Jump to content

Muharram

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muharram
watan kalanda
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na sacred month (en) Fassara da watan Hijira
Bangare na Hijira kalanda
Mabiyi Zulhajji
Ta biyo baya Safar
Garin Ardabil a watan Muharram.

Muharram Ko kuma da (Larabci:مُحَرَّم‎ muḥarram), watan daya kenan a kalandar Musulunci. Yana daga cikin watanni hudu masu alfarma a shekara. Kalmar Muharram na nufin Kauracewa.

Ranar goma ga watan shine ranar Ashura wadda Musulmi yan Shi'a ke daukar ta a ranar bakin ciki ta duniya yayin da su kuma Musulmai mabiya Sunnah kan yi Azumi a wannan ranar Saboda a Hadisi Ance Annabi Musa ya yi azumi a ranar domin samun nasara a bisa ga Fir'auna. Sannan kuma Annabi Muhammad yayi umarni akan mabiya Addinin musulunci da su azumci wannan rana da kuma ranar tara ga watan kafin ta, wadda yan shi'a ke kira da Tasu'a Kuma sun hakikance a ranar ne aka kashe Imami Haussaini.

Muharram da Ashura ga Musulmi

[gyara sashe | gyara masomin]

Daga ranar da aka ga jaririn watan na Muharram to daga nan farkon shekarar Musulunci ta fara. Watan farko na Musulunci wato Muharram yana daga cikin watanni hudu mafiya alfarma ga muaulmai kamar yadda Allah ya fada a cikin Alkur'ani; Muharram, Rajab, Dhu al Ki'dah da Dhu al Hijjah. Koda kafin zuwan musulunci ma Kuraishawa na girmama su inda yaki ya zama haramun a cikin su.

Muhararram da Ashura ga Yan Shi'a

[gyara sashe | gyara masomin]
Yan shi'a a Husainiya ta kasar Tanzaniya.
Yara yan Shi'a a garin Amroha, Indiya suna bikin ranar Ashura.

Shi'awa na girmama watan muharram saboda a cikin sa ne Imam Hussaini yayi Shahadar sa a wajen da a yanzu shine birnin Karbala a Iran.