Jego

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
jego
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na haihuwa, giving birth (en) Fassara, multi-organism reproductive process (en) Fassara da multi-multicellular organism process (en) Fassara
Bangare na haihuwa
Ta biyo baya haihuwa da matrescence (en) Fassara
Has cause (en) Fassara Ciki
Yana haddasa neonate (en) Fassara, muscle fatigue (en) Fassara da haihuwa
Gudanarwan likitan fiɗa, obstetrician (en) Fassara da midwife (en) Fassara

Jego ko Biki ((النفاس)) wasu kance Wankan jego ko Wankan biki jego ko biki al'ada ce a kasar Hausa, wato wankan biki. Jego wasu kwanaki ne da mace wadda ta haihu takan dauka wanda Karancin sa kwanaki arba'in zuwa sittin (40-60) amma wasu matan basa kaiwa sittin musamman wadanda suka dade suna haihuwa misali wadda ita haihuwa ta biyu, uku ko abinda ya wuce haka. Amma ita wadda ta zamo haihuwan farko ce to tana iya wuce arba'in kardai ta kasa. To a wadannan kwanakin anayi wani wanka wanda a Hausance ana kiranshi da (wankan Jego/biqi) wannan wanka yanada muhimmanci sosai tunba gurin mai haihuwan farko ba don idan anyi shi da kyau akan rabauta da samun ingantancce lafiya.[1].

Yadda ake wankan Jego/biki[gyara sashe | gyara masomin]

Daga farko ana dafa ruwa har sai ya tafasa akan saka ganyaye saiwoyi da dai sauran su a ruwan wankan sai a dafashi su tare. Bayan an dafa ruwan an saukeshi sai a zuba shi a kwatarni ko kuma baho sai a kaiwa mai jego ban daki tayi wanka dashi, akan samo mata ko ganyen darbejiya ko na taura ds. To da wannan ganyen zata na tsomashi cikin ruwan zafin nan tana bubbugawa a jikinta har ta gama. Ita wacce haihuwan farko ce wani lokacin ana samun wata tsohuwa sai ta dinga mata wankan Jego har ta gama, ita kuma wanda ta saba to da kanta takeyi. A satin farko idan mace ta haihu ba'a barin ta daukan ruwan zafi, sai dai a kaimata. Idan anyi sati tayi ma kanta komai. Amma ita me haihuwan farko har ta gama Kai mata za'a dingayi (ruwan zafin).

Amfanin wankan Jego[gyara sashe | gyara masomin]

Wankan Jego yanada amfani sosai, wanda baza su kirgu ba ga kadan daga cikin su:

1. Yana karawa mace lafiyan jiki.

2. Yana hana tabbatuwar gaban mace a bude saboda a lokacin haihuwa gaban yakan bude sosai, to idan an samu wadataccen wankan biki gaban yakan dawo ya matse.

3. Wankan Jego rigakafi ne daga kamuwa da wasu cututtuka musaman lokacin haihuwa, Mata kan samu wasu cututtuka a lokacin haihuwa, to idan akayi wannan wankan sai a samu kariya.

4. Wankan Jego yana daidai ta jinin mai biki da kuma rage kasala.Wadannan sune kadan daga amfanin wankan Jego. Saboda haka masu ganin kamar wannan Al'adar ta zamo ta da ko kauyanci ce, sai kuyi hattara,don kuwa likitoci da masu maganin gargajiya da Malamai masana sun tabbatar da illar rashin yin wankan Jego da kuma amfanin shi.Wannan Al'adar tanada kyau sosai. Allah ya sa mu dace da kuma samun lafiyar jiki.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. www.alummarhausawa.com.ng