Jump to content

Azumi a Musulunci

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Azumi a Musulunci
Islamic term (en) Fassara, Sufi terminology (en) Fassara, dietary restriction (en) Fassara, tunanniyar addini da spiritual practice (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Azumi, chastity (en) Fassara da religious activity (en) Fassara
Bangare na Rukunnan Musulunci
Amfani worship in Islam (en) Fassara, worship (en) Fassara da religious rite (en) Fassara
Facet of (en) Fassara Musulunci da Sufiyya
Suna a harshen gida صَوْمٌ da صِيَامٌ
Muhimmin darasi Fasting Pillars in Islam (en) Fassara
Mabiyi Sahur
Ta biyo baya Iftar
Hashtag (en) Fassara Sawm da Siyam
Has characteristic (en) Fassara Farilla da Sallar Nafila
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Wani hoto na gaisuwar azumi da Musulmai ke aikewa

Azumi ko kuma da Larabci Sawm صوم ko Sawm صوم. Yana daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar wadanda dole sai da su ne Musuluncin mutum yake kammaluwa. Ma'anar azumi shi ne kamewa daga barin ci da sha da jima'i tun daga farkon fitowar Alfijir har ya zuwa faduwar rana.[1]

Bayanin kalmar Sawm

[gyara sashe | gyara masomin]

Kalmar Sawm daga Larabci ne ma'anar ta Kamewa

A wasu harsunan

[gyara sashe | gyara masomin]

Musulmai a tsakiyar Asiya kamar Afghanistan, Indiya, Iran, Bangladash, Pakistan da Turkiya, sunayin amfani da kalmar Roza/Rozha/Roja/Oruc, wadda asalinta daga yaren Farsi ne na mutanen Farisa wato Iran kenan a yau. Amma jama'ar Malay na kasar Malesiya, da a harshen Brunai da Singafo suna kiran kalmar da Puasa haka kuma a kan yi amfani da wannan kalmar a Indonesiya da kudancin Tailan da kudancin Filifin. Al'umar Hausawa suna amfani da kalmar Azumi sannan wadansu kan yi amfani da kalmar rikon baki.

Ma'anar Azumi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haramta ma Musulmai ci da sha da jima'i tun daga lokacin bullowar alfijir Fajr har zuwa lokacin faduwar rana maghrib. Musulmi na da damar yin dukkan abubuwan da aka haramta masa da rana tun daga faduwar rana har zuwa lokacin fitowar Al'fijir. Azumi na taimaka ma musulmi wajen kara kusanci da Allah da kuma tsoron Allah. Sannan musulmai na kara gane kyautar Allah a gare su sakamakon abubuwan da suka saba yi na Al'ada kuma na dole kamar ci da sha da kusantar iyali amma sakamakon azumi dukkan wadanan an haramta masu su. A nan ne musulmai kan farga da irin halin da wadanda basu da wadata kan shiga na rashin ci da sha.[2]

Ma'anar azumi ba wai kawai hana bukatun dan Adam na al'ada ba ne ba kadai a'a harma da yana taimakama dan Adam wajen yin ainahin biyayya ga Allah da kara tsoron Allah da biyayya ga manzon Allah (s.a.w) da kuma kara lafiyar jiki da tattalin arziki da kara sada zumunci.[3]

Sunnonin Azumi

[gyara sashe | gyara masomin]

1. Gaggauta bude baki, shi ne kuma bude-baki da zarar an tabbatar da faduwar rana.[4]

2. Abin bude baki ya kasance danyen dabino ko busasshen dabinon ko kuma ruwa, wanda ya fi a cikin ukun wadanan shi ne na farko da na karshe kuma shi ne na karshen su, mai bi musu kuma shi ne na biyun.

3. Cin sahur, har zuwa kashe karshen dare, da niyyar azumi.

4. Jinkirta sahur, har zuwa tsagin dare na karshe.

Haujjar wajabcin azumi a Al-Kur'ani

[gyara sashe | gyara masomin]

Allah Yace: لبسم الله الرحمن الرحيم

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ كُتِبَ عَلَيْكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ‬

Al-Baqarah (2), Ayah 183


أَيَّامًۭا مَّعْدُودَٰتٍۢ ۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍۢ فَعِدَّةٌۭ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ۚ وَعَلَى ٱلَّذِينَ يُطِيقُونَهُۥ فِدْيَةٌۭ طَعَامُ مِسْكِينٍۢ ۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًۭا فَهُوَ خَيْرٌۭ لَّهُۥ ۚ وَأَن تَصُومُوا۟ خَيْرٌۭ لَّكُمْ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ‬

Kur'ani Surah Al-Baqarah (2), Ayah 184


شَهْرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلْقُرْءَانُ هُدًۭى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَٰتٍۢ مِّنَ ٱلْهُدَىٰ وَٱلْفُرْقَانِ ۚ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ ۖ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍۢ فَعِدَّةٌۭ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ۗ يُرِيدُ ٱللَّهُ بِكُمُ ٱلْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ ٱلْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا۟ ٱلْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا۟ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ‬

