadin ka ga an ce daga wani mutum ko baban Zainab ya ji daga Manzon Allah.Kuma in mutum ya duba tarihi zai ga cewa lokacin da khalifan Abbasawa mai suna Mansur ya bukaci Malik dan Anas wato shugaban mazhabar malikiyya da ya rubuta littafi na hadisi,wanda da ya rubuta ya sa masa suna muwaddha,to daga cikin sharadin da ya gindaya masa shi ne kada ya kawo hadisai da aka samo daga Imam Ali,mutum na iya bincika muwaddha ya ga hadisai guda nawa ne aka samo daga Imam Ali.Saboda haka tattara hadisai da rubuta su a matsayin littafi bai auku ba a Ahlus-sunnah sai a cikin karni na biyu,kuma in mutum ya yi bincike zai ga cewa mafi yawan malaman Ahlus-sunnah sun bayyana cewa littafin Hadisi na farko da aka soma rubutawa shi ne Muwa]]a.[2]To amma idan muka juya a bangaren shi’a zamu ga akasin haka in mutum ya yi bincike zai ga yadda A'imma na Ahlul bait suka rubuta kuma suka karfafa mabiyansu ga rubuta hadisai na Manzon Allah [S.A.W]. Farkon wanda ya soma rubuta hadisai na Manzon Allah [S] da kuma tattara su shi ne Sayyadina Aliyu AS. kana ya yi haka ne da umarnin Manzon Allah [S.A.W]. Akwai ma manyan littafai na hadisai guda biyu da A'imma [AS] suka gada daga wajen Imam Ali[AS] mai son ganin sunayen littafan da kuma abubuwan da suka kunsa,ya duba littafi mai suna “Ma’alimul-madrasataini” juz’i na biyu. Bayan haka kuma akwai Mus’hafi Fatima wanda abin da ke cikinsa shi ne Hadisai da sayyida Fadima [AS] ta ji,musamman ma na abubuwan da za su auku,amma abun mamaki daga wasu sashen Musulmi na rashin adalci da kuma jahiltar me ake nufi da mushafi Fatima,sai suna kazafin cewa wai mus’hafi Fatima wani Al-kur’ani ne. Na farko duk wanda zai ce maka wasu na da wani Al-kur'ani,wannan ya nuna lalle bai fahimci ayar da take cewa, “Mune muka saukar da Ambato kuma lalle mune masu kare shi”Allah [S.W.T] ya kare Alkur’ani ta kowace fuska,wato na kayi masa kari ko ragi ballantana kuma wai a kirkire shi. Mai wannan tunanin, haka ya nuna jahilcinsa da kuma wautarsa.Na biyu wasu kalmomi a larabci wani lokaci ana amfani da su a ma’anarsu ta lugga ko isdilahi,saboda haka ya danganta,misali anan mus’hafi fadima,Mus’haf anan da nufin ma’anarsa ta lugga ba wai isdilahi ba.Saboda haka idan mutum yaji ko ya karanta ire-iren wadannan kalmomi sai ya bincika ana nufin ma’ana ta lugga ko isdilahi.Ba gashi an yi bayanin ma’anar hadisi da sunnah a isdilahin malaman hadisi ba amma in da za a duba ma’anarsu a luggace zamu ga ai ba haka bane,misali ma’anar sunnah a luggace shi ne hanya,ma’anar kuma hadisi a luggace shi ne Labari. Na uku idan zaka yi hukunci ga wasu mutane kan wani abu da aka jingina masu, to adalci da kuma ilimi shi ne ka bincika littafansu ka ga haka ne? Shi ya sa anan muna kira ga yan’uwanmu musulmi Ahlus sunnah na duk wani abu da suka ji ko suka karanta wadanda aka jingina ma shi’a da su bincika a littafan shi’ar su ga haka ne ko ba haka ba. Ko wannan mus’hafi Fadima ga mai bukatar bayani akansa ya duba littafin ma’alim da aka ambata a sama.zai ga yadda malamin ya kawo wani hadisi daga Imam Sadiq [AS] dangane da mus’hafi Fatima,ya ke cewa, “Acikinsa babu wata aya ta Alkur’ani, ko hukunce-hukunce na halal da haram,abinda ke cikinsa ilimi ne na abubuwan da za su kasance, har ya cika da cewa wallahi ba Alkur’ani bane.”Haka nan kuma Imam Ali [AS] shi ne farkon wanda ya tattara Alkur’ani a waje guda, in mutum ma ya bincika zai ga cewa abinda Imam Ali ya soma yi bayan wafatin Manzon Allah[S] shi ne tattara Alkur’ani amma mu duba yadda a daya bangaren aka jirkita abun aka mai da shi lokacin Usman dan Affan (AS) abubuwa da yawa makamantan haka sun faru,wasu aka jirkita su wasu kuma aka boye,wanda sai mutum ya bincika a bangaren Ahlul bait zai ga hakika. A kwai wani hadisi a cikin muwaddha Malik mai ban tsoro kuma abin tsokaci ga masu tunani,Hadisin shi ne bayan yakin Uhud sahabban da suka yi shahada bayan an kammala jana’izarsu sai Manzon Allah [S.A.W] ya ce ga su shuhada na uhud:Wa]annan zan yi masu shaida'u sai Sayyidina Abubakar (RA) ya ce ya Manzon Allah mu ba yan’uwansu bane,mun musulunta kamar yadda suka musulunta, mun yi jihadi kamar yadda suka yi jihadi? sai Manzon Allah[S] ya ce haka ne, sai dai ban san me zaku yi a bayana ba,jin haka sai Abubakar ya fashe da kuka, cikon hadisin yake cewa zamu kasance a bayan ka ne.To idan mutum ya duba sharhin muwadda mai suna Tanwirul-Hawalik, wajen sharhin wadannan zan yi masu shaida sai malamin ya ce: Ai zan yi masu shaida ga Imani sahihi da kuma rashin canzawa da kuma rashin gogoriyo ga neman duniya, da makamantansu.Idan mutum na son ya ga wannan Hadisi cikin muwaddha sai ya duba Kitabul-jihad fasalin da ya ke Magana kan shuhada’u fi sabilillah. Wannan hadisi ya nuna abubuwa za su faru bayan wafatin Manzon Allah [S A W] kuma lalle sun faru musammam ga Ahlu baitinsa da kuma mabiyansu, kai da ma Hadisan Manzon Allah [S A W]. Da mutum zai yi bincike kan irin jarabawowin da wasu daga cikin masu ruwaito hadisai suka fuskanta a hannun masu tafi da iko a daular bani umayya da Abbasawa dama gabanin haka ta fuskoki dabam-dabam da ya sha mamaki. A takaice dai mabiya Ahlul bait sun riga mabiya Ahlus sunnah wajen rubuta hadisai, Wato saboda hani da su Ahlus-sunnah suka bi daga masu tafi da iko na hana rubuta hadisai da kuma yada su. Wai saboda hujjar kada a hada wani abu da Alqur’ani, alhali in mutum ya duba zai ga cewa ba yadda za’a yi ka fahimci Alqur’ani in ba tare da hadisi ba,domin hadisi shi ya ke fassara abubuwan da suke dunkule na cikin Alkur'ani.

  1. Campo, Juan Eduardo (2009). "Hadith". Encyclopedia of Islam. ISBN 9781438126968.
  2. al-Asqalani, Ahmad ibn 'Ali (2000). Fath al-Bari (in Larabci). 1. Egypt: al-Matba'ah al-Salafiyyah. p. 193. ISBN 978-1-902350-04-2.