Arewa ta Yamma (Najeriya)
Arewa ta Yamma (Najeriya) | |
---|---|
geopolitical zone of Nigeria (en) | |
Bayanai | |
Ƙasa | Najeriya |
Arewa ta yamma (wanda aka fi sani da Arewa-maso-Yamma ) itace ɗaya daga cikin shiyyoyin siyasar Najeriya guda shida dake wakiltar yankunan ƙasar ta fuskar siyasa na arewa maso yammacin ƙasar. Yankin ta ƙunshi jihohi bakwai – Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da kuma Zamfara.[1]
Ta fuskar yanayin ƙasa, yankin na ƙarƙashin nau'in tsirrai na yankin savanna na yammacin Sudan. A al'adance, yawancin shiyyar ta hada da ƙasashen Hausa - ƙasar asali na Hausawa, ƙungiyar da ke da kaso mafi girma na al'ummar arewa maso yamma; duk da haka, akwai ƴan tsiraru na fulani da sauran ƙungiyoyi, a yankunan yankin.
Ta fuskar tattalin arziki, biranen Arewa maso Yamma – kamar birnin Kano – suna taka rawa sosai wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya[2] yayin da akasarin yankunan karkara suka koma baya saboda rashin tsaro,[3][4] karancin ilimi, da rashin kulawar gwamnati.[5] Yankin yana da yawan mutane kusan miliyan 49, kusan kashi 23% na yawan al'ummar ƙasar. Kano ita ce birni mafi yawan jama'a a arewa maso yamma sannan kuma birni na biyu mafi yawan jama'a a Najeriya kuma birni na ashirin mafi yawan jama'a a Afirka. Sauran manyan garuruwan arewa maso yamma sun haɗa da ( bisa ga yawan jama'a) Kaduna, Zaria, Sokoto, Katsina, Gusau, Garki, da Funtua.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Quadri, Opeyemi (2021-10-17). "6 Geopolitical Zones In Nigeria And The States Under Them". infomediang.com. Retrieved 2022-11-04.
- ↑ "Kano | Location, History, & Facts | Britannica". www.britannica.com. Retrieved 2022-11-04.
- ↑ "Insecurity: The Bane of Northern Nigeria – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2022-11-04.
- ↑ "North West Archives". Premium Times Nigeria. Retrieved 2022-11-04.
- ↑ "UN must recognise 'critical emergency' malnutrition crisis in northwest Nigeria - Nigeria | ReliefWeb". reliefweb.int. Retrieved 2022-11-04.