Surah Al-Baqarah (2), Ayah 185

Azumin Wajabci na Watan Ramadana

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai abubuwan da ayar Kur'ani ta [2:187] ta baiyana a kaurace masu yayin azumi kamar: Abinci, abin sha, da kuma kusantar iyali. Sannan akwai kari kan haka wanda Shari'a ta baiyana a kaurace masu kamar (Girman kai, mummunan kalami, fada, gulma, da sauran su). Idam musulmi ya kasance yana aikata koda daya daga cikin wadannan ne to azumin sa ka iya lalacewa. Musulmai an umarce su ne da yin sadaka da taimako ga mabukata a cikin watan Ramadana ko kuma yayin azumi. Daga Kur'ani da Sunnah dukkannin wanda yanayi na rashin lafiya ya kaishi ga bazai iya azumi ba ko matafiyi wanda yake yin tafiyar da shari'a ta amince kuma halin tafiya yasa bazai iya azumi ba, to wadannan zasu yi kokarin su rama azumin da ya kubuce masu. Amma kuma wanda wata cuta wadda an kasa shawo kanta ke damunsa to wannan zai nemi shawarar masana lafiya ne idan har sun bashi tabbacin zai iya yin azumi to lallai azumi ya wajaba a kansa, amma kuma idan likitan ya fada masa cewa yin azumin ka iya zama sila ta karuwar larurar tasa to wannan hukuncin sa shine ya ciyar da mutane ko kuma wani mutun guda na tsawon kwana talatin ko kuma ashirin da tara gwargwadon dai yadda watan yayi.

Shiri'ar Musulunci ta haramta azumi ga matar da take jinin al'ada har sai lokacin da jinin ya dauke to sai ta yi wanka kuma taci gaba da azumi. Sannan wannan azumin daya kubuce mata to zata rama shi kafin dawowar wani ramadanan. Wani malamin Musulunci a kasar Amurika Nouman Ali Khan yace "hanin yin azumi ga mata masu al'ada yana da nasaba ne ga lafiyar su domin musulunci ne kadai ke kare lafiyar mabiyansa". Amma kuma matan masu al'ada ka iya cigaba da yin zikirori da adduo'in su.

Azumi ya wajanta ga wanda ya hada wadannan abubuwa guda biyar din

    1. Musulmi ko Musulma
    2. Baligi ko Baliga
    3. Zai iya ko zata iya azumin (wato babu wata larura wadda shari'a ta amince zata sa a dakatar da azumi).
    4. Mazaunin gida (wand ba matafiyi ba)
    5. Wanda baya daga cikin wadannan Mai tsohon ciki, Mara lafiya, Mai babban rauni, Mai shayarwa.

Karya azumi

[gyara sashe | gyara masomin]

Idan mutum cikin halin mantuwa yaci ko yasha ko ya kusanci iyali yayin kuma da yake azumi to hukuncin sa shine zai rike wannan azumin wato ya karasa wannan ranar ba tare da aikata dukwani abinda zai karya azumi ba kuma zai rama shi bayan watan azumi. Amma kuma mutumin da yakasance yana sane ya ci ko yasha ko ya kusanci iyalin sa to wanna ga abinda shariar musulunci ta ce a kansa,

    1. Zai yanta bawa, idan ba hali to
    2. Zai azumci wata biyu, shima idan ba hali to
    3. Zai ciyar ko ya tufatar da mutun sittin.


Jerin Abubuwan dake karya azumi

    • Cin abinci da gangan
    • Shan abin sha da gangan.
    • Saduwa da mace da gangan.
    • Kakaro amai da gangan
    • Fasa niyar azumi.
    • Rashin dauko niyya tun dare ga mai azumin farilla.
    • Zuwan jinin Al’ada ko na haihuwa ana cikin azumi.
    • Shafar gaba da sha’awa, Ko kallo, Da shaawa, Ko tunanin mace da sha’awa, Har maniyyi ya fito.
    • Yin ridda da fita musulunci.
    • Yin Allurar Abinci.

Azumin Kaffara

[gyara sashe | gyara masomin]

Idan wani yayi rantsuwa kuma yazo ya karya to ga hukuncin sa,

    1. zai yanta bawa daya, idan ba hali to
    2. zai ciyar koya tufatar da mutum goma, shima idan ba hali ne to
    3. sai ya azumci kwana uku

Abubuwan da Ake son Mai Azumi Ya Kiyaye

[gyara sashe | gyara masomin]

An karhantawa mai azumi wasu al’amura wadanda ke iya jawo lalacewar azumi, amma da yake ita akarankanta ba sa karya azumi kai-tsaye, su ne:

1. Kai makura wajan kurkurar baki da shaka ruwa a hanci lokacin alwala.

2. Sumbata, ita tana tasiri ta janyo sha’awa wanddaa ke bata azumi ta dalilin fitowar maziyi ko ta saduwa ta yadda za ta wajabta kaffara.

3. Yawan kallon mata don jin sha’awa.

4. Tunani a wajan sha’anin saduwa.

5. Shafa mace da hannu ko rungumarta.

Azumin da aka Haramta

[gyara sashe | gyara masomin]

1. Azumi ranar bukuwan sallah karama ko babba.

2. Ranakun shanya nama (yanyane, ranakun 11, 12, 13 na Zul hajji) . ga wanda ba mai tamattu’i da bai sami fidiya ba.

3. Ranakun al’ada da jinin haiuwa.

4. Azumin mara lafiya rashin lafiya mai tsanani wadda yake ji wa kansa tsoron halaka.

  1. https://islamhouse.com/read/ha/fikhu-a-sawwake-2778721
  2. https://aminiya.dailytrust.com/tarihin-azumin-ramadan/
  3. https://m.dw.com/ha/azumin-watan-ramadan-na-2021/a-57216309
  4. https://hausa.legit.ng/1236562-falalar-watan-azumin-ramadan-da-irin-rahman-da-ke-cikinsa.html